‘Ka Sakar Masa Mara’: Matar Ganduje Ta Roki Kwankwaso game da Mulkin Abba

‘Ka Sakar Masa Mara’: Matar Ganduje Ta Roki Kwankwaso game da Mulkin Abba

  • Uwargidar tsohon gwamnan Kano, Farfesa Hafsat Ganduje, ta bukaci Rabiu Musa Kwankwaso ya ajiye rigingimun siyasa da Gwamna Abba Kabir
  • Ta ce Abba Kabir Yusuf ya shafe kusan shekaru 40 yana aiki karkashin Kwankwaso, don haka ya dace a amince da zabinsa
  • Uwargidan Ganduje ta bukaci hadin kai a APC, tana cewa shigowar Gwamna Yusuf jam’iyyar alama ce ta fifita ci gaba da zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohuwar Uwargidan tsohon gwamnan Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje, ta roki Rabiu Musa Kwankwaso ya manta da gabar siyasa.

Hafsat Ganduje ta yi kira ga tsohon gwamna kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, da ya ajiye duk wani abu tsakaninsa da Abba Kabir.

Matar Ganduje ta nemi sulhunta Abba da Kwankwaso
Gwamna Abba Kabir da Abdullahi Ganduje da jagora Rabiu Kwankwaso. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Abba: Matar Ganduje ta shawarci Kwankwaso

Uwargidar Ganduje ta yi wannan kiran ne yayin jawabi a wani shirin tallafa wa al’umma da karamar Ministar harkokin Abuja, Mariya Bunkure, ta shirya, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Kano ta kara daukar zafi, an kalubalanci Kwankwaso kan wasu kwangilolin gwamnatin Abba

Ta ce ya kamata Kwankwaso ya bar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gudanar da mulkinsa cikin kwanciyar hankali domin amfanin al’ummar Jihar Kano baki daya.

A cewarta, lokaci ya yi da tsohon gwamnan Kano zai nuna girma ta hanyar yafiya da goyon bayan ci gaban jihar fiye da rike sabanin siyasa.

Ta ce:

“Ina kira ga tsohon gwamnan Kano da ya yi hakuri. Abba ya yi aiki a karkashinsa tsawon shekaru 40 bisa umarninsa.”

Ta kara da cewa Kwankwaso ya kamata ya bar duk wani fushi a baya tare da amincewa da shawarar Gwamna Abba Yusuf na komawa jam’iyyar APC.

Da take jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC, ta bukace su da su hada kai bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yanke shawarar shiga jam’iyyar.

“Tun da Gwamnan Kano ya yanke shawarar shiga APC, ya dace mu hada kai domin tabbatar da ci gaba.”

- In ji Farfesa Hafsat Ganduje.

Hafsat Ganduje ya roki Kwankwaso ya sasanta da Abba
Matar tsohon gwamnan Kano, Hafsat Ganduje da Abdullahi Ganduje. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Facebook

'Kokarin da Ganduje ya yi kan Abba'

Hafsat Ganduje ta kuma bayyana cewa mijinta, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo Kano kwanan nan domin karbar Gwamna Abba Kabir zuwa APC.

Kara karanta wannan

Sunan malami ya fito: An shawarci Kwankwaso kan 'yan takarar da za su kifar da Abba

Uwargidan ta ce duk shari’o’in da suka biyo bayan zaben da ya gabata har zuwa Kotun Koli sun nuna cewa Allah ne ya kaddara dawowar Abba APC.

A cewarta, tsohon gwamnan ya katse doguwar tafiya da yake yi domin ya dawo da kansa ya tarbi Gwamna Yusuf cikin farin ciki.

Ta bayyana hakan a matsayin shaida cewa Ganduje mutum ne mai kaunar hadin kai kuma ba ya rike gaba idan ana maganar ci gaba.

NNPP ta nesanta kanta da kalaman Kwankwaso

A wani labarin, maganar da Rabiu Kwankwaso ya yi cewa ya dauki Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa wurin alkalan kotun koli sun tada kura.

Tsagin jam'iyyar NNPP karkashin jagorancin Agbo Major ya nesanta kansa da maganar da Kwankwaso ya yi, ya ce lokacin ba dan jam'iyyarsu ba ne.

Hakan ya zo a daidai lokacin da kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta kai korafin Sanata Kwankwaso gaban Sufetan Yan Sandan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.