Ana Goyon Bayan Shugaban Kasa da Gwamnoni Su Dawo Wa'adi 1 a Najeriya

Ana Goyon Bayan Shugaban Kasa da Gwamnoni Su Dawo Wa'adi 1 a Najeriya

  • Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ce neman wa’adi na biyu na hana shugabanni daukar tsauraran matakai masu amfani ga jama’a
  • ’Yan siyasa, masana doka da kungiyoyin farar hula da dama da sauransu sun bayyana goyon bayansu ga tsarin wa’adi guda mara maimaituwa
  • Masu goyon bayan shawarar sun bayyana cewa hakan na iya rage cin hanci, almubazzaranci da jinkirin aiwatar da muhimman manufofi a fadin kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kalaman Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, kan cewa neman wa’adi na biyu na hana gwamnonin jihohi da shugaban kasa aiwatar da muhimman matakai, sun jawo martani da goyon baya.

Gwamna Bago ya bayyana hakan ne yayin rantsar da sababbin kwamishinoni, shugabannin kananan hukumomi da mambobin wasu hukumomi da kwamitoci a jihar a Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Bayan shiga APC, Abba zai kawo karshen rikicin Sanusi II da Aminu Ado Bayero

Shugaba Bola Tinubu da wasu gwamnoni
Shugaba Bola Tinubu a gefen hagu, wasu gwamnonin APC a gefen dama. Hoto: Bayo Onanuga|Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa gwamna Bago ya ce tsoron rasa tazarce kan sa shugabanni gujewa yanke shawarar da za ta amfani jama’a.

Dalilin kiran wa’adi 1 a Najeriya

A cewar Gwamna Bago, gwamna ko shugaba na iya kin hukunta wasu da suka saba ka’ida ko suka fadi jarabawa saboda tsoron rasa goyon bayan su a zaben wa’adi na biyu.

Punch ta wallafa cewa ya bayyana cewa hakan na janyo tsaiko ga ci gaban jihohi da kasa baki daya, domin shugabanci yana karkata zuwa siyasa maimakon hidimar jama’a.

Saboda haka, ya yi kira da a samar da wa’adi daya tilo ga gwamnonin jihohi da shugaban kasa domin su mai da hankali kan aiki tun daga farko har zuwa karshe.

Wabara ya goyi bayan wa'adi 1 a Najeriya

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Adolphus Wabara, ya ce tsarin wa’adi guda na tsawon shekaru shida zai rage cin hanci da almubazzaranci da ake yi wajen neman wa’adi na biyu.

Kara karanta wannan

Ayyukan da gwamnatin Kano za ta saka a gaba bayan Abba ya koma APC

Ya ce yawancin shugabanni kan tara kudin jama’a ne domin amfani da su a yakin neman zabe maimakon ayyukan ci gaba a kasa.

Wabara ya ce tsarin zai taimaka wajen magance korafin wariya tsakanin yankunan kasa, ta hanyar bai wa kowanne yanki damar rike shugabanci a bisa doka.

Ra’ayoyin masana kan yin tilon wa'adi

Lauya kuma masani, Chief Bolaji Ayorinde, SAN, ya ce maganar gwamna Bago ta tona matsala mai zurfi tsakanin bukatar shugabanci nagari da kuma tsoron rasa mulki.

Ya ce wa’adi guda na iya bai wa shugabanni damar daukar matakai masu tsauri kuma masu muhimmanci ba tare da la’akari da zabe ba, sai dai ya jaddada bukatar karfafa cibiyoyin sa ido da shari’a.

Hakazalika, lauya kuma dan gwagwarmayar kare hakkin bil’adama, Barista Femi Aborisade, ya ce tsarin na iya rage kwadayin cin hanci da sakaci, idan aka hada shi da karfafa majalisa da hukumomin yaki da rashawa.

Gwamna Umaru Bago a majalisar Neja
Gwamna Umaru Bago na yi wa 'yan majalisar Neja bayani. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Twitter

Karin ra’ayoyin kan wa'adi mara tazarce

Tsohon Ministan Ilimi da Lafiya, Farfesa Ihechukwu Madubuike, ya goyi bayan wa’adi guda na shekaru shida, yana mai cewa an taba amincewa da hakan tun a taron kundin tsarin mulki na 1995.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ganduje ya tura wa Kwankwaso goron gayyatar sulhu

Shugaban gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) Jamilu Aliyu Charanchi ya goyi bayan maganar yana mai cewa shugabanni na mayar da hankali kan tazarce da zarar an rantsar da su.

An yi jinkirin gyara dokar zabe

A wani labarin, kun ji cewa kungiyoyin farar hula sun fara magana game da jinkirin gyara dokokin zaben Najeriya da majalisar dattawa ta yi.

Tun a shekarar 2025 majalisar wakilai ta kammala gyara game da dokokin zaben, amma majalisar dattawa ta ce za ta sake nazari a kansa.

Kugiyoyi sun bayyana cewa jinkiri wajen gyara dokokin zai iya shafar sahihancin zaben shugaban kasa da gwamnoni da za a yi a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng