Kwankwaso Ya Magantu kan Dalilan da Abba Ya Fada Masa yayin Shiga APC
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna takaicinsa kan yadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar NNPP ba tare da abin da ya kira wata hujja mai ƙarfi ba
- Jagoran NNPP ya ce dalilan da aka faɗa masa kan sauya sheƙar gwamnan abubuwa ne da a cewarsa za a iya gyarawa domin ci gaba da tafiya tare
- Kwankwaso ya kuma yi watsi da zargin rikicin cikin gida a NNPP, yana mai cewa jam’iyyar na cikin kwanciyar hankali fiye da yadda ake yaɗa jita-jita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana karon farko kan dalilan da ya ce suka sa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya juya masa baya.
Bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan sauya sheƙar gwamnan Kano da tasirinta ga siyasar jihar da kuma makomar jam’iyyar NNPP.

Source: Twitter
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Rabiu Kwankwaso ya bayyana takaici kan yadda gwamnan ya ɗauki abin da ya kira haƙƙin 'yan jam’iyyar NNPP da kuma jama’ar Kano, ya miƙa su ga tafiyar Gandujiyya ba tare da ƙwaƙƙwarar hujja ba.
Mene ne dalilin sauya shekar Abba Kabir?
Sanata Kwankwaso ya ce sau da dama yana yin tunani a kan abin da ya faru tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana tambayar kansa ko shi ne ya yi laifi ko jam’iyyar ce ko kuma 'yan jam’iyyar.
Ya ce duk da wannan nazari da yake yi, har yanzu bai samu amsar da za ta gamsar da shi ba, lamarin da ke ƙara nuna masa cewa sauya sheƙar gwamnan ta zo ne ba tare da dalili mai karfi ba.
Kwankwaso ya ce:
''Ni kaina in na kwanta sai in waiwaya in ce me ya faru? waye ya yi laifi? Ni ne na yi laifi? jam'iyya ce ta yi laifi? ƴan jam'iyya ne suka yi laifi? na kasa samun amsa.''
'Dalilan Abba ba su da karfi,' Kwankwaso
Jagoran NNPP ya bayyana cewa dukkan abubuwan da gwamna Abba ya faɗa masa kai tsaye, da kuma waɗanda aka turo aka faɗa masa a madadinsa, dangane da dalilan sauya sheƙa, ba su wuce matsalolin da za a iya gyarawa ba.
Kwankwaso ya ce a siyasance, irin waɗannan matsaloli na faruwa a kowace jam’iyya, kuma abu ne da ya kamata a zauna a tattauna domin samun mafita maimakon ficewa.
Sanata Kwankwaso ya yi watsi da hujjar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa ta cewa rikicin cikin gida a NNPP ne ya sa ya fice daga jam’iyyar.

Source: Facebook
Ya ce babu wata jam’iyya a duniya da ba ta da ƙorafe-ƙorafe, yana mai ƙara da cewa a iya saninsa, NNPP na ɗaya daga cikin jam’iyyun da suka fi samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Kwankwaso bai hada baki da Abba ba
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karyata cewa ya hada baki da Abba Kabir Yusuf wajen komawa APC.
A hirar da ya yi, Kwankwaso ya bayyana cewa kamar yadda jama'a ke mamaki shi ma haka ya ke ganin matakin da gwamnan ya dauka kamar mafarki.
Ya kara da cewa abin takaici ne yadda Abba Kabir ya dauki mulkin da suka sha wahalar kafawa ya mika a hannun Abdullahi Ganduje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


