APC Ta Sake Taso da Batun Sauya Shekar Kwankwaso zuwa cikinta, Ta Fadin Tanadin da Ta Yi Masa
- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sake yin tsokaci kan batun sauya shekar Rabiu Musa Kwankwaso
- Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana matsayar jam'iyyar idan har Kwankwaso ya yanke shawarar barin NNPP da yake ciki
- Hakazalika, shugaban na APC ya kare Mai girma Bola Ahmed Tinubu kan yawan tafiye-tafiyen da yake yi zuwa kasashen waje
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana kan yiwuwar shigowar madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar.
Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce har yanzu kofar jam’iyyar mai mulki hara bude take domin karbar Rabiu Musa Kwankwaso, idan ya yanke shawarar shigowa APC.

Source: Facebook
Shugaban na APC ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wata hira da aka yi da shi a tashar Trust TV a ranar Lahadi, 1 ga watan Fabrairun 2026.
Ana ta rade-radi kan siyasar Kano
Yilwatda ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake samun rade-radi a siyasar jihar Kano, lamarin da ya jawo martani daga Kwankwaso.
Za a iya tunawa cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC a baya-bayan nan, tare da wasu ’yan majalisar dokokin jihar Kano da kuma ’yan majalisar wakilai.
Me shugaban APC ya ce kan Kwankwaso?
Farfesa Nentawe ya ce duk da cewa ba a fara wata tattaunawa ba da tsohon gwamnan na Kano a halin yanzu, amma idan ya yanke shawarar shiga APC, za a karbe shi hannu bibbiyu.
"Kofofinmu a bude suke ga Kwankwaso ya shigo APC. Idan ya zo, muna maraba da shi matuka. Duk da cewa har yanzu ba mu fara tattaunawa da shi ba."
- Farfesa Nentawe Yilwatda
Nentawe ya kare Shugaba Tinubu
Shugaban jam'iyyar ya kuma yi amfani da damar wajen kare yawan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da Shugaba Bola Tinubu ke yi.

Kara karanta wannan
Bayan Abba, Kwankwaso ya shiga tattaunawa da APC kan sauya sheka? Gaskiya ta fito
Ya bayyana cewa gogewarsa, kwarewarsa da alakar da yake da ita a duniya suna ba shi damar cimma manyan nasarori cikin kankanin lokaci.
"Saboda gogewarsa, kwarewarsa da alakar da yake da ita, abin da zai iya kullawa cikin kwana guda, da yawa daga cikinmu sai mun shafe shekaru kafin mu cimma irinsa.”
- Farfesa Nentawe Yilwatda

Source: Twitter
Amfanin tafiye-tafiyen Shugaba Tinubu
Yilwatda ya bayyana tafiye-tafiyen shugaban kasa a matsayin sadaukarwa domin muradun kasa.
Ya bayyana cewa Tinubu na yin irin wadannan tafiye-tafiye ne domin jawo masu zuba jari dava kasashen waje, kulla yarjejeniyoyi tsakanin kasashe, da kuma magance matsalolin tsaro.
"Idan wannan mutum na sadaukar da kansa saboda wannan kasa, yana zagayawa domin jawo masu zuba hannun jari, inganta tsaro da kulla yarjejeniyoyin kasashe, ya dace mu dauki hakan da wasa?"
- Farfesa Nentawe Yilwatda
Gwamna Kefas ya koma jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a hukumance.
Gwamna Kefas ya samu tarba daga wajen jiga-jigan jam'iyyar APC, ciki har da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Shettima ya bayyana sauya shekar a matsayin abin alfahari ga jam’iyyar da kuma kasa baki daya, inda ya yabawa Kefas bisa salon shugabancinsa na hada kan al'ummar jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
