Yadda Shugaba Tinubu Ya Yi wa Gwamna Abin da bai Saba ba a Fadar Aso Rock
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saba al’adar fadar shugaban ƙasa ta hanyar zama a kujerar baƙo tare da Gwamna Uba Sani
- A lokacin da Gwamna Uba Sani ya ziyarci shugaban bayan harin da 'yan bindiga suka kai jiharsa, Tinubu ya dawo kusa da shi ya zauna
- Wannan al'amari ya ja hankalin 'yan Najeriya, inda wasu ke ganin kware wa ce irin ta siyasar Bola Ahmed Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karya ka’ida ta fadar shugaban ƙasa ta hanyar zama tare da Gwamna Uba Sani a kujerar baƙo.
Shugaban na Najeriya ya dawo gefen Uba Sani a kujerar baki ne a lokacin da ya kai masa ziyara Aso Rock bayan sace wasu bayin Allah a jihar Kaduna.

Source: Twitter
Bashir Ahmad, tsohon hadimin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya wallafa hoton ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, 7 ga watan Fabrairu, 2026.
Tinubu ya karya al'adar Fadar Shugaban kasa
A sakon da ya wallafa tare da hoton, Bashir Ahmad ya ce ba da gangan Shugaban kasa ya yi irin wannan zama da Uba Sani ba.
A cewar sa, mataki ne da zai nuna kusancin da ke tsakaninsa da gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani.

Source: Twitter
Bashir Ahmad ya rubuta cewa:
"Shugaban ƙasa ya karya al’adar ne domin nuna cewa Gwamna Uba Sani mutuminsa ne."
Martanin jama'a ga zaman Tinubu da Uba
Masu bibiyar shafin Bashir Ahmad sun bayyana ra'ayoyi daban-daban a kan wannan zama da ba a saba ganinsa a al'adance ba.
Masoya Gwamna Uba Sani sun fara alfahari da yadda shugaban na Najeriya ya karrama shi, suna ganin wannan ya nuna kusancinsu.
Wani mai amfani da shafin X @Christophe23067 ya ce:
“Ta hanyar karya doka da zama a kujerar baƙo, Shugaba Tinubu na aika saƙon amincewa, haɗin kai da goyon bayan. A siyasa, alamu sun fi magana fiye da kalmomi, kuma wannan alamar tana sanya Gwamna Uba Sani a cikin sahun mutanen da shugaban ke matuƙar yarda da su."
@ay_mister ya ce:
“Wannan mutumin da ke zaune da Jagaban nan na iya zama shugaban Najeriya na gaba. Na tabbata PBAT ba zai yi sakaci wajen zaɓar magajinsa ba kamar Buhari.”
@anointingfire89 ya bayyana cewa:
“Na ji tausayin mutanen Jihar Kaduna. Ba su da gwamna; abin da suke da shi mutum ne kawai da ke kwaikwayon shugabanci ne kawai”
@oparaorji ya ce:
“Ku faɗa masa ya daina karya doka, ya gyara matsalolin tsaro da wahalar tattalin arziki. ’Yan Najeriya ba su damu da al’adar zama ba, abin da suke so shi ne aiki.”
Uba Sani ya yi magana a kan Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Malam Uba Sani, ya yi hasashen cewa za a samu ƙarancin gwamnonin da za su iya tsayawa su ƙalubalanci tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cewarsa, irin goyon bayan da Shugaba Tinubu ke bai wa gwamnatocin jihohi ya sa gwamnonin ƙasar za su kasance cikin sahun masu mara masa baya.
Gwamna Uba Sani ya yi wannan furuci ne yayin buɗe wani muhimmin taron tattaunawa tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa na kwanaki biyu da aka gudanar a birnin Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


