Bayan Shigowar Abba, Ganduje Ya Faɗi Dacen da Aka Yi na Samun Tinubu a Najeriya

Bayan Shigowar Abba, Ganduje Ya Faɗi Dacen da Aka Yi na Samun Tinubu a Najeriya

  • Tsohon shugaban APC a Najeriya, Dr. Umar Abdullahi Ganduje, ya yi magana game da dacen da ƴan Najeriya suka yi
  • Ganduje ya ce Najeriya ta yi sa’a da samun Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, yana kiran sa ɗan siyasa na gaskiya
  • Ya bayyana cewa Arewa ba ta da wani madadin ɗan takara face Tinubu a 2027, yana mai cewa masu tunanin akasin haka suna kuskure babba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya bayyana tasirin Bola Tinubu a Najeriya.

Ganduje ya bayyana cewa Najeriya ta yi sa’a ƙwarai da samun Bola Ahmed Tinubu, wanda ya mulki jihar Lagos, a matsayin shugaban ƙasa.

Ganduje ya fadi tasirin da Tinubu ke da shi a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da Abdullahi Ganduje. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Twitter

Ganduje ya fadi tasirin Tinubu a Najeriya

Ganduje ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin da wata tawaga ta Shugabannin Matasan Arewa daga jihohi 19 suka kai masa ziyarar girmamawa, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'Masu tunanin 'yan Arewa ba za su zabi Tinubu a 2027 ba sun tafka babban kuskure'

Dan siyasar ya bayyana Tinubu a matsayin ɗan siyasa na gaskiya, yana cewa masu kaɗa ƙuri’a a Arewa za su mara masa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce babu wani ɗan takara mafi dacewa daga Kudancin Najeriya da zai iya jagorantar ƙasar fiye da Tinubu bayan 2027.

Wasu ’yan Arewa sun zargi gwamnatin Tinubu da fifita Kudanci, duk da cewa shugaban ya musanta hakan tare da gabatar da hujjoji.

Tinubu ya ce adadin ’yan Arewa da aka naɗa a mukaman gwamnati ya fi na Kudanci, amma wasu har yanzu ba su gamsu ba.

Ganduje ya bugi kirji kan tazarcen Tinubu a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tinubu: Ganduje ya ja hankalin yan Arewa

Ganduje ya ce masu tunanin cewa Arewa za ta zaɓi wani daban a 2027 suna yin babban kuskure a fahimtarsa.

Ya ce wannan ne karo na farko da Najeriya ta samu shugaban ƙasa wanda rayuwarsa gaba ɗaya ta ta’allaka da siyasa da kishin haɗin kan ƙasa.

Ganduje ya tuna cewa Tinubu ya taɓa gudun hijira domin kare dimokuraɗiyya a Najeriya, yana mai cewa hakan shaida ce ta jajircewarsa.

Ya ƙara da cewa Tinubu ya ɗauki muhimman gyare-gyare, ciki har da cire tallafin man fetur, abin da ya ƙara wa jihohi kuɗaɗen shiga.

Kara karanta wannan

APC na shirin mamaye Najeriya, bayan Abba, wasu gwamnoni za su sauya sheka

Ganduje ya ce dukkan gwamnonin jihohi, ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba, sun amince cewa cire tallafin ya ƙara musu kuɗaɗe.

Ya tabbatar wa Shugabannin Matasan Arewa cewa zai mara musu baya, yana yaba musu kan ƙoƙarinsu na tara kuɗi da goyon bayan Tinubu.

Abba na samun goyon baya da ya shiga APC

Mun ba ku labarin cewa ana ci gaba da maraba da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano bayan ya koma APC mai mulkin Najeriya.

Wata kungiyar tallata manufofin Shugaba Bola Tonubu (BAT-IG) ta bayyana farin ciki da sauya shekar gwamnan Kano zuwa jam'iyya mai mulki.

Ta ce karuwar da APC ke yi a sassa daban-daban na kasar nan alama ce ta yadda jama'a suka amince da salon mulkin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.