‘Ba a Gudu da Susan Duwawu’: An Shawarci Pantami kan Hada Siyasa da Malanta
- Jaafar Jaafar ya ce yana shakkar yiwuwar nasarar siyasar Farfesa Isa Ali Pantami matuƙar yana son rike matsayin malami da ɗan siyasa lokaci guda
- Ya jaddada cewa hada addini da siyasa na iya janyo ruɗani, inda ya ce shugabancin addini na bukatar tsarkin ɗabi’a, siyasa kuma cike take da datti
- Jaafar Jaafar ya shawarci Sheikh Pantami da ya zabi hanya guda, yana mai cewa siyasar Najeriya ba ta dace da matsayin malamin addini ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Kwararren dan jarida, Jaafar Jaafar ya yi sharhi mai zafi da ya janyo ce-ce-ku-ce kan siyasar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Jaafar Jaafar ya yi sharhin ne kan abin da ya kira burin siyasar Farfesa Isa Pantami, inda ya bayyana shakku kan yiyuwar nasararsa.

Source: Facebook
'Dan jaridar ya bayyana ra'ayinsa a yau Asabar 7 ga watan Faburairun 2026 a shafinsa na X tare da ba shi shawarwari kan siyasa.
Shawarar da Jaafar Jaafar ya ba Isa Pantami
A cewarsa, matsalar Isa Pantami ita ce son kasancewa a matsayin malamin addini da kuma ɗan siyasa, lamarin da ya ce ba ya yiwuwa.
Ya yi nuni da karin magana ta Hausa da ke cewa mutum ba zai iya gudu yana susar duwawu ba lokaci guda, yana mai cewa rarraba hankali na raunana ƙwazo.
Jaafar Jaafar ya bayyana cewa Pantami na fuskantar ruɗanin tunani, inda aka ce addini na bukatar tsarkin ɗabi’a, siyasa kuma ta dogara ne da kalamai marasa daraja.
Ya kuma ce Pantami ya guji zama irin “sadaka yalla”, wato wanda bai tsaya a wuri guda ba, ya kuma cire rigar wa’azi idan har yana son tsunduma siyasa gaba ɗaya.
A cewarsa, siyasar Najeriya cike take da datti, inda ya ce ba za ka shiga magudanar shara ka fito da tsafta ba.
Ya lissafa wasu dabi’u da ake dangantawa da siyasa kamar yaɗa kalaman batanci, rawa da wakokin siyasa, cudanya da kowane irin jinsi, da kuma yin sulhu da abubuwan da addini ke hani.
Ya ce:
"Siyasar Najeriya cike take da datti. Ba za ka yi aiki a magudanar shara ka sa ran ka fito tsaf ba, dole Malam ya shirya jifa da ƙazafi, ya tsoma hannunsa cikin almubazzaranci, ya yi rawa da wakokin Rarara, ya yi musabaha da mata masu zuba jari da jakadun ƙasashen waje.
"Zai ziyarci coci-coci, ya sace biliyoyin kuɗi daga asusun tsaro, ya karkatar da kuɗaɗen gwamnati don harkokin siyasa, ya ɗauki ’yan daba a lokutan gangami, ya yi ƙarya a yaƙin neman zaɓe, ya tafka maguɗi a zaɓe, ya kuma karɓi cin hanci bayan bayar da kwangila."
Jaafar Jaafar ya kammala da gargadin cewa idan Pantami zai shiga siyasa, dole ya shirya fuskantar tsananin kalubale da sauyin hali, domin siyasa da wa’azi ba sa tafiya tare.
Pantami ya sabunta katin zama dan APC
A wani labarin an ji Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ziyarci sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Gombe domin sabunta rajistarsa ta zama mamba.
Tsohon Ministan na sadarwa a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya dade yana shiga cikin harkokin siyasa.
Farfesa Pantami ya kuma bayyana shawarar da ya taba samu daga wajen tsohon shugaban kasar na Najeriya kan siyasar Gombe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


