PDP Ta Samu Nakasu a Arewa, Tsohon Gwamna Ya Yi Murabus daga Jam’iyyar
- Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, ya fice daga jam’iyyar PDP, yana zargin rikice-rikicen cikin gida da ba sa ƙarewa
- Sanata Suswam ya ce PDP ta rasa haɗin kai, dimokuraɗiyyar cikin gida da tsari, ta koma jam’iyya mai fama da rikici mara mafita
- Babban 'dan siyasar ya bayyana cewa bai ƙara iya daidaita kasancewarsa a PDP da akidarsa ta siyasa da burinsa na gina ƙasa ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Suswam ya yi murabus daga jam’iyyar yana mai cewa rikice-rikicen cikin gida da ba su da ƙarshe ne suka tilasta masa yanke wannan shawara.

Source: Facebook
Tsohon gwamna Suswam ya yi murabus
Hakan na cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 4 ga Fabrairu, 2026, wadda ya aike wa shugaban PDP na Mbagber a ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue, cewar Punch.
A cewarsa, tsawon shekaru da dama PDP ta ba shi dama ya yi wa Najeriya hidima ta fannoni daban-daban, ciki har da zama dan majalisar wakilai, gwamnan jihar Benue, da kuma sanata.
Ya ce yana matuƙar godiya ga damar da aka ba shi da kuma amincewar da jam’iyyar ta nuna masa a lokuta daban-daban na rayuwarsa ta siyasa.
Sai dai Suswam ya bayyana cewa jam’iyyar PDP, wadda a da ta kasance alamar haɗin kai, dimokuraɗiyyar cikin gida da adawa mai ƙarfi, yanzu ta fada cikin rikice-rikice masu ɗorewa da ba a iya warwarewa.
Ya ce rikice-rikicen suna shafar jagoranci, ladabi da akidar jam’iyyar, kuma an bar su suna ƙaruwa ba tare da wata sahihiyar hanya ta warware su ba.

Source: Facebook
Kokarin sulhu da Suswam ya yi
Tsohon sanatan ya ƙara da cewa duk da yawan ƙoƙarin sulhu, kafa kwamitoci da kuma alkawuran da aka yi a bainar jama’a, PDP na ci gaba da kasancewa cikin matsanancin rikici.
Ya bayyana halin jam’iyyar da cewa kamar cibiyar da ke cikin dakin jinya ta siyasa, wadda ba ta da cikakken bincike kan matsalarta kuma babu tsayayyen shirin da magance matsalar.
Suswam ya jaddada cewa jam’iyyun siyasa ya kamata su zama tushe na tunani, ladabi da tattaunawa mai amfani, ba filin yaƙi ba.
A cewarsa, abin takaici, halin da PDP ke ciki a yanzu bai dace da waɗannan ƙa’idoji ba, kamar yadda TheCable ta ruwaito.
“Saboda haka, na ga ya dace cikin mutunci in janye, ina kuma yi wa jam’iyyar fatan alheri, idan har wata rana za ta samu jarumta da haɗin kai don warware matsalolinta na cikin gida.”
- In ji Suswam.
Tsohon gwamna, Duke ya shiga ADC
Kun ji cewa jam'iyyar hadaka, ADC ta yi kamun da ake hasashen zai kara mata karfi a jihar Cross River gabanin babban zaben shekarar 2027.
Tsohon gwamnan Cross River, Donald Duke ya tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa jam'iyyar ADC a hukumance yau Juma'a a Kalaba.
Shugabannin tafiyar hadaka ta ADC sun yi kira ga 'yan Najeriya da su hada kai da ita domin ceto kasar daga gurbataccen mulkin jam'iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

