An Turo Sako daga Kasar Faransa kan Sauya Shekar Gwamna Abba zuwa APC a Kano
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na ci gaba da shan yabo daga ciki da wajen Najeirya ka ln sauya shekarsa daga NNPP zuwa APC
- Jam'iyyar APC reshen kasar Faransa ta bayyana cewa Gwamna Abba ya biyo hanyar da jihar Kano za ta samu karin ayyukan ci gaba
- Shugabar APC reshen Faransa, Hajiya Amina Suzuki ta ce 'yan Najeriya mazauna kasashen waje na bibiyar abubuwan da ke faruwa a gida
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Jam'iyyar APC reshen kasar Faransa ta yi maraba da sauya shekar gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tana mai kiran hakan da farar dabara.
Shugabar APC reshen kasar Faransa, Hajiya Amina Suzuki, ta yi hasashen cewa ficewar Gwamna Abba daga NNPP zuwa APC zai kai jihar Kano ga babban mataki na ci gaba.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa Hajia Amina ta fitar ranar Talata, inda ta yaba wa matakin gwamnan Kano ya dauka, kamar yadda The Nation ta ruwaoto.
APC ta Faransa ta yaba wa Gwamna Abba
Amina Suzuki ta bayyana matakin a matsayin wanda ya zo a kan gaba kuma na jarumta, tana mai cewa hakan zai amfani jihar Kano da ma Najeriya baki daya.
Ta kara da cewa sauya shekar Gwamma Abba zuwa APC ya nuna jajircewarsa ga shugabanci na gari, hadin kan kasa, da kuma tafiya kafada da kafada da Shugaba Bola Ahmed Tinubu don samar da ci gaba ga kowa.
Ta ce matakin zai kara karfafa jam’iyyar APC a Kano, sannan zai inganta hadin gwiwa tsakanin jihar da gwamnatin tarayya, musamman a fannonin ababen more rayuwa, tattalin arziki, tsaro, da ci gaban al'umma.
Ta jaddada cewa wannan mataki ya nuna cewa gwamnan yana da fahimtar yanayin siyasar Najeriya na yanzu, kuma hakan zai sa Kano ta ci moriyar shirye-shiryen gwamnatin tarayya.
Sakon 'yan APC mazauna Faransa ga Abba
Shugabar APC reshen Faransa ta tabbatar wa Gwamna Abba cikakken goyon bayan mambobin APC da ke kasashen waje musamman na kasar Faransa.
Hajiya Amina ta tabbatar da cewa 'yan Najeriya mazauna kasashen waje suna sanya ido sosai kan harkokin siyasar gida, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Ta ce shigowar gwamnan APC za ta hada kan masu ruwa da tsaki da magoya baya a fadin jihar Kano, wanda hakan zai tabbatar da dorewar zaman lafiya da mulki mai nagarta.

Source: Facebook
Amina Suzuki ta karkare da yaba wa shugabannin APC na jihar Kano kan yadda suka karbi gwamnan da hannu bibbiyu, tana mai yakinin cewa jam’iyyar za ta kara karfi da hadin kai gabanin zabuka masu zuwa.
Kwankwaso ya ce Abba zai yi nadama
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf da muƙarrabansa za su yi nadamar barin jam’iyyar NNPP.
Jagoran NNPP na kasa ya ce fitar gwamna Abba daga NNPP ta ba mutane da dama mamaki, har ma da shi kansa, inda ya ce yana jin abin kamar a mafarki.
Kwankwaso ya ce ganin yadda tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya karɓi Abba zuwa APC har ya ɗaga hannunsa, alama ce cewa gwamnan ya riga ya yi nisa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


