Ana Batun Dokar Zabe, INEC Ta Yi Wa Sababbin Jam'iyyu Rajista daga cikin 171 da Suka Nema

Ana Batun Dokar Zabe, INEC Ta Yi Wa Sababbin Jam'iyyu Rajista daga cikin 171 da Suka Nema

  • Jam'iyyun siyasar da ake da su a Najeriya sun kara yawa bayan hukumar INEC ta amince da yi wa wasu sababbi rajista
  • Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan ya bayyana cewa sun bukatar neman rajista daga wajen kungiyoyi 171
  • Farfesa Amupitan ya bayyana cewa an zaftare wasu daga cikin masu neman rajistar a matsayin jam'iyyun siyasa yayin da ake aikin tantancewa

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta amince da bukatar wasu kungiyoyi masu neman yin rajista a matsayin jam'iyyun siyasa.

Hukumar INEC ta yi rajista ga sababbin jam’iyyun siyasa guda biyu daga cikin wadanda suka nemi bukatar hakan a wajenta.

INEC ta yi wa sababbin jam'iyyu rajista
Hukumar hukumar zabe ta INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta ce shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

APC ta ce Sheikh Pantami zai taka rawa yayin sabunta katin jam'iyya a Gombe

Farfesa Joash Amupitan ya bayyana hakan ne yayin taron shawarwari na farko na yau da kullum da hukumar ta yi da jam’iyyun siyasa a birnin tarayya Abuja.

Wadanne jam'iyyu INEC ta yi wa rajiata?

Sababbin jam’iyyun da aka yi wa rajista su ne: Democratic Leadership Alliance (DLA) da Nigeria Democratic Congress (NDC), jaridar The Nation ta kawo labarin.

Farfesa Amupitan ya ce an yi rajistar ne bayan tsauraran matakan tantancewa, bayan da hukumar ta karɓi takardun neman rajista guda 171 daga ƙungiyoyi da ke neman a amince da su a matsayin jam’iyyun siyasa.

A cewar shugaban na hukumar INEC, kungiyoyi 14 ne suka tsallake matakin tantancewar farko.

"Daga cikinsu, takwas sun samu nasarar ɗora takardunsu a shafin yanar gizo na musamman na hukumar.”
"Ƙungiyoyin su ne: All Democratic Alliance (ADA), Citizens Democratic Alliance (CDA), Abundance Social Party (ASP), African Alliance Party (AAP), Democratic Leadership Alliance (DLA), Green Future Party (GFP), National Democratic Party (NDP) da Peoples Freedom Party (PFP)."
"Daga cikin waɗannan takwas, guda biyu kacal ne suka cancanci tantancewa ta karshe da tabbatar da cikakken bin kundin tsarin mulki da dokar zaɓe.”

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Katsina ya girgiza majalisa, ta mika bukata wajen Tinubu

- Farfesa Joash Amupitan

An zaftare wasu wajen tantancewa

Ya bayyana cewa bayan kammala bita ta karshe, jam’iyyar DLA ce kaɗai ta cika dukkan sharuddan doka.

“Saboda haka, hukumar ta yanke shawarar yi wa Democratic Leadership Alliance (DLA) rajista a matsayin jam’iyyar siyasa."

- Farfesa Joash Amupitan

Hukumar INEC ta amince da yi wa sababbin jam'iyyu rajista
Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan da sauran wasu jagororin hukumar Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Kotu ta ba INEC umarni

Amupitan ya kuma kara da cewa za a yi wa Nigeria Democratic Congress (NDC) rajista ne bisa umarni daga kotu da ya wajabta wa hukumar yin hakan.

“Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a Lokoja, jihar Kogi, a shari’a mai lamba FHC/LKJ/CS/49/2025 tsakanin Barr. Takori Mohammed Sanni da wasu v. INEC, ta umurci hukumar da ta yi wa Nigeria Democratic Congress (NDC) rajista a matsayin jam’iyyar siyasa."
"Hukumar ta yanke shawarar bin umarnin kotun, kuma ana yi wa jam’iyyar rajista a hukumance. Za a miƙa takardar shaidar rajista ga sababbin jam’iyyun siyasa guda biyu a lokacin da ya dace.”

- Farfesa Joash Amupitan

Kara karanta wannan

Wike ya shiga tsilla tsilla, APC ta fadi matsayinsa wurinta kan rigima da Fubara

Majalisa ta yi gyara a dokar zabe

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta amince da kudirin yin gyara ga dokar zaben Najeriya ta shekarar 2022.

Majalisar dattawa ta kammala aiki kan gyare-gayren da aka yi wa dokar, tare da amincewa da sabuwar dokar zabe ta 2026.

Daga cikin manyan gyare-gyaren da aka yi akwai rage lokacin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke da shi na fitar da sanarwar gudanar da zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng