Siyasar Kano: Ganduje Ya Tura wa Kwankwaso Goron Gayyatar Sulhu
- Tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shirinsa na daidaitawa da Rabiu Musa Kwankwaso
- Tsohon shugaban APC, Dr. Abdullahi Ganduje ya ce siyasa ta tanadi sassauci, kuma a matsayinsu na Musulmi, babu wanda bai dace a nemi sulhu da shi ba
- Ya yi magana game da batun shugabancin APC a Kano da makomar Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda Ganduje ya nuna akwai yiwuwar goyon bayan tazarce
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Bayan komawar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC, tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sake buɗe ƙofar sulhu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Tsohon gwamnan da ake yi wa lakabi da Khadimul Islam ya nuna a shirye yake ya sasanta da tsohon mai gidansa lokacin da suna mulki a 1999 da 2011.

Source: Twitter
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Ganduje ya ce yana buɗe zuciya domin daidaita bambance-bambancen siyasa da Kwankwaso, duk da dogon sabanin da ya shiga tsakaninsu a baya.
Maganganun na Abdullahi Ganduje na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar Kano ke fuskantar sabon yanayi bayan sauya sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma sake tsara shugabanci a jam’iyyar APC a jihar.
Ganduje zai iya sulhu da Kwankwaso?
Da yake magana a hirar, Ganduje ya ce a matsayinsu na Musulmi, sulhu da fahimtar juna abu ne da ya dace a ko da yaushe.
Ya ce babu mutumin da za a ce ba a son a daidaita da shi gaba ɗaya, yana nuni da cewa siyasa hanya ce ta amfani da bambance-bambance domin cimma manufa.
A cewarsa, shi da Kwankwaso sun taɓa yin siyasa tare tun da dadewa, kuma dangantakarsu ba ta takaita ga siyasa kaɗai ba, domin suna kallon kansu a matsayin ‘yan uwa.
Ganduje ya ce:
'A matsayinmu na Musulmi, akwai mutumin da za ka ce baka son daidaitawa da shi ne?.
Harka ce fa ta siyasa. saboda haka, nan gaba muna fata za mu daidaita da shi a zo a tafi tare baki daya. Dama can ai mun yi siyasa tare kuma 'yan uwan juna ne."
Dangantakar Ganduje da Kwankwaso
Ganduje ya yi aiki a matsayin mataimakin gwamna a ƙarƙashin Kwankwaso, kafin daga bisani ya gaje shi a matsayin gwamnan Kano a 2015.
Sai dai dangantakarsu ta samu tsaiko bayan raba gari a siyasance, lamarin da ya haifar da gagarumin rarrabuwar kai tsakanin magoya bayansu a jihar.

Source: Facebook
Duk da wannan tarihi na sabani, Ganduje ya nuna cewa babu abin da zai hana sake samun fahimta, musamman idan hakan zai amfani Kano da siyasar Najeriya gaba ɗaya.
Bayanin Kwankwaso kan Abba Kabir
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi hira da 'yan jarida game da makomar siyasar Kano bayan sauya shekar Abba Kabir Yusuf.
Ya bayyana cewa matakin da Gwamnan Kano ya dauka ya zo masa da mamaki, wanda hakan ke sanya jama'a tunanin kamar baki suka hada.
Duk da haka, Kwankwaso ya tabbatar da cewa tsarin Kwankwasiyya zai cigaba da gudana a Kano kuma har yanzu 'yan jihar na tare da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


