Kwankwaso Ya Firgita Mutanen Abba Kabir bayan Tara Dandazon Jama'a a Kano
- Tarin jama’a da Rabiu Musa Kwankwaso ya tara ya haifar da ce-ce-ku-ce a Kano, musamman daga bangaren magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Ziyarar Kwankwaso kasuwar Singer domin jaje bayan gobara ta sake janyo hankalin jama’a, inda aka gan shi cikin tarin mutane masu yawa
- Biyo bayan haka, magoya bayan Abba Kabir Yusuf sun fitar da ra’ayoyi mabambanta, wasu na neman sulhu, wasu kuma na gargadi kan abin da zai iya faruwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Al’amuran siyasa a Kano sun dauki sabon salo bayan yadda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi bakuncin dimbin jama’a a gidansa da ke Miller Road, tare da ziyarar da ya kai kasuwar Singer domin jaje.
A ranar Alhamis, 5, Fabrairu, 2026, jama’a daga karamar hukumar Dawakin Kudu sun kai ziyarar nuna goyon baya ga Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Kwankwaso ya ce ya yi musu jawabi yana kira da su kasance masu lura da duk wani yunkuri da ka iya lalata nagarta da ingancin tsarin Kwankwasiyya.
Taron jama’a a gidan Kwankwaso
A jawabin da ya yi wa jama’ar Dawakin Kudu da suka kai masa ziyara, Kwankwaso ya bayyana farin cikinsa bisa goyon bayan da aka nuna masa, yana mai jaddada bukatar kare mutuncin tsarin siyasa daga duk wata dabara ta magudi.
Ya bukaci magoya bayansa da su kasance masu hakuri da hangen nesa, tare da tsayawa kan gaskiya da adalci a harkokin siyasa.
A wannan rana, Kwankwaso ya ziyarci kasuwar Singer domin jajantawa ‘yan kasuwa bayan gobarar da ta lakume shaguna da dama.
Abba ya je kasuwar Singer
Bayan tafiyar Rabiu Kwankwaso, Gwamna Abba Kabir Yusuf ma ya kai ziyara kasuwar Singer domin jajanta wa ‘yan kasuwa.
Mai magana da yawun Abba, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya nuna matukar damuwa kan asarar da aka yi.

Source: Facebook
Abba Kabir ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga wadanda gobarar ta shafa, tare da umarnin fara aikin fadada da gyaran hanyoyin kasuwar.
Martanin magoya bayan Abba Kabir
Bayan ganin dandazon jama’ar da Kwankwaso ya tara, wasu daga cikin magoya bayan Abba Kabir Yusuf sun fitar da ra’ayoyinsu a fili.
Ummi Abba Gama ta fitar da sako a Facebook tana rokon gwamnan da ya jawo Kwankwaso cikin tafiyar gwamnati, ko kuma a samu sulhu tsakanin bangarorin:
“Don Allah Mai Girma Gwamna, ka jawo ubanmu Kwankwaso cikinmu. Ko kuma ka kwashe mu ka maida mu gidan ubanmu.”
Abdullahi Giggs ya rubuta gargadi a Facebook cewa idan ba a dauki mataki ba, Kano na iya fuskantar yanayin gwamna mai jama’a da kuma gwamna mai iko:
“Idan ba a taka masa burki ba, za a yi gwamna biyu a Kano — gwamna mai jiniya da gwamna mai jama’a.”
Salisu Lawan Dankaka ya wallafa a Facebook cewa har yanzu Kwankwaso yana da tasiri a Kano, yana mai cewa ba da sauki za a iya yi masa ritaya a siyasa ba.
“Ka da mu yaudari kanmu, na rantse da Allah Kwankwaso dai a Kano sai an jira. Matsalarsa kawai na kewaye da shi suke rusa tafiyarsa.
"Amma wallahi yi wa Kwankwaso ritaya a siyasa karya ne; ba wanda zai iya, sai Allah. Amma mu muna layin gwamnati, Allah dai ya sa mu ci dadin nan.”

Source: Facebook
Ahmad Sabo Gama ya yi kira ga Gwamna Abba da ya sauya salon tafiya a sakon da ya fitar a Facebook:
Ahmad Sabo Gama ya ce:
“Wallahi Gwamna Abba, idan ba ka canza salo ba, da mu da ka samu a APCn da kai da ka shigo. Madugu 'yar guda ɗaya zai yi mana.”
Legit tattauna da Muhammad Sani
A tattaunawa da Muhammad Sani da ke goyon bayan tsarin Kwankwasiyya, ya bayyana wa Legit cewa abin da ya faru ya ba shi mamaki.
Ya ce:
"Har yanzu ban gama yarda da cewa da gaske Abba Kabir ya raba hanya da Kwankwaso ba. Ina ganin kamar abin ba gaskiya ba ne.
"Ina fata a ce ba haka ba ne. Idan kuma ta tabbata hakan ne, ta abin ya zo min da mamaki."
'Dan Ganduje ya gana da Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa dan tsohon Shugaban APC, Abdulaziz Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Abdulaziz ya ziyarci Kwankwaso ne a gidansa da ke Miller Road a Kano yayin da jagoran NNPP ya karbi baki da wasu sassan Kano.
Hakan na zuwa ne yayin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba hanya da Kwankwaso ya hada kai da Abdullahi Ganduje a jam'iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



