Mutanen Kwankwaso Sun Gargadi Kakakin Abba kan Batun Takara a Majalisar Kano
- Jam'iyyar NNPP ta ce Nabil Sarki Aliyu Daneji da Sa’adu Aminu Sa’adu su ne sahihan ‘yan takararta a zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokokin Kano
- Rahoto ya nuna cewa NNPP ta bayyana cewa tuni ta aika sunayen ‘yan takarar zuwa INEC domin cike guraben da rasuwar ‘yan majalisa biyu ta bari
- NNPP ta mayar da martani ne bayan kakakin gwamnan Kano ya zargi wasu mutane da ƙoƙarin tayar da rikici ta hanyar gabatar da wasu ‘yan takara
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Shugabancin rikon kwarya na jam’iyyar NNPP ya jaddada cewa ‘ya’yan ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano da suka rasu ne sahihan ‘yan takarar jam’iyyar a zaɓen cike gurbi da za a gudanar.
Jam’iyyar ta ce Nabil Sarki Aliyu Daneji ne ɗan takararta a mazaɓar Kano Municipal, yayin da Sa’adu Aminu Sa’adu ke wakiltar Ungogo, domin cike guraben da aka samu bayan rasuwar ‘yan majalisa biyu da ke kan mulki.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa bayanin na zuwa ne yayin da ake rade-radi da muhawara kan fitowar sunayen ‘yan takara daga ɓangarori daban-daban da Sanusi Bature D-Tofa ya danganta da NNPP.
Matsayar jam'iyyar NNPP kan ‘yan takara
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran NNPP na rikon kwarya, Injiniya Ibrahim Karaye, ya fitar, jam’iyyar ta ce ta bi dukkan matakan doka wajen tsayar da ‘yan takarar.
Karaye ya bayyana cewa an riga an miƙa sunayen Nabil Sarki Aliyu Daneji da Sa’adu Aminu Sa’adu ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, INEC, domin zaɓen cike gurbi da aka shirya gudanarwa a ranar 21, Fabrairu, 2026.
Ya ce duk wani sunan da aka gabatar daga wani ɓangare ba ya wakiltar matsayar jam’iyyar, yana mai cewa NNPP ba ta amince da irin waɗannan matakai ba.
Gargadin NNPP ga kakakin Abba
NNPP ta ce kalaman da kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya yi na cewa fitowar ‘yan takara da yawa daga NNPP ta tabbatar da dalilin sauya sheƙar Abba Kabir Yusuf zuwa APC ba gaskiya ba ne.
Jam’iyyar ta bayyana cewa wannan magana ƙoƙari ne na karkatar da hankalin jama’a da kuma neman hujjar kare wasu matakai da ake kallon sun sabawa jam’iyyar da shugabancinta.
Karaye ya ce maimakon yin irin waɗannan kalamai, ya kamata kakakin gwamnan ya mayar da hankali kan ayyukan ofishinsa da kuma muradun al’ummar Kano.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanusi Bature ya yi ikirarin cewa bangarorin jam'iyyar NNPP sun fitar da 'yan takara uku a zaben cike gurbin da za a yi a Kano.
Batun shugabanci da ɓangarori a NNPP
Sanarwar ta kuma nesanta NNPP daga wasu mutane da ke kiran kansu shugabannin ɓangarori a jam’iyyar, ciki har da Sanata Mas’ud Jibrin Doguwa, wanda jam’iyyar ta ce bai taɓa zama mamba a NNPP ba.
Karaye ya jaddada cewa Hon. Abdullahi Ibrahim Maikano ne ke jagorantar jam’iyyar a matsayin shugaba na rikon kwarya, bisa tsarin da jam’iyyar ta amince da shi.

Source: Twitter
Ya ce ikirarin Hon. Abdullahi Zubairu Abiya na shugabanci ya zama ba shi da inganci tun bayan rushe shugabancin da Dungurawa ke jagoranta da kwamitin gudanarwa na ƙasa ya yi.
Kwanishinonin Abba sun yi murabus
A wani labarin, kun ji cewa wasu daga cikin kwamishinoni a gwamnatin Abba Kabir Yusuf sun yi murabus bayan gwamnan ya koma APC.
Daga cikin wadanda suka ajiye aiki karkashin Abba Kabir akwai Dr Yusuf Ibrahim Kofarmata da Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwamishinoni biyar da suka sauka da mukamansu sun bayyana cewa za su cigaba da kasancewa karkashin tsarin Kwankwasiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


