Zance Ya Kare, Shugaban APC na Kasa Ya Warware Batun Canza Kashim Shettima a 2027

Zance Ya Kare, Shugaban APC na Kasa Ya Warware Batun Canza Kashim Shettima a 2027

  • Farfesa Nentawe Yilwatda ya kawo karshen jita-jitar da ake yadawa cewa APC na shirin sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettim a 2027
  • Shugaban APC na kasa ya bayyana cewa jam'iyya ce ke da ikon yanke wanda zai mata takara da wanda ba zai mata ba a dokar zaben Najeriya
  • Yilwatda ya ce duk labaran da ake yadawa game da sauya Shettima ba gaskiya ba ne, ya roki 'yan Najeriya su yi watsi da su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya warware zare da abawa kan zargin cewa ana shirin sauya Sanata Kashim Shettima a zaben 2027.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta fara tattaunawa kan tikitin mataimakin shugaban ƙasa na zaɓen 2027 ba, yana mai cewa duk abin da ake yaɗawa a kafafen watsa labarai jita-jita ne kawai.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro zai rikide zuwa siyasa bayan gwamnatin APC ta ba shi mukami

Mataimakin shugaban kasa.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima yana jagorantar taron NEC a Abuja Hoto: @OfficialSKSM
Source: Twitter

Farfesaa Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 1 ga Janairu, 2027 yayin wata hira da ya yi a tashar Trust TV, wanda Legit Hausa ta bibiya.

APC ta kwantar da hankula kan Shettima

A cewarsa, yawancin labaran da ke yawo a kafafen watsa labarai kan batun sauya mataimakin shugaban ƙasa a zabe mai zuwa ba su da tushe balle makama.

Shugaban APC na kasa ya ce:

“’Yan takara na jam’iyya ne, ba na mutum ɗaya ba. Ko shugaban ƙasa ma, idan ya zama ɗan takara, ɗan takarar jam’iyya ne. Don haka jam’iyya kaɗai ce ke da ikon faɗin wanda zai mata takarar mataimakin shugaban ƙasa.
"Duk wanda ya yi wata magana daban ba jam'iyya ba, jita-jita ce kawai mara tushe.”

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta samun ce-ce-ku-ce da hasashe a taakanin yan Najeriya kan dabarun da jam'iyyar APC ke tunanin amfani da su gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano sun dimauce bayan fashewar abu mai kama da bam

Yadda aka fara jita-jitar sauya Shettima

Legit Hausa ta ruwaito cewa a ‘yan makonnin nan, wasu kafafen watsa labarai da shafukan sada zumunta sun riƙa wallafa labarai da ke nuna cewa APC na shirin sauya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.

Daga cikin sunayen da aka riƙa ambata a matsayin wadanda za su maye gurbin akwai limamim cocin Katolika na Sokoto, Mathew Kukah daga jihar Kaduna, da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara daga jihar Bauchi.

Shugaban APC, Farfesa Nentawe.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentwe Yilwatda Hoto: @Nentawe1
Source: Twitter

Haka kuma, a wani lokaci an yi hasashen cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin daga jihar Kano, na iya maye gurbin Shettima, kamat yadda Punch ta kawo.

Amma a halin yanzu, shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya kawo karshen jita-jitar, inda ya ce labaran da ake yadawa ba gaskiya ba ne.

Shettima ya gayyaci gwamnoni 2 zuwa APC

A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana sauya sheƙar Gwamna Agbu Kefas zuwa APC a matsayin abin alfahari.

Kara karanta wannan

APC na shirin mamaye Najeriya, bayan Abba, wasu gwamnoni za su sauya sheka

Shettima ya kuma mika goyon gayyata zuwa ga gwamnonin jihohin Adamawa da Bauchi, yana mai bayhana fatan su dawo jam'iyyar APC mai mulkin kasa.

Mataimakin shugaban kasar ya ce yana fatan Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa za su sake nazari kan matsayarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262