Gwamnoni, Kwamitin Gudanarwa Sun Zauna, An Tsayar da Lokacin Babban Taron APC
- Gwamnonin APC sun saka labule da kwamitin zartarwar jam'iyya inda aka cimma matsaya a kan a babban taro mai zuwa
- Gwamnonin sun yaba da yadda matasa suka shiga shirin rajistar ƴan jam'iyya da ake yi ta tsarin yanar gizo da ke hade NIN
- Sun jaddada buƙatar a tabbatar da gaskiya, haɗin kai da daidaito a dukkannin matakan jam’iyya don a kai ga ci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Kungiyar gwamnonin APC, wato 'Progressive Governors Forum' (PGF), ta gudanar da taro a daren Laraba da Kwamitin gudanarwar jam'iyyar na ƙasa (NWC).
Tattaunawar da aka yi a ƙarƙashin na Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Netanwe Yilwatda ta ɗauki sama da awanni huɗu kafin a kammala ta.

Kara karanta wannan
Bayan shigar Gwamna Abba APC, sakataren ADC ya ja kunnen jam'iyyar kan zaben 2027

Source: Facebook
The Nation ta ruwaito cewa Gwamnan jihar Imo kuma Shugaban PGF, Sanata Hope Uzodimma, ne ya karanta sanarwar bayan taro ga manema labarai.
Gwamnonin APC sun zauna a kan taron jam'iyya
TVC News ta wallafa cewa Hope Uzodinma ya bayyana cewa sun duba tare da amincewa da jadawalin da kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) ya amince da shi.
An Amin da da jadawalin da za a yi zaɓukan jam’iyya na matakan unguwa, ƙaramar hukuma, jiha, shiyya da kuma babban taron ƙasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnonin sun yaba wa Shugaban APC na ƙasa bisa ci gaban rajistar ƴan jam'iyya ta yanar gizo da sabunta bayanansu.
An nuna cewa shirin ya samu gagarumar nasara, musamman shigar matasa rajistar da kuma haɗa katin shaidar ɗan ƙasa ta NIN a tsarin.
Gwamnoni sun aminta da rajistar ƴan APC
Ƙungiyar gwamnonin ta ce wannan shiri zai taimaka wajen tsara tsare-tsare bisa bayanai da fahimtar alƙaluman jama’a tun daga ƙananan al’umma zuwa matakin jihohi.
Haka kuma, ta sake jaddada ƙudirinta na zurfafa dimokuraɗiyyar a cikin gida, gina tsayayyun ginshiƙan jam’iyya, da inganta sauye-sauyen da ke haɓaka gaskiya, riƙon amana da haɗa kowa da kowa a APC
Sanarwar ta nanata muhimmancin gudanar da kuɗi a cikin gaskiya da haɗin kai yayin tarukan jam’iyya da manyan taruka, domin tabbatar da adalci, daidaito da riƙon amana a duk jihohi—har da waɗanda ba APC ke mulki ba.

Source: Twitter
Haka kuma, ƙungiyar ta jaddada buƙatar haɗin kai da daidaito. cikin gida, tare da kiran shugabanni da su rika magana da bin ƙa’ida domin ƙarfafa amincewar jama’a ga tsarin dimokiraɗiyyar jam’iyyar.
Ƙungiya ta yi maraba da Gwamnonin Taraba da Filato, tare da sake tabbatar da kudirin gwamnoni na ci gaba na yin aiki tare da shugabancin APC don bunƙasa ƙasa, ƙarfafa dimokiraɗiyya, da mulki mai mayar da hankali ga jama’a.
Haka kuma an yaba wa Shugaban APC na ƙasa, sakatareda ƴan kwamitin zartarwa bisa kyakkyawar mu’amala, tare da tabbatar da shirin ci gaba da aiki kafada da kafada domin gudanar da taruka masu inganci.
An yi wa Abba magana da shiga APC
A wani labarin, kun ji cewa Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya yi martani kan sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.
Keyamo, wanda ke riƙe da muƙamin minista tun bayan zaɓen 2019, ya yaba wa Gwamna Abba bisa dawowarsa jam’iyyar APC mai mulki duk da dambarwar da aka sha fama da ita
A cewar Ministan, dawowar Gwamna Abba APC na da muhimmanci ga siyasar Kano da kuma haɗin gwiwar jihar da gwamnatin tarayya.m, wanda zai kara karfafa dimokiraɗiyya.
Asali: Legit.ng

