APC na Tilasta Ma’aikatan Gwamnati Shiga Jam'iyyar ? An Samu Gaskiya kan Rade Radin

APC na Tilasta Ma’aikatan Gwamnati Shiga Jam'iyyar ? An Samu Gaskiya kan Rade Radin

  • Jam'iyyar APC ta yi karin haske bayan zargin da ake yi mata cewa tana tilasta ma'aikatan gwamnati shiga cikinta
  • APC ta ce zargin ƙarya ne tsantsa, tana zargin ADC da yaɗa bayanan bogi saboda nasarar rajistar jam'iyyar
  • APC ta tsawaita wa’adin rajista daga 31 ga Janairu zuwa 8 ga Fabrairu 2026 saboda dimbin ‘yan Najeriya da suka shiga rajistar da kansu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar APC ta fusata da ake yada rahotanni kan tilasta ma'akatan gwamnatin Najeriya shiga cikinta.

Jam'iyyar ta ƙaryata zargin da jam’iyyar ADC ta yi na cewa ana tilasta wa ma’aikatan gwamnati shiga rajistar mambobin APC ta hanyar intanet.

APC ta caccaki ADC kan rahoton karya
Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Nentawe Yilwatda. Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran APC ta ƙasa, Felix Morka ya fitar ranar Litinin 2 ga watan Faburairun 2026, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

An fara nuna wa juna yatsa kan wanda ya shirya katin rijistar Bello Turji a jam'iyyar APC

A ranar Lahadi 1 ga watan Faburairun 2026, ADC ta yi ikirarin cewa a jihohi da dama ana matsa wa ma’aikatan gwamnati lamba domin su shiga rajistar APC ta intanet da ke gudana a halin yanzu.

APC ta zargi ADC da shirya mata karairayi

Jam’iyyar ta ce wannan zargi ƙarya ne gaba ɗaya kuma ba shi da tushe, tana zargin ADC da ƙoƙarin bata mata suna sakamakon nasarar da APC ke samu a rajistar intanet.

APC ta bayyana cewa wannan zargi na daga cikin yaɗa bayanan ƙarya da ADC ke yi, ciki har da yada wata takardar rajistar APC ta bogi wadda ake ƙoƙarin nuna cewa wani sanannen ɗan ta’adda ya yi rajista da jam’iyyar.

A cewar sanarwar, miliyoyin ‘yan Najeriya ne suka shiga jam’iyyar APC da son ransu, karkashin shirin 'Renewed Hope Agenda', lamarin da ya sa jam’iyyar ta yanke shawarar tsawaita wa’adin rajistar daga 31 ga Janairu zuwa 8 ga Fabrairu 2026.

APC ta caccaki ADC kan yada tilastawa ma'aikata shiga jam'iyyar
Shugaban jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya, David Mark. Hoto: ADC Party.
Source: Twitter

'Musabbabin yada karya da ADC ke yi'

Jam’iyyar APC ta zargi ADC da tsorata sakamakon yadda jama’a suka rungumi rajistar, tare da kira ga jam’iyyar adawa da ta daina yaɗa labaran ƙarya da ƙage.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bi sawun dan kasuwar Kano, sun ɗauke shi a jihar Nasarawa

Sanarwar ta ce:

“Yayin da ADC ke ci gaba da ruɗewa tana yaɗa ƙarya, jam’iyyarmu mai ƙarfi tana ci gaba da nausawa gaba, tana zama abin koyi a Afirka wajen amfani da fasahar zamani da dimokuraɗiyya.”

APC ta jaddada cewa ba za ta bari yaɗa labaran ƙarya su karkatar da ita daga manufofinta na ƙarfafa dimokuraɗiyya da amfani da tsarin zamani a siyasar Najeriya ba, cewar The Nation.

Turji: APC ta zargi ADC kan katin jam'iyya

Kun ji cewa an fara nuna wa juna yatsa tsakanin APC da ADC game da rahoton yi wa Bello Turji katin zama dan jam'iyya mai mulki.

Sakataren yaɗa labaran APC, Felix Morka ya ce suna zargin ADC ta shirya katin shaidar da ke nuna Bello Turji ya shiga jam'iyyarsu.

Ya ce jam'iyyar ADC ta tsorata da yadda jama'a ke tururuwar shiga APC shi yasa ta bullo da yada wadannan karerayi domin bata mata suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.