Yaron Ganduje Ya Ziyarci Kwankwaso har Gida yayin da Abba Ya Hade da Ganduje

Yaron Ganduje Ya Ziyarci Kwankwaso har Gida yayin da Abba Ya Hade da Ganduje

  • Ɗan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ziyara har gida
  • Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar rikicin sauya sheƙa a siyasar Kano da ta kai Gwamna ya sauya sheka
  • Jama’a sun tofa albarkacin bakinsu kan jaddada mubaya’ar ɗan Ganduje ga Kwankwaso bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar NNPP

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Abdul’aziz ɗan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ziyara har gida.

Wannan na zuwa ne bayan sauya sheƙar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC, wadda Ganduje ke a matsayin uban jam’iyyar a matakin ƙasa.

Yaron Ganduje, Abdul'Aziz ya ziyarci Kwankwaso
Abdul'Aziz Ganduje yayin ziyarar ban girma ga Rabiu Kwankwaso Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Saifullahi Hassan, hadimin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ne ya tabbatar da ziyarar a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Abin da Ganduje da makusantan Gwamna Abba suka tattauna a Abuja

Ɗan Ganduje ya ziyarci Kwankwaso

A sakon da Saifullahi Hassan ya wallafa, ya bayyana cewa Abdul’aziz ya kai ziyarar ne a matsayin ban girma da kuma jaddada mubaya’arsa ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Duk da ba mu samu labarin abin da aka tattauna ba, jama'a sun ga babban 'dan na Abdullahi Ganduje sanye da jar hula mai nuna alamar tafiyar Kwankwasiyya.

A ‘yan kwanakin nan dai an samu barakar siyasa a jihar Kano, inda Kwankwaso ya sha bayyana takaicinsa kan yadda makusancinsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, wadda Ganduje ke jagoranta.

Kwankwaso ya nuna mamakinsa kan yadda Abba Kabir Yusuf zai bar jam’iyyar da ta ba shi tikitin takarar gwamna.

Ya yi takaicin yadda aka sha wahala sosai kafin a samu nasarar karɓe mulki daga gidan Ganduje a zaben da ya gabata, amma aka mayar masa da kujerar har gida.

Sai dai a lokuta mabambanta, an ji tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yana bayyana aniyarsa ta yin sulhu da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, yana mai cewa sulhu alheri ne ga Kano.

Kara karanta wannan

Bayan shigar gwamna APC, Shettima ya tura roko ga gwamnonin PDP 2 a Arewa

Kwankwaso: Ra’ayin jama’a kan ziyarar ɗan Ganduje

Jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan ziyara, musamman duba da irin rashin jituwar siyasa da ake fama da ita tsakanin Kwankwaso da Ganduje na tsawon shekaru.

Yaron Ganduje ya jaddada mubaya'a ga Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Twitter

Nuraddeen Hussain Adam ya ce:

“Sani kalamu neman albarka yake abokina tun da babu a gida.”

Abubakar Mansur Abubakar ya ce:

“Ya kamata a ba shi takarar dan majalisar tarayya na Dawakin Tofa da Tofa saboda amanar Madugu da ya rike.”

Ibraheem Khaleel Yunusa ya ce:

“Allah ya ƙara haɗa kan manyanmu na Kano da ma ƙasa baki ɗaya.”

Abdul Aziz Yahaya ya ce:

“Ya ku ‘ya ’yan Malam Shehu ku shiga taitayinku, siyasar wannan lokaci daga kauri sai gwiwa.”

An kalubalanci Kwankwaso a Kano

A bya, kun ji cewa musayar yawu ta fara zafi tsakanin magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da ’yan Kwankwasiyya kan batun kwangilolin gwamnatin jihar Kano.

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano kan kafafen sadarwa na zamani, Salisu Yahaya Hotoro, ya fito ya kalubalanci ’yan Kwankwasiyya tare da jefa masu tambayoyi masu nauyi.

Wannan kalubale na zuwa ne biyo bayan ikirarin da ake yi a wasu bangarori na siyasa cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin godiya da butulci ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng