'Dalilin da Zai Sa Yankin Arewa Ya Yi Wa Tinubu Ruwan Kuri'u a Zaben 2027

'Dalilin da Zai Sa Yankin Arewa Ya Yi Wa Tinubu Ruwan Kuri'u a Zaben 2027

  • Tun kafin ya bayyana cewa zai yi takara a 2027, ana ci gaba da samu masu goyon bayan tazarcen Mai girma Bola Ahmed Tinubu
  • Kungiyar NYF ta yaba kan salon mulkin Shugaba Tinubu da yadda yake gudanar da jagorancin kasar nan
  • Hakazalika, kungiyar ta nuna cewa yankin Arewacin Najeriya zai ba da gagarumin goyon baya ga tazarcen Shugaba Tinubu a 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar Northern Youth Frontiers (NYF) ta yi magana kan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027.

Kungiyar ta bayyana cewa Arewa za ta mara wa Shugaba Tinubu baya domin ya sake samun wa’adi na biyu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Shugaba Tinubu ya samu goyon baya kan zaben 2027
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Rahoton jaridar The Nation ya ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban NYF, Sama Musa, ya fitar a madadin kungiyar a ranar Laraba, 28 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Lokuta 3 da aka ga Shugaba Tinubu ya yi tuntube ya fadi a wajen taro

Meyasa Arewa za ta zabi Tinubu?

Ƙungiyar ta danganta matsayar ta da sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ke aiwatarwa, jajircewarsa wajen tabbatar da haɗin kan ƙasa, da kuma bin ka’idar karba-karba a mulki da Najeriya ta amince da ita, jaridar The Guardian ta kawo rahoton.

Sama Musa ya ce Arewa ta tsaya tsayin daka wajen goyon bayan Shugaba Tinubu, inda ya bayyana gwamnatinsa a matsayin ginshiƙi na kwanciyar hankali, haɗa kai da shugabanci mai tafarkin ci gaba tun bayan dawowar mulkin dimokiraɗiyya a 1999.

Ya ce tsarin raba mulki da sauya shugabanci tsakanin shiyyoyi ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da adalci, wakilci da zaman lafiya a tsakanin yankuna daban-daban na kasar nan.

Tinubu ya samu yabo

"Tun daga fara tafiyar dimokiraɗiyyarmu a shekarar 1999, Najeriya ta samu gagarumin sauyi a tsarin siyasar ta."
"Tsarin karba-karba a mulki, wanda aka kafa domin samar da haɗa kai da wakilci ga ƙabilu da yankuna daban-daban, ya zama ginshiƙi a tsarin dimokiraɗiyyarmu."

Kara karanta wannan

Hadimin Shugaban kasa: Abin da ya kai Bola Tinubu Turkiyya daga dawo wa Najeriya

“Wannan tsari ba wai kawai ya samar da damar raba iko cikin adalci ba, har ma ya kasance garkuwa daga rikici da rarrabuwar kai a tsakanin sassan al’umma."
“Wa’adin mulkin Shugaba Tinubu ya nuna a sarari muhimmancin wannan tsarin na sauya mulki, tare da ƙarfafa amanna cewa ya kamata shugabanci ya dace da muradu da bukatun dukkan ’yan Najeriya, musamman na Arewa."
"Gwamnatinsa ta ƙaddamar da sauye-sauye da dama da ke da nufin magance matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da suka daɗe suna addabar yankinmu.”
"Daya daga cikin manyan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan shi ne sauya shekar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP zuwa APC."
"Wannan sauyi wata muhimmiyar alama ce da ke nuna yadda Arewa za ta kaɗa ƙuri’a a zaben shugaban ƙasa na 2027. Wannan mataki ya tabbatar da cewa Arewa za ta mara wa Bola Ahmed Tinubu baya."

- Sama Musa

Kungiyar NYF ta ce Arewa za ta zabi Tinubu a zaben 2027
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zaune a wurin taro Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Kungiyar NYF ta yi kira ga matasan Arewa da sauran masu ruwa da tsaki da su fara wayar da kan jama’a daga tushe domin tallafa wa sake zaɓen Shugaba Tinubu, tare da ƙarfafa shiga harkokin siyasa.

Kara karanta wannan

Tazarcen Shugaba Tinubu a 2027 ya samu gagarumin tagomashi daga Arewa

Dan Atiku ya goyi bayan tazarcen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Abubakar Atiku Abubakar wanda yake matsayin da ne ga tsohon mataimakin shugaban kasa, ya goyi bayan tazarcen Mai girma Bola Tinubu a 2027.

Abba Atiku ya bayyana cewa babu wata jam’iyyar siyasa ko haɗakar jam’iyyu da za su iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu komawa fadar Aso Rock.

Ya bayyana cewa yana ganin manufofin da Shugaba Tinubu ke jagoranta na da tasiri na hakika wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng