Buba Galadima Ya Kawar da NNPP, Ya Faɗi Jam'iyyar da Za Ta Kayar da Tinubu a 2027

Buba Galadima Ya Kawar da NNPP, Ya Faɗi Jam'iyyar da Za Ta Kayar da Tinubu a 2027

  • Jigon NNPP, Buba Galadima ya ce hadakar jam’iyyun adawa za ta kifar da APC a 2027, yana cewa Bola Tinubu ba zai iya lashe zabe ba
  • Dattijon ya bayyana cewa jam’iyyun adawa sun koyi darasi daga 2023, kuma za su mara wa dan takarar da ya fi farin jini a Najeriya
  • Ya ce NNPP na shirye yin kawance da jam’iyyu masu akida iri daya, yana mai jaddada cewa Rabiu Kwankwaso ne dan siyasar da ke da mabiyan gaske

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jigo a jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima, ya yi magana game da yiwuwar kayar da Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Buba Galadima ya ce hadakar jam’iyyun adawa da ake shiryawa za ta kori APC daga fadar Aso Rock a takarar da za a yi a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sare gwiwoyin 'yan adawa, ya haska dalilan da za su sa APC lashe zabe a 2027

Buba Galadima ya tsoratar da Tinubu kan zaben 2027
Shugaba Bola Tinubu da jigon NNPP, Buba Galadima. Hoto: Bayo Onanuga, Buba Galadima.
Source: Facebook

Buba Galadima ya yi hasashen zaben 2027

Dattijon ya bayyana haka ne yayin wata hira da jaridar Tribune, inda ya ce jam’iyyun adawa sun koyi darasi daga kuskuren zaben 2023.

Ya kara da cewa jam’iyyun adawa za su hada kai su mara wa tikitin da ya fi samun karbuwa da farin jini a tsakanin ‘yan Najeriya.

A cewarsa, shugabannin jam’iyyun adawa na tattaunawa tare da nemo dan takarar da ya fi karfi don fafatawa da Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Ya ce Tinubu ba zai iya lashe zaben 2027 ba ko da yana da goyon bayan gwamnonin jihohi 36 a karkashinsa.

Ya zargi Tinubu da kokarin murkushe adawa, yana mai cewa ko da gwamnonin sun samu dukiya, adawa ba za ta mutu ba.

Da aka tambaye shi kan yiwuwar hadakar Kwankwaso da Peter Obi, Buba Galadima ya ce har yanzu babu tabbaci kan kowanne tsari.

Ya ce ana jin rade-radin tikitin Obi/Kwankwaso ko Jonathan/Kwankwaso, amma ba a yanke hukunci ba tukuna.

Kara karanta wannan

'Dalilin da zai sa yankin Arewa ya yi wa Tinubu ruwan kuri'u a zaben 2027'

Buba Galadima ya ce Tinubu zai fadi a 2027
Shugaba Bola Tinubu a ofishinsa da ke Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

'PDP za ta kayar da Tinubu' - Buba Galadima

Jigo na NNPP ya jaddada cewa zabin dan takara mai karbuwa shi ne zai fi muhimmanci a zaben shekara mai zuwa wato 2027.

'Dan siyasar ya kara da cewa idan PDP ta samu dan takarar da take nema, jam’iyyar za ta kafa gwamnatin tarayya a 2027.

Buba Galadima ya ce rikicin da ke addabar PDP a yanzu zai gushe da zarar lokacin zabe ya karato.

Ya ce PDP ce za ta lashe zaben shugaban kasa a 2027, yana mai cewa Shugaba Tinubu zai bar mulki.

Ya ce:

"“Ina so ku rubuta abin da zan fada, PDP za ta lashe zaben shugaban kasa a 2027. Tinubu zai tafi.”

Kan batun Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Galadima ya ce dole ya mika wa NNPP kundin nasarar da ya samu a 2023.

Ya ce al’ummar Kano sun kada kuri’a ne ga jam'iyyar NNPP, don haka jam’iyyar ce ke da ikon wannan nasara.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tuna bibiyar alkalan kotun koli da ya yi saboda Abba a zaben 2019

Buba Galadima ya kalubalanci Tinubu a 2027

Mun ba ku labarin cewa babba a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi tsokaci kan yawan sauya shekar da 'yan adawa suke yi zuwa APC mai mulki.

Buba Galadima ya bayyana cewa yawan sauya shekar ba za ta sanya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a babban zaben 2027 ba.

Dattijon ya koro bayani kan abin da ya sanya 'yan Najeriya ba za su bari APC ta cigaba da mulkin kasar nan a badi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.