Sanata Kano Zai Kwace Motocin da Ya Ba Shugabannin NNPP da Suka Bi Abba zuwa APC

Sanata Kano Zai Kwace Motocin da Ya Ba Shugabannin NNPP da Suka Bi Abba zuwa APC

  • Sanata Rufai Hanga ya bayar da umarnin kwace motocin da ya bai wa shugabannin NNPP bayan sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a Kano
  • Wasikar ofishin Sanatan ta bukaci shugabannin kananan hukumomi goma sha biyar dake Kano ta Tsakiya su dawo da motocin jam'iyya zuwa ofishinsa
  • AA Zaura ya yi alkawarin bai wa tsofaffin shugabannin NNPP sabbin motoci masu kyau idan har Sanata Hanga ya dage kan kwace wadanda ya bayar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Sanatan dake wakiltar shiyyar Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga, ya bada umarnin gaggawa ga tsofaffin shugabannin jam’iyyar NNPP na kananan hukumomin shiyyar da su dawo da motocin da aka ba su.

Wannan mataki na zuwa ne sakamakon ficewar shugabannin zuwa jam’iyyar APC mai mulki, biyo bayan canjin shekar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

'Babu gwamnan da zai zauna a NNPP': An fadi babban dalilin Abba na shiga APC

Sanata Rufai Hanga ya na shirin kwace motocin da ya ba shugabannin NNPP da suka koma APC a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf (hagu), Sanata Rufai Sani Hanga (tsakiya, da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso (dama). Hoto: @Kyusufabba, @KwankwasoRM, @SenHanga
Source: Facebook

Kano: Umarnin dawo da motocin jam'iyya

A cikin wata wasika mai dauke da sa hannun sakataren ofishin sanatan, Engr. Ibrahim Nakwalli Kawaji, an umarci tsofaffin shugabannin da su dawo da motocin da ke hannunsu, in ji rahoton Daily Trust.

An umarni tsofaffin shugabannin na NNPP na shiyyar Kano ta Tsakiya su mika motocin zuwa ofishin Sanata Hanga dake lamba 48, titin Sokoto a Nasarawa GRA, Kano.

Wasikar ta bayyana cewa wadannan motoci kadarorin jam’iyya ne da aka bayar domin gudanar da ayyukan NNPP, saboda haka ya zama dole a dawo da su tsakanin 28 zuwa 30 ga watan Janairu, 2026.

Ofishin Sanatan ya jaddada cewa za a ajiye motocin ne har sai an shawo kan rikicin cikin gida na jam’iyyar. Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Dala, Fagge, Gwale, Madobi, Tarauni, da sauran kewayen Kano ta Tsakiya.

Sanata Rufai Hanga ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Bayan Abba, Kwankwaso ya shiga tattaunawa da APC kan sauya sheka? Gaskiya ta fito

“Dole ne a mika motocin kai-tsaye ga shugaban ofishin sanatan, Alhaji Shehu Tijjani Usman Tarauni, domin su mallakar jam’iyya ne.”

AA Zaura ya yi martani kan matakin Hanga

Wannan umarni ya janyo raddi mai zafi daga bangaren siyasar jihar, inda wasu ke ganin matakin bai dace ba, kamar yadda rahoton Aminiya ya nuna.

Fitaccen dan siyasa, Alhaji Abdussalam Abdulkarim (AA Zaura), ta bakin kakakinsa Malam Dahiru Ahmad Maihuddadu, ya bayyana takaicinsa kan matakin Sanatan.

AA Zaura ya bayyana cewa a shirye yake ya samar da wasu sababbin motocin ga dukkan shugabannin da Sanata Hanga ya kwace wa nasu.

Sanata Rufai Hanga ya ce dole shugabannin NNPP da suka koma APC su dawo masa da motocin da ya ba su.
Sanata Rufai Hanga a zauren majalisar dattawa da ke Abuja. Hoto: @SenHanga
Source: Twitter

'Za a ba su motoci mafi kyau'

Maihuddadu ya ce:

“AA Zaura yana a shirye domin ya tallafa wa wadannan shugabanni da motocin da suka fi wadanda suke amfani da su yanzu kyau, domin abin da sanatan ya yi abin takaici ne.”

Shi ma wani mai amfani da kafafen sada zumunta, Sani Gilashi Haruna, ya soki matakin inda ya tuna cewa AA Zaura ya taba raba motoci 44 ba tare da ya taba tunanin kwace su ba ko da bayan ya fadi zabe, saboda ya bayyana su a matsayin tallafi.

Kara karanta wannan

Kwamishinoni 5 da suka yi murabus a gwamnatin Abba suka bi Kwankwaso

Hanga ya gargadi maciya amana a Kwankwasiyya

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sanata Rufa’i Sani Hanga ya ce wadanda suka rika kiran Gwamna Abba Yusuf ya koma APC ba masoyinsa ba ne, illa masu son cin amanar talakawa.

Dattijon ya jaddada cewa bai dace Abba Kabir ya butulce wa Rabiu Musa Kwankwaso ba, duba da irin gudunmawar da Kwankwaso ya bayar a rayuwarsa ta siyasa.

Hanga ya sake tabbatar da tsayuwarsa a jam'iyyar NNPP, yana mai kira ga ’yan Kwankwasiyya da su guji rade-radi da masu zuga jama'a su sauya sheƙa zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com