APC Ta Kafa Kwamitin sama da Mutum 70 don Shirin Babban Taron Jam'iyya
- Jam’iyyar APC ta ƙaddamar da kwamitin shirya babban taron ƙasa mai mambobi 73 gabanin taron watan Maris 2026
- Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, shi ne shugaba, yayin da gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ke matsayin sakatare
- Kwamitin ya haɗa manyan gwamnoni, tsofaffin shugabannin majalisa da tsofaffin shugabannin jam’iyyar ta APC a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam’iyyar APC mai mulki ta kafa kwamitin domin shirye-shiryen babban taron ƙasarta wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 27 da 28 ga watan Maris na shekarar 2026.
An bayyana kwamitin, wanda ya ƙunshi mutum 73 a hukumance a ranar Litinin, abin da ke nuna yadda jam’iyyar ke ƙara ƙaimi wajen tanadin taron da ake sa ran zai zama mai matuƙar muhimmanci ga makomar jagorancinta.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa sanarwar ta fito ne daga bakin Sakataren Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, wanda ya bayyana cewa an zaɓi Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, a matsayin Shugaban Kwamitin.
An kafa kwamitin Babban taron APC
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, Shi ne ya zama Sakataren Kwamitin da ke shirya babban taron.
Wannan tsari, a cewar jam’iyyar, na nuni da haɗa manyan ginshiƙai daga sassa daban-daban na ƙasar domin tabbatar da taron ya gudana cikin tsari, adalci da fahimtar juna.
APC ta bayyana cewa babban taron ƙasa na shekarar 2026 zai kasance wani muhimmin mataki na sake fasalin jagoranci da tafiyar da harkokin jam’iyyar, musamman ta fuskar zaɓen sababbin yan kwamitin gudanarwa (NWC).
Sakataren APC na Ƙasa, Ajibola Basiru, ya kuma bayyana cewa Gwamnan Jihar Kwara kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), AbdulRahman AbdulRazaq ne Mataimakin Shugaban Kwamitin. A cewarsa, wannan zaɓi ya nuna ƙoƙarin jam’iyyar na haɗa ƙwarewa, gogewa da wakilci daga dukkannin yankunan ƙasar.
Basiru ya tunatar da cewa tun a shekarar da ta gabata APC ta fitar da cikakken jadawalin gudanar da tarukan ƙananan hukumomi, mazabu, jihohi da shiyyoyi na shekarun 2025 zuwa 2026, waɗanda dukkansninu ke kaiwa ga babban taron ƙasa.
'Yan kwamitin Babban taron APC
Kwamitin ya ƙunshi tarin gwamnoni daga sassa daban-daban na ƙasar, abin da ke nuna tsarin shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa.
Wannan haɗin gwiwa, a cewar APC, zai taimaka wajen tabbatar da cewa an yi la’akari da ra’ayoyi da bukatun yankuna daban-daban yayin shirya taron.
Daga cikin yan kwamitin akwai Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Bassey Eno; Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri da Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia.
Akwai Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum; Gwamnan Jihar Cross River, Bassey Otu da Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori
Sauran sun hada da Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru; Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo; Gwamnan Jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji; da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah.

Source: Twitter
Sauran gwamnoni da ke cikin kwamitin sun haɗa da Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya; Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Akwai Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani; Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda; Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris da Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo.
Sai Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Olusola Sanwo-Olu; Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule; Gwamnan Jihar Niger, Mohammed Umar Bago da Gwamnan Jihar Ogun, Abiodun Adedapo Oluseun.
Akwai Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa; Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang; Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara; Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu; da Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas.
APC ta ƙaryata batun tilastawa ma'aikata rajista
A baya, kun ji cewa APC ta bayyana fusata kan abin da ta kira yaɗa rahotannin ƙarya game da tilasta wa ma’aikatan gwamnatin Tarayya shiga rajistar ƴan jam’iyyar ta intanet.
APC ta ce babu wani tsari ko umarni da ya tilasta wa kowa shiga jam’iyyar, tana mai jaddada cewa dukkannin ƴaƴanta suna shiga ne bisa ra’ayin kansu ba komai ba.
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar ba za ta amince da irin waɗannan zarge-zarge ba, domin suna da nufin rikita hankalin jama’a da ɓata sunan jam’iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


