Bayan Haduwar Mutanen Abba da na Ganduje, an Gwabza Rikici a Taron APC a Kano
- Rikici ya tayar da kura a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a mazaɓar Dawakin-Tofa/Tofa/Rimingado, lamarin da ya tilasta tarwatsa taron kafin a kammala
- Saɓani ya ɓarke ne bayan wasu kalaman da shugabar mata ta NNPP da suka koma APC ta yi, wadda ta jawo martani mai zafi daga ɗan majalisar tarayya na yankin
- Taron ya zama dandali na farko da ya haɗa tsagin siyasar yankin da ke bangarorin Abba Kabir Yusuf da Gandujiyya a inuwa ɗaya, abin da ya ƙara tayar da hankali
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Rikici ya ɓarke a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano, wanda aka gudanar a mazaɓar Dawakin-Tofa/Tofa/Rimingado, lamarin da ya tarwatsa taron.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga muhawara mai zafi da ta taso tsakanin wasu manyan 'yan siyasa a yankin, musamman bayan kalaman ƙalubale da aka yi a bainar jama’a.

Source: Facebook
Daily Nigerian Hausa ta wallafa a Facebook cewa lamarin ya faru ne yayin da taron ke gudana, inda aka samu tashin hankali har aka yi yunkurin hana wasu jawabi.
Yadda rikici ya ɓarke a taron APC
Rikicin ya fara ne bayan shugabar mata ta jam’iyyar NNPP a Dawakin-Tofa da suka koma APC, Hajiya Hasiya Aminu ta yi korafi kan ɗan majalisar tarayya na yankin, Tijjani Abdulkadir Jobe.
An rawaito cewa Hajiya Hasiya ta zargi Jobe da gazawa wajen kulawa da 'yan jam’iyya, inda ta yi kira gare shi da ya yi koyi da Shugaban Karamar Hukumar Dawakin-Tofa, Anas Mukhtar Bello DanMaliki, da kuma Abba Ganduje.
Arewa Updates ta wallafa bidiyon da Hajiya Hasiya ta yi korafin a Facebook, kuma an ce kalaman da ta yi ne suka janyo ɓacin ran ɗan majalisar tarayyan.
Rahotanni sun ƙara da cewa yayin da Hajiya Hasiya ke tsaka da jawabi, sai Tijjani Jobe ya so ba da amsa, amma aka yi ƙoƙarin hana shi, har ma aka kwace lasifika.
Yadda taron APC ya tarwatse a Kano
A wannan lokaci ne waje ya kaure, inda wasu fusatattun matasa masu goyon bayan ɗan majalisar tarayya suka tarwatsa taron. An rawaito cewa an kekketa rigar mai gabatar da taron, wato MC, wanda ya sha da ƙyar kafin ya tsira daga wajen.
Wani daga cikin mahalarta taron ya shaida cewa da dama daga cikin masu ruwa da tsakin jam’iyyar sun gudu domin tsira da rayukansu, bayan da taron ya rikide zuwa tashin hankali.

Source: Facebook
Rahoton ya nuna cewa wannan shi ne taro na farko da ya haɗa tsagin ɗan majalisar Joɓe da kuma na Abba Ganduje, waɗanda suka fafata a zaɓen 2023 kuma ba sa ga maciji da juna.
Sanata Kwankwaso ya firgita 'yan APC
A wani labarin, mun kawo muku cewa an fara maganganu game da makomar siyasar Kano bayan Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC.
Tattaunawa ta karu game da siyasar Kano bayan Rabiu Kwankwaso ya tara dandazon jama'a a gidansa da kuma yayin ziyara kasuwar Singer.
Wasu magoya bayan Abba Kabir Yusuf sun yi kira ga gwamnan da ya mayar da su, su cigaba da tafiya da Rabiu Kwankwaso wanda shi ne uban gidansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

