Gwamnan Nasarawa Ya Yi Magana kan Takarar Tinubu da Shettima Tare a 2027
- Gwamna Abdullahi Sule ya ce tikitin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima zai kasance mai ƙarfi matuƙa a zaɓen 2027
- Ya ce dunkulewar jihohin Arewa ta Tsakiya gaba ɗaya a APC ta ƙara tabbatar da nasarar da jam’iyyar ke hangen samu a zaɓe mai zuwa
- A cewarsa, sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa ne ke jawo ’yan siyasa da dama shiga APC, tare da ƙarfafa tikitin Tinubu/Shettima
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau – Gwamnan Jihar Nasarawa kuma Shugaban Gwamnonin Arewa ta Tsakiya, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa tikitin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima ba zai samu kalubale ba a zaɓen 2027.
Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a birnin Jos na Jihar Plateau, inda ya ce damar sake zaɓen Shugaba Tinubu ta tabbata sakamakon sauyin siyasa da ya faru a yankin Arewa ta Tsakiya.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa gwamna Abdullahi Sule ya wallafa hotunan yadda taron ya guda da wasu bayanai da ya yi a shafinsa na Facebook.
Dunkulewar Arewa ta Tsakiya a APC
Gwamna Sule ya bayyana farin cikinsa kan yadda jihohin Arewa ta Tsakiya suka koma karkashin jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan ya ƙarfafa gwiwar jam’iyyar a matakin ƙasa.
A cewarsa, jihohin Kwara da Kogi tuni suna APC, haka kuma Niger da Plateau, yayin da Nasarawa da Benue ke cikin jam’iyyar. Ya ce wannan dunkulewa ta sa yankin ya zama tsintsiya madaurinki ɗaya a siyasance.
Ya kuma yaba wa gwamnan Jihar Plateau, Barrista Caleb Manasseh Muftwang, bisa matakin da ya ɗauka na shiga APC, yana mai cewa wannan zaɓi ne da zai amfanar da al’ummar jiharsa da yankin baki ɗaya.
Batun nasarar Tinubu/Shettima a 2027
A cewar Gwamna Sule, da haduwar da suka yi a APC, Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumar nasara a Arewa ta Tsakiya, ciki har da Jihar Plateau, idan aka gudanar da zaɓe.
Ya ce:
“A yau, duk inda ka je a Plateau, Kogi, Niger, Benue, Kwara da Nasarawa, APC ce ke da rinjaye.”
Leadership ta rahoto ya ce wannan ne ke nuna cewa tikitin Tinubu/Shettima ba shi da kishiya a yankin.
Gwamnan ya kara da cewa goyon bayan da APC ke samu a yankin ba wai kawai sakamakon siyasa ba ne, illa dai saboda amincewar jama’a da shugabancin Tinubu da tsare-tsarensa.

Source: Facebook
Dalilin shigowar ’yan siyasa APC
Gwamna Sule ya ce ’yan siyasa da dama na tururuwa zuwa APC ne saboda imanin da suke da shi ga tafiyar Tinubu/Shettima.
Ya jaddada cewa babu wata tafiya ko tikiti da ya taba doke APC tun bayan hawanta mulki, yana mai cewa hakan ya kara tabbatar da karfin jam’iyyar a fagen siyasar Najeriya.
A cewarsa, mutanen Arewa ta Tsakiya sun fahimci haka, kuma hakan ne ya sa suke sa ran ƙarin nasarori a shekarar 2027.
Zancen sauya Shettima a 2027
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya yi magana kan zancen sauya Kashim Shettima a 2027.
Yakubu Dogara ya amsa tambayoyi game da rade-radin cewa zai maye gurbin mataimakin shugaban kasa a APC a zabe mai zuwa.
Ya bayyana cewa ba ya so a saka shi a cikin zancen duk da ya ce ya kamata a tattauna batutuwan da suka shafi addini a siyasar Najeriya.
Asali: Legit.ng


