Shugaban APC Ya Cika Baki, Ya Sace Gwiwoyin Atiku da Sauran 'Yan Jam'iyyar ADC
- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya nuna cikakken kwarin gwjwarsa kan babban zaben shekarar 2027
- Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ba za ta iya kawo wani kalubale ba ga tasirin APC idan aka yi karo
- Ya bayyana cewa tururuwar da gwamnonin adawa ke yi zuwa APC, alama ce da ke nuna irin karfin da jam'iyyar take da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana kan tasirin jam'iyyar ADC mai adawa.
Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce jam’iyyar ADC ba ta da karfin da za ta iya kalubalantar APC gabanin zaɓen da za a yi shekarar 2027.

Source: Twitter
Nentawe Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 3 ga watan Fabrairun 2026 yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Tv.
Nentawe Yilwatda ya raina tasirin ADC
Farfesa Nentawe ya raina karfin tasirin siyasar manyan mutanen da ke jagorantar haɗakar jam’iyyun adawa a ƙarƙashin ADC.
"ADC ko kadan ba tsarar APC ba ce. Duk mutum daya da suke da shi, mu muna da mutum biyar ko shida irinsa.”
- Farfesa Nentawe Yilwatda
Haka kuma, ya yi watsi da tasirin siyasa da wasu jagororin adawa ke da shi, ciki har da shugaban ADC na kasa kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.
"Idan suna da David Mark a matsayin tsohon shugaban majalisar dattawa, mu kuma muna da Ahmad Lawan, muna da tsofaffin shugabannin majalisar dattawa guda biyu daga Kudu maso Gabas.”
- Farfesa Nentawe Yilwatda
Shin da gaske APC na tilasta wa ma'aikata?
Shugaban APC ya kuma yi watsi da ikirarin cewa jam’iyyar mai mulki na fuskantar matsin lamba ko barazana daga haɗakar jam’iyyun adawa, yana mai jaddada cewa APC ba ta taɓa tilasta wa ma’aikatan gwamnati shiga jam’iyyar ba.
"Ba mu taɓa roƙon kowa ba, ba mu taɓa neman wani ma’aikacin gwamnati ba. Babu wanda aka tilasta masa ta wasiƙa ko ta baki. Idan aka kawo min bidiyo guda ɗaya da ke nuna hakan, zan nemi afuwa.”
"Wataƙila 'yan adawa ne ke tilasta wa ma’aikatan gwamnati shiga jam’iyyunsu domin su kara yawa.”
- Farfesa Nentawe Yilwatda

Source: Facebook
Shugaban APC bai damu da tasirin ADC ba
Yilwatda ya kuma ce APC ba ta damu da irin manyan ’yan siyasar adawa da ke cikin ADC ba, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar wakilai, Aminu Tambuwal, Peter Obi da Rauf Aregbesola.
A cewarsa, ci gaba da shigowar gwamnoni daga jam’iyyun adawa zuwa APC hujja ce da ke nuna cewa har yanzu ita ce jam’iyyar siyasa mafi ƙarfi da ake tsoro a ƙasar nan.
Amfanin tazarcen Tinubu a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi tsokaco kan amfanin tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Gwamnan na Katsina ya ce sake zaben Shugaba Tinubu a shekarar 2027 zai ba jihohi da kananan hukumomi damar ci gaba da kai wa al’umma romon dimokuradiyya a yankunansu.
Ya bayyana cewa tun bayan hawan shugaban kasar kan kujerar mulki, yana sakin kudade ga jihohi da kananan hukumomi ba tare da jinkiri ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

