Kwamishinoni 5 da Suka Yi Murabus a Gwamnatin Abba Suka Bi Kwankwaso
Bayan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, wasu kwamishinoni akalla biyar sun yi murabus sun tsaya da Rabiu Kwankwaso a NNPP.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - A ranar Litinin, 26 ga Janairun 2026 gwamnan jiha Kano, Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC bayan fita daga NNPP.
Wasu daga cikin jami'ansa sun tafi tare da shi zuwa jam'iyyar, yayin da wasu suka bayyana cewa ba za su iya tafiya su bar Rabiu Kwankwaso ba.

Source: Facebook
A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin kwamishinonin jihar Kano da suka ajiye mukamansu a gwamnatin Abba Kabir suka bi jagoran NNPP.
1. Yusuf Kofarmata ya bi Kwankwaso NNPP
Kwamishinan kimiya da fasaha na jihar Kano, Dr. Yusuf Ibrahim Kofarmata ya sanar da yin murabus daga mukaminsa na mamba a majalisar zartarwar jihar Kano.
Ya ce ya dauki matakin ne saboda rashin amincewa da sauyin akida da gwamnatin ta yi daga tafiyar NNPP da Kwankwasiyya da ta kai ta ga nasararta a 2023.
Dr. Kofarmata ya bayyana murabus dinsa ne a wata sanarwa da ya fitar a Facebook a ranar 25, Janairu, 2026, inda ya ce ya dauki matakin ne bayan nazari.

Source: Facebook
Duk da ficewarsa daga gwamnati, Dr Kofarmata ya nuna godiya ga jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa damar da ya ba shi da kuma tafiyar siyasar da suka yi tare.
Haka kuma, ya mika godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa sun yi aiki tare da nufin ciyar da jihar gaba a wani mataki na tarihi.
2. Mustapha Kwankwaso ya yi murabus
Kwamishinan matasa da wasanni na Jihar Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa tare da ficewa daga majalisar zartarwar jihar Kano.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a Facebook, inda ya ce ya dauki matakin duk da nayin da ya ke da shi a gare shi.
A cikin sanarwar, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa damar da ya ba shi na yi wa al’ummar jihar hidima.

Source: Facebook
Ya ce ya amfana matuka daga gogewa da darussan da ya koya yayin da yake rike da mukamin, tare da yabawa da amincewar da aka nuna masa a lokacin da aka nada shi.
3. Kwamishinan jin-ƙai ya yi murabus
Kwamishinan harkokin jin-ƙai da rage talauci na Jihar Kano, Hon. Adamu Aliyu Kibiya, ya yi murabus daga muƙaminsa bayan Abba ya koma APC.
Ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa da ya aikawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya ce murabus ɗin ya fara aiki nan take.

Source: Facebook
A cikin wasiƙar da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook, Kibiya ya bayyana cewa ya fara aiki a matsayin kwamishina tun ranar 29, Yuni, 2023, kuma ya ɗauki matakin yin murabus ne bayan nazari mai zurfi.
4. Kwamishinan tsaron Kano ya yi murabus
Kwamishinan Tsaron Ciki da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, Ibrahim Umar, ya shiga jerin kwamishinonin da suka yi murabus bayan sauya sheƙar Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan
Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC
Punch ta wallafa cewa Ibrahim Umar ya bayyana murabus ɗinsa ne a wata wasiƙa da ya aikawa Abba Kabir, inda ya sanar da cewa murabus ɗin ya fara aiki nan take.

Source: Facebook
A cewarsa, ya ɗauki matakin yin murabus ne sakamakon rashin daidaito da ya taso tsakanin gwamnan jihar da jagoransa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A cikin wasiƙar, Ibrahim Umar ya ce:
“Ina miƙa godiyata ta gare ka, Mai Girma Gwamna, bisa amincewa da ka yi da ni da kuma damar da ka ba ni na yi wa al’ummar Kano hidima.”
5. Nasiru Garo ya yi murabus daga kujerar kwamishina
Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Kano, Nasiru Sule Garo, ya yi murabus daga muƙaminsa, inda murabus ɗin ya fara aiki ba tare da wata-wata ba.
Ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 26, Janairu, 2026, wadda aka aikawa Babban Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG) domin isar da ita ga Gwamnan jihar.

Source: Facebook
A cikin wasiƙar, Sule-Garo ya ce ya ɗauki matakin yin murabus ne bayan ya yi nazari sosai, tare da nuna godiyarsa bisa amincewa da goyon bayan da aka ba shi a tsawon lokacin da yake kan muƙamin.
Daily Nigerian ta wallafa cewa ya ce:
“Ina matuƙar godiya bisa amincewa da goyon bayan da aka ba ni a lokacin aikina. Yi wa al’ummar Jihar Kano hidima abin alfahari ne da gata a gare ni,”
Martanin APC ga Kwankwaso kan Abba
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso martani kan cewa Abba Kabir Yusuf zai fadi zabe a 2027 bayan sauya sheka.
Daraktan yada labaran APC, Bala Ibrahim ya bayyana cewa maganganun Kwankwaso sun fi kama da siyasa maimakon nuna abin da zai faru.
APC ta kara da cewa jam'iyyar tana da farin jini a Kano kuma tsohon gwamna Abdullahi Ganduje zai tattabar da Abba Kabir Yusuf.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


