‘Na Hango Shi a Karagar Mulki’: An ‘Fadi’ Gwamnan da Zai Gaji Kujerar Tinubu

‘Na Hango Shi a Karagar Mulki’: An ‘Fadi’ Gwamnan da Zai Gaji Kujerar Tinubu

  • Limamin coci a Najeriya ya bayyana wahayi da ya samu game da wanda zai gaji kujerar shugaban kasa bayan Bola Tinubu
  • Fasto Abel Boma ya bayyana cewa Allah zai yi amfani da Gwamna wajen dawo da martabar Najeriya bayan mulkin Tinubu
  • Limamin ya ce shugabancin Najeriya “yana rataye a kafadar gwamnan”, duk da cewa ba nan take ba ne zai faru

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers – A daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar kalubale, wani shahararren Fasto, Abel Tamunominabo Boma, ya yi hasashen magajin Bola Tinubu.

Fasto Abel ya bayyana cewa Allah ya nuna masa mutumin da zai dawo da martabar ƙasar nan bayan kammala mulkin Tinubu.

Fasto ya hango magajin Tinubu a Najeriya
Fasto Abel Tamunominabo Boma yayin huduba a coci. Hoto: @ProphetBomaAbel.
Source: Twitter

An yi hasashen wanda zai gaji Tinubu

Legit Hausa ta samu wannan bayani daga shafin Faston wanda ya wallafa a shafinsa na X a yau Alhamis 29 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

'Dalilin da zai sa yankin Arewa ya yi wa Tinubu ruwan kuri'u a zaben 2027'

Fasto Boma ya ce Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, shi ne mutumin da Allah ya tanada domin jagorantar Najeriya zuwa girma a nan gaba.

A cewar faston, shugabancin Najeriya “yana rataye a kafadar” Makinde ne bayan wa’adin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kodayake ba nan take ba ne.

Fasto Abel Boma ya ce:

“Yayin da nake magana yanzu, na gan shi (Makinde) yana zaune, Shugaba Tinubu kuma yana kallonsa. Ubangiji ya ce ba nan take ba, amma shugabancin ƙasar nan yana kan kafadarsa.
“Allah yana duba ko’ina, sai ya zaɓi mutum daga jihar da mutane ke ganin ba ta da muhimmanci. Sai Ya ce, ‘A kansa zan dora shugabancin.’ Ban san sunansa ba, ban taɓa ganinsa ba, ban taɓa magana da shi ba, amma shugabancin Najeriya yana rataye a kafadarsa.”

Faston ya ci gaba da bayyana abin da ya gani a wahayi, inda ya ce ya hango Makinde yana zaune kusa da Shugaban ƙasa, yana mai tabbatar da cewa gwamnan daga jihar Yarbawa ne.

A cewarsa:

“Na ga yana zaune kusa da Shugaban ƙasa. Jiha ce ta Yarbawa, ko ba haka ba? Ubangiji ya ce, ‘Ba yanzu ba, amma ka gaya masa cewa shugabancin ƙasar nan yana kan kafadarsa.’”

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tuna bibiyar alkalan kotun koli da ya yi saboda Abba a zaben 2019

Sunan Makinde ya fito game da gadon kujerar Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Seyi Makinde. Hoto: Bayo Onanuga, Seyi Makinde.
Source: Twitter

Wahayin da Fasto ya samu kan Makinde

Fasto Boma ya ce Allah ya nuna masa cewa shugabancin Najeriya zai ci gaba da kasancewa a hannun mutumin Yarbawa, musamman daga Jihar Oyo, Ibadan, kafin daga bisani ya fahimci cewa Makinde ne.

A ƙarshe, Faston ya jaddada cewa babu yadda za a sauya wannan kaddara, ko da kuwa mutane sun yi fushi.

Ya ce:

“Allah bai nuna min mugun mutum ba. Bai nuna min kowa ba face Gwamnan Jihar Oyo.
“Ko da sun sa wani shugaban ƙasa, wannan (Makinde) na nan gaba ne. Wannan wahayi ne na 2026. Allah ya riga ya fara shirya masa hanya. ‘Yan Najeriya ba za su so ba, za su tambaya ‘ta yaya?’ Amma za ku ga yadda Allah ke daidaita komai.”

Fasto ya gano wanda zai yiwa Kwankwaso mataimaki

Kun ji cewa sanannen Fasto a jihar Akwa Ibom ya yi hasashen abin da ya gano a mafarki game da siyasar 2027 da sabon shugaban kasa.

Kara karanta wannan

'Barazanar da Abba Kabir zai fuskanta daga Kwankwaso a 2027 bayan bijire masa'

Fasto Francis Udo ya ce Allah ya nuna masa Rabiu Musa Kwankwaso zai gaji Bola Tinubu, bayan mulkin ya koma Arewa a 2031.

Udo ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio zai kasance mataimakin shugaban kasa a tikitin Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.