Kwankwaso Ya Fita Kasar Waje, Ya Yi Magana kan Sauya Shekar Abba Kabir
- Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi tawagar magoya bayan Kwankwasiyya a birnin Dubai da suka jaddada masa biyayya
- Kwankwaso ya yi jawabi ga ‘yan Kwankwasiyya inda ya yi kira gare su da su ci gaba da kare martabar Najeriya da Kano a duk inda suke
- Ya kuma yi tsokaci kan sauya shekar gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya ce bai ga wani dalili na rikici ko sabani da zai kai ga haka ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Dubai – Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karɓi wata tawagar magoya bayan Kwankwasiyya da ke zaune a Dubai.
Jama'an sun kai wa Kwankkwaso ziyara ne domin sake tabbatar da cikakken goyon bayansu ga tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP.

Source: Facebook
Hadimin Rabiu Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ziyarar ta gudana ne a ranar 8 ga Fabrairun 2026.
Maganar Rabiu Kwankwaso a Dubai
A yayin jawabin da ya gabatar, Kwankwaso ya fara da godiya ga Allah da ya ba su damar yin ayyuka na alheri a lokacin da suka samu dama.
Ya taya 'yan Kwankwasiyya murna bisa samun damar barin Najeriya daga Kano zuwa Dubai domin neman halal da bunƙasa sana’o’insu.
Kwankwaso ya jaddada cewa ya kamata ‘yan Kwankwasiyya da ke ƙasashen waje su kasance jakadu nagari na Najeriya, ta hanyar kare martabar ƙasa a duk abin da za su yi a wuraren da suke zaune.
Ya ƙara da cewa an san mutanen Kano da ɗabi’ar kare mutunci da martabar ƙasa tun shekaru masu yawa da suka gabata, yana mai cewa hakan al’ada ce da ta dace a cigaba da riko da ita gam.
Maganar sauya shekar Abba Kabir
Da yake tsokaci kan sauya shekar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zuwa APC, Kwankwaso ya ce bai gano dalilan da suka kai ga daukar matakin ba.
A cewarsa, babu wani faɗa ko rikici da ya sani da zai zama hujjar sauya shekar, kuma babu wata matsala ta kai tsaye da ya kamata a ce ta tilasta hakan.

Source: Facebook
Duk da haka, Sanata Kwankwaso ya karfafa 'yan Kwankwasiyya da cewa bai kamata su ji jikinsu ya yi sanyi ba saboda wasu sun yi butulci.
Ga bidiyon da Kwankwaso ya yi bayani game da sauya shekar Abba Kabir Yusuf a kasa, wanda Sulaiman Uwais Idris ya wallafa a shafinsa na X:
Kwankwaso ya je kasuwar Singer
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara kasuwar Singer bayan gobara ta lakume dukiya mai yawa.
Dandazon jama'a ne suka tarbi Rabiu Kwankwaso a kasuwar, lamarin da ke nuna alamar cewa har yanzu yana da karbuwa a Kano duk da sauya shekar Abba Kabir Yusuf.
Biyo bayan ziyarar, wasu magoya bayan Abba Kabir Yusuf sun yi kira ga gwamnan Kano da ya koma tafiya da Kwankwaso a jam'iyyar NNPP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

