APC, Ganduje Sun Yi Taho Mu Gama da Kwankwaso kan Makomar Abba a 2027
- Zazzafar muhawara ta barke a siyasar Kano bayan Rabiu Kwankwaso ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rufe wa kansa kofar tazarce
- Kwankwaso ya bayyana hakan ne bayan Abba da manyan ‘yan NNPP sun koma APC tare da jaddada kusancinsa da Abdullahi Ganduje
- Abdullahi Ganduje da APC a Kano sun yi watsi da kalaman Kwankwaso, suna cewa iko daga Allah yake fitowa ba daga mutum ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Siyasar Jihar Kano ta ɗauki sabon salo yayin da jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, suka fara magana kan makomar Gwamna Abba Kabir Yusuf a 2027.
Rikicin ya samo asali ne bayan wata hira da Kwankwaso ya yi, inda ya bayyana cewa Abba ya zai samu matsala a zaɓen 2027 bayan ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC tare da haɗa kai da Ganduje.

Source: Facebook
Wasu manyan APC a Kano sun yi wa Sanata Rabiu Kwankwaso martani a hira da suka yi da jaridar Leadership.
Maganar Kwankwaso kan makomar Abba
Kwankwaso ya bayyana ra’ayinsa ne a hirarsa ta farko da BBC Hausa tun bayan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf, ‘yan majalisar dokoki 22 na NNPP a jihar, wasu ‘yan majalisar tarayya da kuma shugabannin kananan hukumomi 44 zuwa jam’iyyar APC.
A cewarsa, wannan mataki ya nuna sauya alkibla daga tafiyar Kwankwasiyya, lamarin da ya sa ya yi imanin cewa hakan zai shafi makomarsa ta siyasa a zaɓen gwamna na gaba.
Ganduje ya yi wa Kwankwaso martani kan Abba
Da yake martani kan kalaman Kwankwaso, Ganduje ya rage tasirinsu, yana mai cewa ikon shugabanci ba na mutum ba ne, daga Allah yake fitowa.
“Allah ne kawai ke ba da iko. Mu yi addu’a kawai mu kai shekarar 2027,”
- Inji Ganduje.
Ya ƙara da cewa sakamakon zaɓe ne kawai zai tabbatar da gaskiya ko akasin haka, yana mai jaddada cewa Allah ne ke zabar shugabanni.
Ganduje ya bayyana haka ne ta bakin hadiminsa, Mohammed Garba, a wata tattaunawa ta wayar tarho, inda ya ce Kwankwaso na fadin ra’ayinsa ne kawai domin ba shi da ikon yanke hukuncin wanda zai ci zaɓe.
APC a Kano ta caccaki Kwankwaso
A nasa bangaren, sakataren yaɗa labaran APC a Kano, Hon. Ahmad Aruwa, ya bayyana kalaman Kwankwaso a matsayin marasa tushe da ma’ana. Ya ce tsohon gwamnan ya rasa karfin tasiri da goyon bayan jama’a a jihar.
Aruwa ya ce sauya shekar Gwamna Abba Kabir da sauran manyan ‘yan siyasa ya nuna cewa Kwankwaso ya rasa rinjaye a siyasar Kano, musamman a yankin Kano ta Kudu.

Source: Facebook
Kwarin gwiwar APC a Kano a zaben 2027
Jam’iyyar APC ta ce tana da cikakken tabbacin samun nasara a 2027, tana mai danganta hakan da shigowar manyan ‘yan siyasa, ‘yan majalisar tarayya, ‘yan majalisar jiha da shugabannin kananan hukumomi cikin jam’iyyar.
Aruwa ya jaddada cewa Abba ya koma APC ne domin samun damar ci gaban jihar Kano da kuma amfani da goyon bayan gwamnatin tarayya, yana mai cewa hakan ya fi wa al’ummar jihar amfani fiye da ci gaba da zama a NNPP.
Buba Galadima ya caccaki Abba Kabir
A wani labarin, mun kawo muku cewa daya daga cikin dattawan NNPP, Buba Galadima ya caccaki Abba Kabir Yusuf kan komawa APC.
Buba Galadima ya bayyana cewa Abba Kabir Yusuf ya nuna tsantsar yaudara ga Rabiu Kwankwaso da mutanen jihar Kano baki daya.
'Dan siyasar ya kara da cewa lura da girman abin da gwamna Abba Kabir ya yi wa Kwankwaso, ya kamata a ba shi kambun butulci na duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


