Bidiyo: 'Pantami Ya Ga abin da Bai Taba Gani ba' a Wajen Sabunta Rajistar APC

Bidiyo: 'Pantami Ya Ga abin da Bai Taba Gani ba' a Wajen Sabunta Rajistar APC

  • Sakataren tsare-tsaren APC a Gombe ya soki Sheikh Isa Ali Pantami a fili kan rashin ziyartar ofishin jam’iyya duk da mukamin da ya rike
  • A cikin bidiyon da ya bazu a shafukan sada zumunta, sakataren ya nuna cewa duk masu yabon Pantami karya suke yi, kowa haushinsa yake ji
  • Yayin da 'yan Najeriya suka yi martani, Sheikh Pantami ya kare kansa, ya bayyana cewa shi dan siyasar boye ne kuma ya dade a jam'iyyar APC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gombe - Bidiyon fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Isa Ali Pantami a ofishin jam'iyyar APC na mazabarsa yayin sabunta rajistar zama dan APC ya jawo ce-ce-ku-ce.

A cikin bidiyon da ya bazu a shafukan sada zumunta, an ga sakataren tsare-tsaren na APC ya yi wa Pantami tatas, duk kuwa da cewa akwai dandazon jama'a a ofishin.

Kara karanta wannan

Rigi-Rigi: Muhimman abubuwan sani game da marigayi Sheikh Khalifa Usman Kusfa

Sakataren APC ya yi wa Pantami tatas kan rashin zuwa ofishin jam'iyya.
Sheikh Isa Ali Pantami a lokacin da ya karbi katin shaidar zama dan jam'iyyar APC da ya sabunta. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Sakataren gudanarwar APC ya soki Isa Pantami

Sakataren APC

Wani matashi, Aliyu Nizam, da ya wallafa bidiyon a shafinsa na X, ya ce:

"Yau Pantami ya ga abin da bai taba gani ba, lallai ku kalli bidiyon nan har karshe."

Legit Hausa kuwa, ta kalli bidiyon tun da farko har karshe, inda ta tsakuro maganganun da sakataren jam'iyyar na APC, Ibrahim Musa Bakas ya fadawa Pantami:

"Farfesa, mutum biyu zuwa uku sun yi magana a kanka, duk karya suke. Duk dakin taron nan, idan dai 'yan majalisar zartarwa ne, suna jin haushinka. Saboda jam'iyya ka yi wa laifi, alheri kuma a ajiye shi a gefe."

Ibrahim Musa Bakas ya furta wannan magana ne a yanayi na fushi-fushi, game da batun rashin ziyartar ofishin jam'iyya da tsohon ministan yake yi.

"Kowa haushinka yake ji" - Bakas ga Pantami

Sakataren tsare-tsaren APC, ya fito fili ya fadawa Sheikh Pantami gaskiya game da yadda shugabannin jam'iyyar suke kallonsa, inda ya fada masa cewa kowane shugabba yana jin haushinsa.

Kara karanta wannan

An yi musayar kalamai bayan rigima ta barke tsakanin APC da tsohon shugabanta na kasa

"Saboda jam'iyya ka yi wa laifi, alheri kuma a ajiye shi a gefe. Sai dai idan an tashi a nan, kowa ya yafe, ya mayar da abin a zuciyarsa, Isa Ali Pantami ya zo ofishin jam'iyya.
"Amma duk karya ne, ana ta luguiguita ka, duk karya ne, kowa haushinka yake ji. Saboda abin da yake faruwa shi ne, ka rike abin da babu wanda ya rike a nan 'yan Gombe, kuma kana tutiya kai dan jam'iyyar APC ne amma ba ka taba zuwa ofishi ba, kuma mutane ba za su fada maka gaskiya ba."

- Ibrahim Musa Bakas.

Jam'iyyar APC ta kuma yaba wa Pantami

Duk da fadin wadannan kalamai, sakataren ya amince cewa Pantami ya taba yi wa jam’iyyar alheri a baya, yana mai cewa ya kawo gudunmawar da ba a taba samu ba.

A nasa bangaren, Sheikh Isa Ali Pantami ya ce yan APC sun kasu kashi biyu, akwai wadanda suke bayyane da kuma masu farin kaya, yana mai cewa shi yana cikin masu farin kaya.

A wani bidiyo da Abba Sani Pantami ya wallafa a Facebook, malamin ya kara da cewa wasu na dauka cewa yanzu ne ya shiga siyasa, amma ba haka ba ne, domin tun 2001 yake harkokin siyasa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Bangaren Turaki ya yi bambami bayan INEC ta watsa musu kasa a ido

Sheikh Isa Ali Pantami ya ce ya dade a cikin jam'iyyar APC kuma shi dan siyasar boye ne.
Sheikh Isa Ali Pantami ya na jawabi a lokacin da yaje sabunta rajistar zama dan APC a Gombe. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Martanin 'yan Najeriya kan bidiyon Pantami

'Yan Najeriya sun yi martani kan wannan bidiyo na Pantami a ofishin APC, kuma Legit Hausa ta zakuro wasu ra'ayoyin jama'a a karkashin bidiyon da Imran U. Wakili ya wallafa a shafinsa na X.

@NazifMusah:

"Hmm! Mutum abin tsoro ne. Kuma babu mamaki gaskiya ne yake fada."

@zeeboy72:

"Irin wadannan mutanen aka rasa a siyayasar."

@SaniDankaka4:

"Pantami ne dan takarar mu a Gombe kuma shi za mu zaba."

A zantawar Legit Hausa da wani matashin mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Arewa, Nura Haruna Maikarfe, ya ce ma damar mutum ya shiga siyasa, to babu irin abin da ba zai gani ba.

Nura Haruna ya ce:

"Siyasa dai ra'ayi ce, da Malamin ka da babanka duk suna iya fitowa takara amma baka isa ka tilasta mutane su zaɓe su ba.
"Sheikh Pantami ya na da 'yancin ya fito ya yi takara, dimokuradiyya ta bashi dama, don haka ban ga aibun hakan ba, sai dai, ba za a hana a kushe shi ba, ba za a hana a fada masa irin maganganun da ake fadawa 'yan siyasa ba.

Kara karanta wannan

Yadda Sheikh Pantami ya ki amsa wa Tinubu da aka yi masa tayin mukaman gwamnati

"Masu cin mutuncin wasu don sun nuna bai kamata ya shiga takara ba, kamar ba su fahimci siyasa ba ne, ita ai ta gaji kushe, yarfe, banbadanci da sauransu, shi yasa har ma sojojin baka ke samu na cin abinci don kare iyayen gidansu."

Nura ya ce a kyale kowa ya yi takararsa, kuma a kyale mutane idan suna kushe dan siyasa ko da kuwa malami ne, domin siyasa rigar 'yanci ce.

APC ta ce Pantami zai yi rawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani sakataren tsare-tsaren na APC a Gombe, Ibrahim Musa Bakas ya ce Sheikh Isa Ali Pantami zai taka rawa yayin da ya je ofishin jam'iyya.

Ibrahim Musa Bakas ya ce duk da cewa an san Sheikh Pantami da ilimin addini da na zamani, siyasa na da nata dabi’un, don haka, za a sanya kida ya taka rawa.

Sakataren jam'iyyar na APC ya kara da cewa tunda Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya taka rawa, ba wanda zai ki yin hakan saboda siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com