Kalaman Kwankwaso na Taimaka wa Abba Kabir a Shari'ar 2019 Sun Jefa Shi a Matsala
- Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta yanke shawarar rubuta koke ga ‘yan sanda kan kalaman Rabi'u Musa Kwankwaso
- Lauyoyin sun bayyana damuwa kan yadda ake zargin Kwankwaso da tsoma baki a shari’ar zaɓen gwamnan Kano a 2019
- Kungiyar ta ce ikirarin samun kusanci da alkalan Kotun Koli na iya girgiza amincewar jama’a ga ‘yancin bangaren shari’a da tsarin dimokuraɗiyya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta amince da rubuta koke ga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya kan kalaman Rabi'u Musa Kwankwaso.
Kungiyar ta ce za ta tura korafin ne ga yan sanda da sauran hukumomin tsaro kan zargin tsoma baki a shari’ar zaben Kano a 2019 da ya ce ya yi.

Source: Facebook
Kalaman Kwankwaso sun jawo matsala
Wannan mataki ya biyo bayan kalaman da ake danganta wa tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, game da shari’ar zaben gwamna ta 2019 a jihar, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
INEC ta dauki bangare 1 a rikicin PDP, ta yi zama da shugabannin jam'iyyu a Abuja
An yanke wannan shawara ne a taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC) na NBA da aka gudanar a Maiduguri, inda aka tattauna batun sosai.
A cewar mahalarta taron, mambobin NEC sun nuna damuwa mai tsanani kan kalaman Rabiu Kwankwaso da ke nuni da hulɗa da alkalan Kotun Koli.
A wajen wani taro, tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya ya bayyana yadda ya ja Abba Kabir zuwa gidajen alkalan Kotun koli lokacin shari'ar zaben 2019.
Duk da gana wa da alkalan da ya yi, jam'iyyar APC da Abdullahi Ganduje ne suka yi nasara.
Kungiyar ta ce irin wadannan kalamai, ko gaskiya ne ko a’a, na da hatsari ga amincewar jama’a kan ‘yancin kai da sahihancin bangaren shari’a.
NBA ta gargadi cewa ikirarin samun damar kusantar alkalan kotu ba bisa ka’ida ba na iya raunana tsarin shari’ar zabe da dimokuradiyya.
A cikin kudurinta, majalisar ta ce dole ne a dauki mataki cikin gaggawa domin hana wulakanta kundin tsarin mulki da tsarin adalci.

Source: Twitter
Korafin da lauyoyi ke yi kan Kwankwaso
Kungiyar ta ce za ta rubuta koke a hukumance ga ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin binciken duk wanda ya yi irin wadannan ikirari.
NBA ta kara da cewa idan aka gano ikirarin karya ne, to yana da illa sosai ga kasa kuma dole ne a yi watsi da shi karara.
Amma idan bincike ya tabbatar da cewa ikirarin gaskiya ne, to wajibi ne a hukunta duk wanda ke da hannu, bisa tanadin doka.
Lauyoyin jaddada cewa matakin da ta dauka ba zargi ba ne ga kowa, illa neman bincike na gaskiya da kwarewa.
Manufar hakan, a cewar NBA, ita ce kare bangaren shari’a daga siyasa da kuma zargin da ba su da tushe, The Nigeria Lawyer ta ruwaito.
NBA ta nanata cewa babu wanda ya fi karfin doka, komai matsayinsa na siyasa, idan zargi ya shafi mutuncin kotuna.
An kalubalanci Kwankwaso kan wasu kwangiloli
A wani labarin, zarge-zargen da tsohon hadimin gwamnan Kano, Sanusi Surajo Kwankwaso ya yi kan gwamnatin Abba Kabir Yusuf sun fara tayar da kura.
Hadimin Gwamnan Kano, Salisu Yahaya Hotoro ya maida martani, inda ya jefa tambayoyi masu zafi ga kalaman na hannun daman Rabiu Kwankwaso.
Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kadan bayan Gwamna Abba ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC mai mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
