APC Ta Fusata da Kwankwaso Ya Ce Abba zai Fadi Zabe a 2027, Ta Yi Martani

APC Ta Fusata da Kwankwaso Ya Ce Abba zai Fadi Zabe a 2027, Ta Yi Martani

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC za ta hana shi samun nasara a zaɓen 2027
  • Jam’iyyar APC ta yi watsi da wannan hasashe, tana mai cewa goyon bayan Abdullahi Ganduje zai tabbatar wa gwamnan nasara a zaɓe
  • Sauya sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf ta ƙara zafafa yanayin siyasa a Kano, inda ake ci gaba da sauya layi da matsaya a fadin jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ba zai yi nasara a zaɓen gwamnan Kano na 2027 ba bayan sauya sheƙarsa zuwa APC.

Kwankwaso ya faɗi hakan ne a wata hira, inda ya bayyana sauyin jam’iyyar da gwamnan ya yi a matsayin cin amana ga tafiyar Kwankwasiyya da kuma masu mara masa baya.

Kara karanta wannan

APC, Ganduje sun yi taho mu gama da Kwankwaso kan makomar Abba a 2027

Abdullahi Ganduje ya daga hannun Abba Kabir Yusuf
Yadda Abdullahi Ganduje ya daga hannun Abba Kabir a gidan gwamnatin Kano. Hoto: Abdullahi Ganduje|Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Sai dai Punch ta rahoto cewa jam’iyyar APC ta gaggauta mayar da martani, tana mai ƙin amincewa da hasashen Kwankwaso, tare da bayyana cewa Gwamna Abba Yusuf zai samu nasara a 2027.

Maganar Kwankwaso kan makomar Abba

A hirar da ya yi da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce ficewar Abba Yusuf daga NNPP zuwa APC, da kuma haɗa kai da abin da ya kira tafiyar Gandujiyya, zai raunana karfin gwamnan a idon masu zaɓe.

A cewarsa, Kwankwasiyya tafiya ce da aka gina bisa amincewa da hadin kai, kuma sauya sheƙar gwamnan ya karya wannan ginshiƙi.

Kwankwaso ya yi nuni da cewa masu biyayya ga Kwankwasiyya ba za su bi Abba Yusuf zuwa APC ba, lamarin da, a ganinsa, zai janyo masa shan kashi a zaɓe mai zuwa.

Martanin APC ga hasashen Kwankwaso

A wata hira da manema labarai, Daraktan yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, ya ce kalaman Kwankwaso ba su wuce furuci na siyasa ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Nasarawa ya yi magana kan takarar Tinubu da Shettima tare a 2027

Bala Ibrahim ya ce goyon bayan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ga Abba Yusuf zai zama ginshiƙin nasara a 2027.

Bala ya jaddada cewa Ganduje ya daga hannun ’yan takara da dama a jihohi daban-daban kamar Imo, Kogi da Osun, inda yawancinsu suka yi nasara a zaɓe.

A kan haka ya ce wannan tarihi hujja ce da ke nuna hannun Ganduje yana tare da nasara:

“Goyon bayan Ganduje sau da dama yana kaiwa zuwa ga nasara. Abba Yusuf ba zai zama na dabam da zai kauce wa wannan ka’ida ba,”

APC Kano ta ce tana da farin jini

Daraktan yaɗa labaran APC ya ce jam’iyyar na da karɓuwa a Kano, yana danganta hakan da manufofin gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce ayyukan da ake aiwatarwa karkashin tsarin Renewed Hope Agenda sun ƙara wa APC goyon bayan jama’a, kuma hakan zai taimaka wa jam’iyyar a zaɓen 2027.

Barau Jibrin da Abba Kabir Yusuf a Kano
Sanata Barau Jibrin yayin karbar Abba Kabir Yusuf zuwa APC. Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Ya kuma yi nuni da cewa Kwankwaso ya taɓa fafatawa da APC a baya kuma ya sha kaye, yana mai cewa hakan ba sabon abu ba ne a siyasar Kano.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tuna bibiyar alkalan kotun koli da ya yi saboda Abba a zaben 2019

Batun mataimakin gwamnan Kano

A wani labarin, kun ji cewa kwamishinan yada labaran Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce ya kamata mataimakin gwaman jihar ya yi murabus.

Ya bayyana cewa babu abin da ya fi dacewa da mataimakin gwamna, Aminu Abdulsalam Gwarzo face ya ajiye mukaminsa ya yi gaba.

Amb. Waya ya fadi haka yayin da ake cewa mataimakin gwamnan ya tsaya a jam'iyyar NNPP tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso maimakon shiga APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng