Kwankwasiyya Ta Yi Karin Haske a kan Zargin Kwankwaso zai koma APC

Kwankwasiyya Ta Yi Karin Haske a kan Zargin Kwankwaso zai koma APC

  • Kwankwasiyya ta bayyana mamaki a kan labarin da ke cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya zauna da APC don sauya sheka
  • Kungiyar ta ce babu wata buƙata ko sharadi da Kwankwaso ya gindaya domin komawa jam’iyyar APC kamar yadda ake cewa
  • Kwankwasiyya ta bayyana cewa labarin kirkirarre ne, kuma akwai dalilin da ya sa aka fitar da shi don cimma wata manufa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kungiyar Kwankwasiyya ta musanta rahotannin da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai a kan shirin sauya shekar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa APC da Kwankwaso sun saka labule domin a cimma matsaya wajen batun sauya sheka.

Kwankwasiyya ta karyata cewa Kwankwaso ya nemi ya koma APC
Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar Kwankwasiyya ta bayyana cewa wannan kirkirarren labari ne marasa tushe, kuma an yi su ne da gangan domin juyar da hankulan jama'a.

Kara karanta wannan

Bayan Abba, Kwankwaso ya shiga tattaunawa da APC kan sauya sheka? Gaskiya ta fito

Kwankwasiyya ta karyata batun sauya shekar Kwankwaso

Jaridar Daily post ta ruwaito cewa wannan martani ya biyo bayan sauya sheƙar da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi zuwa APC.

Sauya shekar ta jawo wasu rahotanni da ke da’awar cewa an taɓa yunƙurin sulhu ko tattaunawa tsakanin APC da jagoran Kwankwasiyya.

Sai dai an ruwaito cewa amma aka ce ta ci tura ne sakamakon wasu manyan buƙatu da aka jingina wa Kwankwaso.

Kwankwasiyya ta yi gargadin a daina yada karya
Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da kakakin ƙungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed, ya fitar, Kwankwasiyya ta bayyana waɗannan zarge-zarge a matsayin jita-jita da aka yi bisa zato.

Ya ce Sanata Kwankwaso bai taɓa shiga wata tattaunawa, zama ko shawarwari da APC, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ko wani wakili ba, dangane da sauya sheƙa ko komawa jam’iyyar mai mulki.

Kwankwasiyya ta yi gargadi kan jita-jita

Sanarwar ta ce Kwankwaso bai taɓa yin wata mu’amala da APC da nufin barin jam’iyyarsa ba, kuma duk wani labari da ke nuna akasin haka ƙarya ce tsagwaronta.

Kara karanta wannan

'Abin da ke jinkirta komawar Kwankwaso ADC bayan Abba ya guje shi a NNPP'

Kungiyar Kwankwasiyya ta nuna damuwa matuƙa kan yadda ake yaɗa rahotannin da ba a tantance ba, musamman ta kafafen yada labarai da ke cewa Kwankwaso ya nemi manyan bukata daga APC.

Ta yi gargaɗin cewa irin wannan salo na iya ɓatar da ra’ayin jama’a tare da ɓata sunan mutane ba tare da hujja ba.

Kungiyar ta yi kira ga ‘yan jarida da gidajen yaɗa labarai da su riƙa bin ƙa’idojin aikin jarida ta hanyar dogaro da sahihan bayanai da amintattun majiyoyi, maimakon yada jita-jitar siyasa.

Mutanen Kwankwaso sun gargadi kakakin Abba

A wani labarin, kun ji cewa shugabancin rikon kwarya na jam’iyyar NNPP ya jaddada cewa ‘ya’yan ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano da suka rasu ne sahihan ‘yan takararsu a zabe mai zuwa.

Jam’iyyar ta ce Nabil Sarki Aliyu Daneji ne ɗan takararta a mazaɓar birnin Kano, yayin da Sa’adu Aminu Sa’adu zai wakilci Ungogo, domin cike guraben da aka samu bayan rasuwar iyayensu

Wannan bayanin na zuwa ne yayin da ake rade-radi da muhawara kan fitowar sunayen ‘yan takara daga ɓangarori daban-daban da Sanusi Bature D-Tofa ya danganta da NNPP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng