Kano: NNPP Ta Dura a kan Masu Neman Mataimakin Gwamna Ya Yi Murabus

Kano: NNPP Ta Dura a kan Masu Neman Mataimakin Gwamna Ya Yi Murabus

  • NNPP ta soki kalaman Kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Ibrahim Abdullahi Wariya a kan buƙatar mataimakin gwamna ya ajiye aiki
  • Jam’iyyar ta ce kundin tsarin mulki ya bai wa Mataimakin gwamna, Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ikon ci gaba da aiki
  • Jam'iyyar NNPP ta gargadi ɓangaren zartaswa da ya kauce wa siyasa, ya mai da hankali kan aikinsa domin ci gaban Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jam’iyyar NNPP ta yi Allah wadai da kalaman Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Waiya, wanda ya buƙaci Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya ajiye aikinsa.

Kara karanta wannan

"Ka nemi yafiya": Tsagin NNPP ya fadi yadda Kwankwaso ya kora Abba APC

Wannan martani na NNPP na zuwa ne a wata sanarwa da kakakin jam’iyyar a jihar Kano, Ibrahim Karaye, ya fitar a ranar Laraba, 29 ga watan Janairu, 2026.

NNPP ba fa ji daɗin kalaman Kwamishinan yaɗa labaran Kano ba
Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya tare da Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo Hoto: Ibrahim A Asiya/Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

BBC ta wallafa NNPP na cewa kalaman kwamishinan ba su da tushe a doka, kuma sun saba wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya.

Jam'iyyar NNPP ta kare Mataimakin Gwamnan Kano

Daily Post ta ruwaito NNPP ta ce tsarin mulki na ƙasar nan har yanzu yana bai wa mataimakin gwamna cikakken iko da damar ci gaba da riƙe mukaminsa har zuwa ƙarshen wa’adin da aka zaɓe shi, matuƙar bai aikata laifi da zai sa a tsige shi ba.

Jam’iyyar ta ce kalaman kwamishinan yaɗa labaran sun zo ne a wani yanayi na siyasa, bayan da mataimakin gwamnan ya ƙi bin gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu manyan muƙarrabansa wajen sauya sheƙa zuwa APC.

NNPP ta bayyana cewa wannan matsaya ta Abdussalam Gwarzo ba laifi ba ne, domin an zaɓe shi tare da gwamnan Kano a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NNPP, kuma hakan ba ya hana shi ci gaba da gudanar da aikinsa.

Kara karanta wannan

A karshe, an ji matsayar Murtala Sule Garo kan sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC

Doka ta ba mataimakin Gwamna ikon aiki - NNPP

Sanarwar ta ƙara da cewa, a bisa doka, babu wani hurumi da kwamishinan yaɗa labarai ke da shi na buƙatar mataimakin gwamna ya ajiye mukaminsa, domin wannan al’amari yana ƙarƙashin ikon kundin tsarin mulki ne kaɗai.

Jam’iyyar NNPP ta kuma buƙaci ɓangaren zartaswa a jihar Kano da ya daina tsoma baki a harkokin siyasa, tare da mai da hankali kan ayyukan da kundin tsarin mulki ya ɗora masa.Ta ce amfani da mukaman gwamnati wajen matsa lamba ko tsoratar da wasu ‘yan siyasa ba zai amfanar da jihar Kano komai ba.

A cewar sanarwar:

“Ci gaba da aikin mataimakin gwamna yana da muhimmanci wajen ɗorewar shugabanci a jihar Kano."

A cewar sanarwar, duk wani yunƙuri na kawo cikas ga ofishin mataimakin gwamna zai iya shafar zaman lafiya da daidaiton tafiyar da mulki.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya yi sababbin nade nade bayan ya koma APC

NNPP ta ce Mataimakin Gwamna na da damar ci gaba da aiki
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Mataimakinsa Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

NNPP ta kuma caccaki kwamishinan yaɗa labaran, tana cewa bai kasance cikin waɗanda suka yi gwagwarmayar kafa gwamnatin NNPP a Kano ba, don haka bai dace ya riƙa yin kalaman da za su iya tayar da hankalin jama’a ba.

Jam’iyyar ta buƙaci kwamishinan da ya ja bakinsa ya yi shiru, ya bar doka ta yi aikinta, tare da girmama kundin tsarin mulkin ƙasa.

Kano: Ana son Mataimakin Gwamna ya yi murabus

A baya, mun wallafa cewa Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya buƙaci Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya yi murabus daga mukaminsa.

Ya bayyana cewa ajiye aiki shi ne zai fi dacewa matukar ba zai iya bin Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyya mai mulki ta APC da gwamnan Kano ya koma ba.

Ibrahim Waiya ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi, inda ya yi tsokaci kan yanayin siyasar da ake ciki a Kano, musamman bayan sauya sheƙar gwamnan jihar zuwa APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng