Ana Batun Sauya Shekar Abba, Za a Bayyana Asalin Wadanda Suka Ci Amanar Kano
- Dambarwar siyasar jihar Kano na neman canza salo biyo bayan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa jam'iyyar APC mai mulki
- Hadimin gwamnan Kano, Salisu Yahaya Hotoro ya ce nan ba da dadewa ba mutane za su gane asalin wadanda suka ci amanar kanawa
- Ya bayyana wasu badakaloli da suka faru a tsohuwar gwamnati a Kano, sai dai bai banbance gwamnatin wanda yake nufi ba tsakanin Kwankwaso da Ganduje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnatin Kano ta nuna alamun cewa nan ba da jimawa ba za ta fallasa asalin wadanda take zargi da cin amanar mutanen jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da zarge-zargen cin hanci da rashawa da rashin shugabanci na gari a karkashin tsohuwar gwamnati ke ci gaba da jan hankalin jama'a a Kano.

Source: Facebook
Babban mataimaki na musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafafen sada zumunta, Salisu Yahaya Hotoro, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a shafinsa na Facebook.
Ana shirin tona maciya amanar Kano
Hadimin gwamnan ya zargi wasu fitattun 'yan siyasa da gurgunta jin dadi da goben mazauna jihar Kano.
A cewarsa, gaskiyar da ke bayan wasu badakaloli masu cike da rudani za ta fito fili nan ba da jimawa ba, domin bai wa jama'a damar tantance wadanda ake zargi da cin amanar Kano da wadanda suka tsaya tsayin daka wajen kare jihar.
"Nan gaba kadan mutane zasu banbance su waye maciya amana tsakanin masu cin amanar Kanawa da kuma wayanda suka dage cewa ba za’a ci amanar Kanawa ba.
Hadimin Abba ya jero wasu badakaloli
Salisu Hotoro ya lissafa wasu batutuwa da ya ce sun faru a karkashin tsohuwar gwamnati (wadda ake kyautata zaton ta Kwankwaso yake nufi ko kuma ta Ganduje).
Daga cikin wadanda hadimin gwamnan ya ambata akwai badakalar Novemed, zargin rashin gaskiya a tsarin bayar da tallafin karatu na kasashen waje da harkar damfarar mutane da sunan sayar da filaye.
Sauran sun hada da zargin rashin gaskiya a kwangilolin gwamnati, musamman wajen sayo sinadarin Alum da sauran sinadaran tace ruwa, da badakalar sayo injinan ruwa da sauran makamanansu.

Source: Facebook
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dambarwar siyasar Kano ke kara zafi bayan Gwamna Abba ya raba gari da jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso a siyasance.
Tribune Nigeria ta rahoto cewa wannan lamari dai ya kara zafafa rikicin siyasar da ya barke a tafiyar Kwankwasiyya, indaagoya bayan Abba suka fara musayar yawu da mabiyan Kwankwaso.
Gwamna Abba ya yi sababbin nade-nade
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da sababbin nade-nade da karin mukamai bayan sauya shekarsa zuwa APC.
Wannan mataki na cikin kokarin gwamnatin jihar na sake fasalin hukumomi domin su yi aiki yadda ya dace wajen bauta wa al’ummar Kano.
Daga cikin wadanda aka nada akwai Hon. Abdulkadir Balarabe Kankarofi (Alhajiji), wanda aka nada a matsayin mai ba gwamna shawara ta musamman kan harkokin jin kai.
Asali: Legit.ng

