Kano: Abba Ya Yi Sababbin Nade Nade bayan Ya Koma APC
- Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da sababbin nade-nade da karin mukamai bayan sauya shekarsa zuwa APC
- Sanawar da Darekta janar kan yada, Sanusi Bature D-Tofa ya fitar ce ta tabbatar da karin nade-naden da Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Ya lissafa mutane bakwai da gwamnatin Kano ta daga likkafarsu, tare da bayyana dalilan da suka jawo aka yi sababbin nade-naden
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sababbin nade-nade da karin girma ga wasu manyan jami’ai a jihar.
Darekta janar a kan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature D-Tofa ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 28 ga watan Janairu, 2026.

Source: Facebook
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce wannan wani mataki ne da zai kara karfin shugabanci da inganta ayyukan gwamnati a muhimman bangarori.
Gwamna Abba ya yi nade-nade a jihar Kano
Sanarwar ta kara da cewa wannan mataki na cikin kokarin gwamnatin jihar na sake fasalin hukumomi domin su yi aiki yadda ya dace wajen bauta wa al’ummar Kano.
A cewarsa, gwamnan ya yi duba sosai kan kwarewa, gogewa da amana kafin yanke shawarar amincewa da nade-naden da karin mukaman.
Daga cikin wadanda aka nada akwai Hon. Abdulkadir Balarabe Kankarofi (Alhajiji), wanda aka nada a matsayin Mai Ba Gwamna Shawara ta Musamman kan Harkokin Jin Kai a Ofishin Babban Gwamna.
Kafin wannan matsayi, Alhajiji ya rike mukamin Babban Mataimaki na Musamman a gwamnatin Kano.
Mutanen da Gwamnan Kano ya nada a mukamai
Haka kuma, an nada Hajiya Aisha Tamburawa a matsayin mai ba Gwamna shawara a kan yada kyawawan ayyukan gwamnati.

Source: Facebook
A bangaren ruwa, Injiniya Mukhtar Yusuf ya samu karin girma zuwa Shugaban Hukumar WRECA, bayan da ya kasance Mataimakin Darakta Janar a baya.
An kuma nada Zakari Usman Balan a matsayin Mataimakin Shugaba na hukumar samar da ruwan sha ta Kano, WRECA.
Sauran nade-naden sun hada da na malami daga jami'ar Bayero, Dakta Mukhtar Bello Maisudan a matsayin Shugaban Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Kano.
Injiniya Abba Kankarofi ya samu karin girma zuwa Shugaban Hukumar Kula da Tituna da Gyare-gyare ta Kano (KARMA), daga mukamin Mataimakin Darakta Janar.
Musayyib Ungogo da Alhajiji sun tashi da mukamai
Bayan ya rasa samun takarar kujerar majalisar dokoki, Hon. Musayyib Kawu Ungoggo ya zama Shugaban hukumar adana namun dawa na jihar Kano.
Da farko an ce gwamna ya zabi Ungogo da Alhajiji Kankarofi a matsayin wadanda za su yi wa APC takarar kujerar majalisar dokoki a Ungogo da birnin Kano.

Kara karanta wannan
Kwamishinoni 2 sun yanke shawara, sun zabi wanda za su bi tsakanin Abba da Kwankwaso
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci dukkannin sabbin jami’an da aka nada da wadanda aka kara wa girma da su tabbatar sauke amanar da aka dora masu.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da karfafa hukumomi tare da aiwatar da shugabanci mai anfani ga jama’a.
Gwamnatin Abba ta shirya aiki a Kano
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kano ta bayyana kudirinta na kara zage damtse wajen samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce an tsara ayyukan ne bisa bukatun al’umma domin tabbatar da adalci da daidaito wajen rabon ci gaba.
Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarauta na jihar, Alhaji Mohammed Tajo Othman, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da bayanai kan manufofin gwamnati a karkara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

