Bayan Abba Ya Shiga APC, An Zakulo Gwamnoni 7 da Suka Rage a Jam'iyyun Adawa
- Jam'iyyar APC ta samu iko a jihohi 29 bayan sauya shekar Gwamna Abba Yusuf na Kano wanda hakan ya rage karfin jam'iyyun hamayya
- Ya zuwa ranar Laraba, 28 ga Janairun 2025, jam'iyyun adawa na da gwamnoni bakwai ne kacal, inda PDP ke da iko a jihohi hudu
- A wannan rahoto, Legit Hausa ta zakulo cikakken jerin gwamnoni 7 da suka rage a bangaren Adawa yayin da ake tuntakarar zabukan 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A ranar Laraba, 26 ga watan Janairu, 2026, wani babban sauyin sheka a fagen siyasar Najeriya ya rage yawan gwamnonin da ke jam’iyyun hamayya.
Wannan gagarumin sauyi ya biyo bayan ficewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki, wanda ya girgiza siyasar kasar.

Kara karanta wannan
Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC

Source: Twitter
Ficewar Abba Yusuf ta nuna yadda karfin iko ya karkata zuwa ga jam'iyyar APC, wadda yanzu take iko da mafi yawan jihohin kasar nan, in ji rahoton BBC.
A halin yanzu, jam'iyyar APC tana da gwamnoni 29 cikin jihohi 36, yayin da PDP da sauran jam'iyyun adawa ke da iko da ragowar jihohi bakwai.
Gwamnoni 4 da suka rage a PDP
A gefe guda, babbar tsohuwar jam'iyyar hamayya ta PDP tana fuskantar kalubale mafi girma a tarihinta, inda yanzu take da gwamnoni hudu kacal.
Jam'iyyar ta rasa jihohi kamar Akwa Ibom, Delta, Enugu, Bayelsa, Taraba, Rivers, da kuma Plateau sakamakon sauya shekar gwamnonin su.
Duk da wannan matsin lamba, Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa ya ci gaba da kasancewa daya daga cikin ginshikan jam'iyyar PDP, in ji rahotn Vanguard.
Fintiri ya sha musanta jita-jitar cewa zai koma APC, yana mai jaddada cewa shi "cikakken dan a-mutun" jam'iyyar PDP ne, don haka babu ranar barinta.
Haka ma a Jihar Bauchi, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ba zai taba mika wuya ga matsin lamba na shiga APC ba.
Ya zargi hukumar EFCC da kokarin jifarsa da lafuffuka domin kawai ya ki bin umarnin gwamnatin tarayya na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, in ji rahoton Punch.
Gwamna Bala ya bayyana cewa duk da kariya ta tsarin mulki da yake da ita, ana ambaton sunansa a takardun kararar da ake yi a kotu.
Makomar Makinde da Dauda Lawal
A Jihar Oyo, Gwamna Seyi Makinde, wanda ake ganin yana zawarcin takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP a 2027, ya gana da Shugaba Tinubu a Abuja.
Bayan wannan ganawa, Makinde ya bayyana cewa ya je ne domin tattauna al'amuran shugabanci, amma yana nan daram a cikin jam'iyyar sa ta PDP, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.
A Jihar Zamfara kuwa, Gwamna Dauda Lawal ya na kan fuskantar matsin lamba daga magabacinsa, Bello Matawalle, yayin da ake ganin shigar APC ce kawai samun saukinsa.
Sai dai Dauda Lawal ya musanta rahotannin cewa ya aika da wasikar neman zama mamba a APC, yana mai bayyana rahoton a matsayin karya bayan an ce Matawalle ya nemi ya shiga jam'iyyar.
Sauyin shekar Adeleke zuwa Accord
Wani babban abin mamaki a taswirar siyasar kasar shi ne matakin Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun na barin jam'iyyar PDP.
Legit Hausa ta rahoto cewa Adeleke ya bayyana cewa "rikicin shugabanci da ya ki ci ya ki cinye wa" a matakin kasa na PDP ne ya sa shi yin murabus a watan Nuwamba 2025.
Gwamna Adeleke ya koma jam'iyyar Accord, wanda hakan ya sa Jihar Osun ta zama jiha daya tilo karkashin wannan jam'iyya.
Wannan mataki ya nuna yadda rikicin cikin gida yake ci gaba da ruguza karfin jam'iyyar PDP yayin da aka tunkari babban zaben 2027.

Source: Instagram
Sauran jam’iyyun hamayya: APGA da LP
A Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ya ci gaba da rike tutar jam'iyyar APGA bayan nasarar samun tazarce a zaben Nuwamba 2025.
Soludo ya kasance mamban APGA tun 2013 bayan ya bar PDP, kuma jihar Anambra ta kasance tungar jam'iyyar APGA tsawon shekaru 20.
A Jihar Abia, Gwamna Alex Otti ne kadai gwamnan jam'iyyar LP a fadin Najeriya baki daya, kamar yadda rahoton Premium Times ya nuna.
Alex Otti ya yi ta sauya sheka tsakanin APGA da APC kafin daga bisani ya samu nasara a karkashin jam'iyyar LP a zaben shekarar 2023.
Abin da ke tunkarar 'yan adawa a 2027
Wannan lamari na sauya shekar gwamnoni daga jam'iyyun adawa zuwa APC ya nuna cewa jam'iyyar ta mamaye kusan kashi 83 cikin dari na jihohin kasar.
Hakan yana nufin cewa idan har jam'iyyun hamayya suna son kalubalantar APC a 2027, dole ne su nemo sabuwar dabarar hadaka ko kuma samar da gagarumin kawance.
A yanzu dai, idanun yan Najeriya suna kan sauran gwamnoni hudu na PDP domin ganin ko za su iya jure matsin lamba, ko kuma za su mika wuya suma su sauya sheka.
Siyasar 2027 ta fara zafi tun yanzu, inda kowane bangare yake kokarin karfafa nasa sansanin domin tunkarar babban kalubalen zaben kasa dake gabatowa.
Gwamna Abba ya shiga jam'iyyar APC
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC a hukumance, bayan raba gari da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ne suka karbi Gwamna Abba ranar 26 ga Janairu, 2026.
Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan Gwamna Abba ya mika takardar ficewa daga jam'iyyar NNPP a mazabarsa da ke karamar hukumar Gwale a Kano.
Asali: Legit.ng



