Hukumar INEC Ta Warware Batun Bangaren da Ta Aminta da Shi a Jam'iyyar PDP
- Hukumar zaben Najeriya watau INEC ta bayyana cewa babu wani tsagi da ta amince da shi fiye da dayan a jam'iyyar PDP
- INEC ta ce halartar bangaren da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi a taron hukumar, ba yana nufin ta amince da shi ba ne
- Wannan dai na zuwa ne bayan tsagin PDP karkashin Abdulrahman Mohammed da Sanata Anyanwu sun halarci taron INEC da jam'iyyun siyasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi bayani kan zargin da ake yadawa cewa ta amince da tsagin Sanata Samuel Anyanwu a rikicin jam'iyyar PDP.
INEC ta bayyana cewa ganin kwamitin gudanarwa (NWC) na PDP da AbdulRahman Mohammed da Samuel Anyanwu ke jagoranta, a taronta ba shi ke nuna hukumar da dauki bangare daya ba.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce wannan na zuwa bayan tambayoyi da aka dinga yi kan dalilin da ya sa tsagin Anyanwu, wanda ministan Abuja, Nyesom Wike ke goyon baya ne kawai ya halarci taron, yayin da tsagin da Tanimu Turaki ke jagoranta bai halarta ba.
Shin INEC ta amince da tsagin Wike?
Mataimakin Daraktan Yada Labarai na INEC, Mista Wilfred Osilama Ifogah, ya bayyana a wata hira da aka yi da shi cewa, hukumar tana aika gayyata ne ga jam’iyya, ba ga wani tsagi na daban ba.
"Ana aika wasiƙun gayyata ne zuwa ga jam’iyya, ba ga mutane ba, muna sanya adireshin wasiƙun ne zuwa ga Shugaba da Sakataren jam’iyya," in ji shi.
Ya bayyana cewa INEC ba ita ke tantance waɗanda jam’iyya za ta tura su wakilce ta ba; hukumar tana karɓar duk wanda jam’iyyar ta gabatar a matsayin wakilinta ne kawai.
Me yasa tsagin Wike ya halarci taron INEC?
Ifogah ya yi watsi da ra’ayin cewa INEC ta nuna goyon baya ga tsagin Anyanwu ta hanyar ba su damar halartar taron.
A cewarsa, idan wakilan jam’iyya suka zo taro, su suke gabatar da kansu, ko dai a matsayin shugabanni ko kuma waɗanda suke wakiltar shugabannin, INEC ba ta binciken gaskiyar wannan wakilci muddin jam'iyyar ta amsa kiran gayyatar.

Source: Facebook
Game da dambarwar da ke gudana a cikin PDP, Ifogah ya jaddada cewa sasanta rigingimun cikin gida ba ya cikin aikin INEC.
“Babu ruwanmu da rikicin cikin gida na jam'iyyu, ba mu damu da hakan ba. Duk sanda suka sasanta, mu kuma za mu yi aiki da su,” in ji shi.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa rashin sasanta rigingimun shugabanci na iya shafar shigar jam’iyya cikin harkokin zaɓe waɗanda ke da ƙayyadajjen lokaci, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Tsagin PDP ya caccaki hukumar INEC
A wani rahoton, kun ji cewa tsagin jam'iyyar PDP da Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta, ya soki hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Kara karanta wannan
INEC ta dauki bangare 1 a rikicin PDP, ta yi zama da shugabannin jam'iyyu a Abuja
Bangaren na Turaki ya yi sukar ne bisa alamun da INEC ta nuna na amincewa da kwamitin rikon kwarya da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke mara wa baya.
'Yan bangaren da aka zaba a wani babban taro na kasa sun bayyana matakin a matsayin wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki kuma mai tayar da hankali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

