Gudaji Kazaure: Tsohon Dan Majalisa Ya Shirya Kara wa da Tinubu, Zai Nemi Takara
- Tsohon dan majalisar tarayya, Hon. Gudaji Kazaure, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2027
- Kazaure ya ce manyan ‘yan siyasa kamar Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Peter Obi duk “iyaye ne”, yana cewa lokacin matasa ya yi
- Ya ce ya zabi jam’iyyar ADC ne saboda burinsa na kawo sauyi, yana mai cewa idan zai saita Najeriya idan samu damar da Bola Tinubu ya samu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dutse, Jigawa - Tsohon dan majalisar tarayya a Najeriya, Hon. Gudaji Kazaure ya yi magana kan shugabanci a Najeriya.
Hon. Kazaure ya bayyana kudirinsa na neman shugabancin Najeriya a shekarar 2027 domin kara wa da Shugaba Bola Tinubu.

Source: Facebook
Gudaji Kazaure zai nemi takarar shugaban kasa
Gudaji Kazaure ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da DCL Hausa wanda ta wallafa a shafin Facebook.
Tsohon dan majalisar ya ce akwai masu neman kujerar da dama kamar Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi da kuma Peter Obi amma duka iyaye ne babu matashi.
A cewarsa:
"A yau kai ne mutum na zan yi magana da a kan niyya ta ta gaba, a Najeriya muna da mutane da suke cikin jam'iyyar ADC hadaka.
"Akwai mai girma babana, Atiku Abubakar, akwai yayana, Rotimi Amaechi akwai Peter Obi sannan akwai wadanda za su so nan gaba.
"Dukkansu iyaye ne da yayu amma babu matashi wanda lokacin mu ya yi da ya kamata a gwada mu, muma a ga gudunmawar da za mu bayar."

Source: Twitter
'Lokacin matasa ya yi' - Gudaji Kazaure
Har ila yau, Hon. Kazaure ya bayyana cewa matasan Najeriya na tsoron neman shugabancin kasar saboda suna ganin sai mai arziki.
Ya ce ya gama yanke shawarar neman kujerar shugaban kasa a jam'iyyar ADC domin kawo sauyi a Najeriya baki daya.
Dan siyasar ya sha alwashin saita Najeriya inda ya rantse da Allah da shi ya samu damar da Bola Tinubu ya samu da an wuce wurin tun da dadewa.
"Don haka matasa suna ganin kujerar shugaban kasa nisa gare ta, tana da wahala sai mai arziki da mai kudi kowa na tsoron fitowa takara.
"Saboda ni na yanke hukunci zan fito takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC a shekarar 2027 idan muna raye.
"Matsayina ya ci na rike Najeriya, da ni na samu dama irin ta Bola Tinubu, da na gyara Najeriya wallahi, da na saita ta, shi ma na kai masa hanyar da za a saita Najeriya.
"Ba a biyo hanyar seta ta ba ne,wasu tsiraru ne ke juya Najeriya, idan aka samu jajirtaccen shugaba wanda zai iya seta Najeriya ba wan abu ba ne."
- Hon. Gudaji Kazaure
'Kafin 12:00 na rana Tinubu ya fadi' - Kazaure
A baya, kun ji cewa tsohon ɗan majalisa Muhammad Gudaji Kazaure ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu, yana zargin ta lalata Najeriya gaba ɗaya.
A cewar 'dan siyasar na Jigawa, idan Allah ya kai mu zaben 2027, kafin ƙarfe 12:00 na rana za a gama da Tinubu saboda gazawar da ya nuna.
Hon. Muhammad Gudaji Kazaure ya ce ya gabatar da bincike kan kudaden da aka wawure, amma Tinubu ya yi biris, kuma ya cigaba da karbo bashi.
Asali: Legit.ng

