Jam'iyyar PDP Ta Samu Koma baya, Sanatocin Jihar Taraba Sun Sauya Sheka zuwa APC

Jam'iyyar PDP Ta Samu Koma baya, Sanatocin Jihar Taraba Sun Sauya Sheka zuwa APC

  • Sanatoci biyu daga Jihar Taraba da daya daga jihar Filato sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC sakamakon rikicin cikin gida dake addabar PDP
  • Jam’iyyar APC yanzu tana da rinjayen kujeru sama da 80 a majalisar dattawa yayin da jam’iyyar hamayya ta PDP ke fuskantar barazanar zagwanyewa
  • Shugaban marasa rinjaye ya soki matakin sauya shekar inda ya bayyana shi a matsayin cin amanar talakawan da suka zabi yan majalisar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Siyasar Majalisar Dattawan Najeriya ta kara canzawa a yau 4 ga watan Fabrairu, 2026, sakamakon ficewar sanatoci biyu daga jihar Taraba daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Sanata Haruna Manu (Taraba ta Tsakiya) da Sanata Shuaibu Isa Lau (Taraba ta Arewa) sun aike da wasiƙun murabus ɗinsu ga shugaban majalisar, inda suka bayyana matsalolin cikin gida na PDP a matsayin dalilinsu.

Kara karanta wannan

Majalisar Amurka ta ki hakura, za a kuma zama kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

'Yan majalisar dattawa 2 daga Taraba sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Zauren majalisar dattawan Najeriya a lokacin da 'yan majalisa ke gudanar da zama. Hoto: @SenateNGR
Source: Facebook

'Yan majalisar Taraba sun bar PDP zuwa APC

Wannan sauya sheka na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan siyasa ke sake lissafi domin fuskantar babban zaɓen shekarar 2027 dake tafe, in ji rahoton The Punch.

Sanata Haruna Manu ya bayyana cewa "rikicin cikin gida wanda ba za a iya sasantawa ba" ne ya tilasta masa barin jam'iyyar PDP.

A cikin wasiƙarsa, ya jaddada cewa zai fi samun damar gudanar da ayyukan ci gaba ga al'ummarsa idan yana ƙarƙashin inuwar jam'iyya mai mulki ta APC.

Haka ma Sanata Shuaibu Isa Lau ya bayyana cewa manufofin jam'iyyar APC sun yi daidai da burinsa na yi wa al'ummar Taraba ta Arewa hidima yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa:

“Na zo gaban wannan zaure ne domin sanar da ficewata daga PDP zuwa APC nan take domin yi wa ƙasata aiki cikin inganci.”

Raguwar tasirin jam'iyyar PDP a majalisa

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Atiku ya yi ganawar sirri da babban Sanatan APC Abdulaziz Yari

Wannan sauya sheka ta jefa jam'iyyar PDP cikin mawuyacin hali, inda yawan kujerunsu a majalisar dattawa ya ragu zuwa 21 kacal.

A farkon majalisa ta 10, PDP tana da kujeru 36, amma yanzu APC ta mamaye majalisar da kujeru 81, wanda hakan ke nuna rashin tasirin hamayya mai ƙarfi.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sanata Abba Moro, ya bayyana takaicinsa, inda ya kwatanta matakin a matsayin "cin amanar zaɓen da jama'a suka yi musu."

Ya bayyana cewa abin baƙin ciki ne yadda abokan aikinsa suka "gano" cewa APC jam'iyya ce mai ci gaba bayan an riga an kammala zaɓe.

APC ta kara karfi da shigowar Sanata Pam

Baya ga sanatocin Taraba, Sanatan Plateau ta Arewa, Pam Dachungyang, shi ma ya bar jam'iyyar ADP ya koma APC sakamakon rikicin cikin gida na jam'iyyarsa.

Sanata Godswill Akpabio ya yi barkwanci da sanatocin Taraba suka bar PDP zuwa APC.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio kan kujerarsa a Abuja. Hoto: @SenGodswill
Source: Twitter

Dachungyang ya bayyana cewa rikice-rikicen dake cikin ADP sun hana shi gudanar da ayyukansa na wakilcin jama'a yadda ya kamata a majalisar, kamar yadda muka rahoto.

Bayan karanta wasiƙun, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya buƙaci jam'iyyar APC da ta kula da yawan mambobinta domin guje wa rikicin cikin gida.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi lalata da mata, sun tatsi talakawa a Cross River? Gaskiya ta fito

Ya yi barkwanci da cewa ƴan tsirarun jam'iyyun hamayya da suka rage yanzu suna zura ido ne kawai domin neman damar shiga jirgin jam'iyya mai mulki, in ji rahoton Vanguard.

Sanata Abba Moro dai ya soki matakin sauya shekar inda ya bayyana shi a matsayin cin amanar talakawan da suka zabi yan majalisar a karkashin jam'iyyun da suka bari.

Yanayin kason kujerun majalisa tsakanin jam'iyyu

Bayan waɗannan sauye-sauyen sheka, ga yadda jadawalin ƙarfin jam'iyyu yake a majalisar dattawan Najeriya a halin yanzu:

Jam'iyya

Adadin Kujeru

APC

81

PDP

21

LP

2

ADC

1

NNPP

1

APGA

1

'Matsalar da APC za ta samu' - Ndume

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume, ya yi tsokaci kan yawan sauya shekar da ake yi zuwa APC.

Sanata Ndume ya yi gargadin cewa APC mai mulki na iya shiga mummunar matsala saboda yawan sauya shekar gwamnoni da ‘yan majalisa daga jam’iyyun adawa zuwa cikinta.

'Dan majalisar dattawan ya bayyana cewa yawancin masu sauya sheka ba sa bada wata gudunmawar a zo a gani bayan shigowa cikin jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com