Majalisa Ta Yi Magana kan Batun Tsige Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Gwarzo

Majalisa Ta Yi Magana kan Batun Tsige Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Gwarzo

  • Majalisar dokokin jihar Kano ta musanta rahotanni da ake yadawa cewa tana yunkurin tsige mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo
  • Mai magana da yawun kakakin Majalisar Kano, Kamaluddeen Sani Shawai ya ce babu wani yunkuri ko shiri na cire Kwamred Aminu Gwarzo
  • Ya tabbatar da cewa, a halin yanzu Majalisar dokokin jihar aliKano ta maida hankali ne wajen gudanar da ayyukanta kamar yadda doka ta tanada

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Majalisar Dokokin Kano ta yi watsi da rahotannin da ke ikirarin cewa ta fara wani yunkuri na tsige mataimakin gwamnan Jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo.

Majalisar ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa ta fara shirin tsige Aminu Garzo, inda ta bayyana rahotannin a matsayin marasa tushe ballantana makama.

Majalisar dokokin jihar Kano.
Majalisar dokokin jihar Kano yayin da take zama kamar yadda doka ta tanada Hoto: Kano State Assembly
Source: Facebook

A wani rahoto da Tribune Nigeria ta kawo, majalisar ta bayyana cewa babu wani kudiri ko yunkuri a gaban mambobin majalisar Kano da nufin tsige mataimakin gwamnan.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yadda 'yan ta'adda suka kira Sallah, suka kashe duk wanda ya zo Masallaci

Ta kuma yi ikirarin cewa an kirkiri wadannan rahotannin na karya ne kawai domin haddasa takaddama ta siyasa da ba ta da amfani a jihar Kano.

Majalisar Kano na shirin tsige Aminu Gwarzo?

Da yake magana da manema labarai ranar Asabar, mai magana da yawun Shugaban Majalisar Kano, Kamaluddeen Sani Shawai, ya ce jita-jitar da ke yawo a wasu kafafen yada labarai ba gaskiya ba ce.

"Babu ko kudiri daya ko wani yunkuri a cikin majalisar nan na tsige mataimakin gwamna. Wadannan rahotanni na karya ne, don haka ya kamata jama'a su yi watsi da shi.
"Mataimakin Gwamna na ci gaba da gudanar da ayyukansa tare da cikakken goyon bayan majalisa," in ji Shawai.

Ya yi kira ga jama'a da yan jarida da su tantance bayanai kafin wallafawa, yana mai nuni da cewa rahotannin da ba su da tabbas na iya lalata kwanciyar hankalin siyasa da kuma amincewar jama'a.

Yadda aka nemi Aminu Gwarzo ya yi murabus

Wannan dambarwa ta biyo bayan wasu kalamai da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya yi a yayin wata hira da gidan rediyo.

Kara karanta wannan

Bauchi: NEDC ta kawata kabarin Tafawa Balewa a gagarumin gyara da ta yi

Kwamishinan ya yi kira ga mataimakin gwamnan da ya yi murabus saboda ya ki bin tafiyar siyasar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke jagoranta.

Aminu Gwarzo.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo Hoto: Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo
Source: Twitter

Duk da cewa mataimakin gwamnan bai fito ya ce uffan ba kan wannan jita-jita, majiyoyi daga cikin gwamnatin jihar Kano sun tabbatar da cewa yana nan yana gudanar da ayyukansa na yau da kullum kamar yadda aka saba.

Aminu Gwarzo ya halarci saukar Alkur'ani

A wani rahoton, kun ji cewa Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ya halarci taron sauka da haddar Alkur'ani mai girma ranar Lahadi.

Aminu Gwarzo ya halarci wani taron saukar karatun Alkur'ani mai girma, wanda shi ne taro na farko da ya halarta tun bayan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC.

Shugaban ya ya bukaci daliban da suka haddace Littafin Allah mai tsarki da su yi amfani da abin da suka karanta wajen tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262