Bayan Raba Gari a Siyasa, Abba da Kwankwaso Sun Gwada Farin Jininsu a Kano
- Kasuwar Singer a Kano ta rikide zuwa dandalin gwajin farin jini, yayin da Gwamna Abba Yusuf da Rabiu Kwankwaso suka kai ziyara
- Kwankwaso ya fara ziyara inda magoya baya suka tarbe shi, sai daga baya Gwamna Yusuf ya zo, ya yi alkawarin tallafin gwamnati
- Ziyarorin sun nuna rarrabuwar kan siyasar Kano bayan gwamnan ya bar NNPP zuwa APC, yayin da ake shirin zaben 2027 da ke tafe
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Kasuwar Singer da ke Kano ta zama wurin gwajin farin jini a ranar Alhamis 5 ga watan Fabrairun 2026.
Gwamna Abba Yusuf da tsohon uban gidansa a siyasa, Rabiu Kwankwaso, sun kai ziyarar jaje game da iftila'in gobara.

Source: Twitter
Ziyarorin sun biyo bayan mummunar gobara da ta kone kayayyaki da dukiyoyi masu darajar sama da Naira biliyan daya a kasuwar da tsakar dare, cewar Premium Times.
Kwankwaso ya ziyarci kasuwar Singar a Kano
Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso shi ne ya fara isa kasuwar, inda magoya bayansa suka tarbe shi cikin murna da rera wakoki.
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda aka gano dandazon jama'a suna yi masa barka.
Bayan ziyararsa, an gano shi yana gaisawa da jama’a bayan ya sauko daga mota kirar Toyota Land Cruiser.
Ya sanya babbar riga tare da jar hular, wadda ke zama alamar tafiyar Kwankwasiyya a siyasar Kano.
Kwankwaso ya rubuta cewa:
“Na gode mutanen Kasuwar Singer, Kano. Allah ya saka muku da alheri, ya mayar da asarar da mafi alheri. Ameen.”
Ziyarar Kwankwaso da irin tarbar da aka yi masa ta nuna cewa har yanzu tasirinsa yana nan daram a siyasar jihar Kano.

Source: Facebook
Ziyarar Abba Kabir a kasuwar Singer
Bayan wasu awanni, Gwamna Abba Yusuf ya kai tasa ziyarar, inda shi ma jama’a suka tarbe shi da taron magoya baya masu yawa.
A yayin ziyararsa, Gwamna Abba ya yi alkawarin daukar matakan gaggawa tare da bayar da tallafin kudi ga ‘yan kasuwar da gobarar ta shafa.
Hadimi na musamman ga gwamnan, Salisu Yahaya Hotoro shi ma ya yaɗa bidiyon Abba Kabir Yusuf a Facebook yayin ziyara a kasuwar.
Magoya bayan bangarorin biyu sun rika yada bidiyoyi a kafafen sada zumunta domin nuna irin farin jinin gwanayensu a idon jama’a.
Lamarin ya dauki salo na siyasa, yayin da tsofaffin abokan tafiya a tafiyar Kwankwasiyya suka koma fafatawa a bainar jama’a.
Wannan ita ce babbar haduwar jama’a ta farko da bangarorin biyu suka yi domin gwada karfinsu tun bayan rabuwa a siyasa.
Kalaman Kwankwaso sun jawo masa matsala
An ji cewa Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta yanke shawarar rubuta koke ga ‘yan sanda kan kalaman Rabi'u Musa Kwankwaso.
Lauyoyin sun bayyana damuwa kan yadda ake zargin Kwankwaso da tsoma baki a shari’ar zaɓen gwamnan Kano a 2019.
Kungiyar ta ce ikirarin samun kusanci da alkalan Kotun Koli na iya girgiza amincewar jama’a ga ‘yancin bangaren shari’a da tsarin dimokuraɗiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

