‘Tun Farkon Mulki ne’: An Fadi Lokacin da Abba Ya Fara Bijirewa Kwankwaso a Kano
- Jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya yi tone-tone game da butulci da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ga Rabiu Musa Kwankwaso
- Buba Galadima ya nuna takaici game da lamarin inda ya ce tun bayan watanni uku kacal da hawansa mulki a Kano aka fara samun matsala
- Dattijon ya bayyana sauya shekar Abba a matsayin cin amana ga Kwankwasiyya, yana cewa ba don al’ummar jihar Kano ya koma APC ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Dattijo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana irin cin amana da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi wa Rabiu Musa Kwankwaso.
Injiniya Buba Galadima ya ce Abba ya rabu da jagoransa na siyasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, tun kafin ya sanar da sauya shekarsa zuwa APC.

Source: Facebook
Buba Galadima ya tona 'asirin' Abba Kabir
A cewarsa, gwamnan ya katse alaka da Kwankwaso ne tun bayan watanni uku kacal da hawansa kujerar gwamna, duk da cewa a bainar jama’a yana nuna masa girmamawa, cewar Vanguard.
Galadima ya ce matakin da Abba Kabir Yusuf ya dauka na hade kai da APC da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya zama wani tarihi na cin amana ga tafiyar siyasar da ta kai shi ga mulki.
Ya yi watsi da ikirarin cewa sauya shekar gwamnan an yi shi ne don amfanin al’ummar Kano, yana mai cewa muradun kansa kadai ne suka rinjaya
Ya ce:
“Watanni uku bayan ya hau mulki ya rabu da Kwankwaso, amma a fili yana nuna masa kamar Sarki ne shi, abin da ke faruwa a bayan fage ya sha bamban.
“Muradinsa ne kawai na kansa, na kansa, na kansa. Ba na mutanen Kano ba. Ba na zaman lafiya a Kano ba."

Source: Facebook
Abin da Buba Galadima ya tsammata daga Abba
Buba Galadima ya kara da cewa da a ce Abba Kabir Yusuf ya bar NNPP zuwa wata jam’iyya dabam ba APC ba, da za a iya cewa ya sauya sheka cikin mutunci.
Ya bayyana cewa matakin ya jefa shugabannin NNPP cikin radadi, yana tuna irin gagarumin kokarin da suka yi domin ganin Abba Kabir ya yi nasara a zabe, cewar The Sun.
“Da ace ya koma wata jam’iyya ban da APC, da zan ce ya sauya sheka lafiya, amma wannan ba komai ba ne illa neman tsira."
“Babu abin da ba mu yi ba domin Abba Kabir Yusuf ya yi nasara. Kwanaki uku ni da Kwankwaso ba mu yi barci ba. Mun yi tafiya, mun yi gwagwarmaya, mun sadaukar da komai,”
- In ji Buba Galadima
Kwankwaso ya soki wadanda suka bi Abba
Mun ba ku labarin cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana takaici kan sauya shekar Gwamna Abba Kabir da ya ce ya ba shi mamaki.
Kwankwaso ya ce duk wanda ya bi Abba zuwa APC, ko da jar hularsa, ba ya cikin Kwankwasiyya, ana kallonsa a matsayin 'dan Gandujiyya.
Jagoran Kwankwasiyya ya kalubalanci tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, yana cewa daga hannun Abba Kabir Yusuf alama ce ta faduwa a zabe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

