'Waye Ya Ce Ka Yi': Gwamna Fintiri Ya Hasala da Aka Yi Masa Ihun 'Ba Ma Yi'

'Waye Ya Ce Ka Yi': Gwamna Fintiri Ya Hasala da Aka Yi Masa Ihun 'Ba Ma Yi'

  • Wasu matasa sun fusata Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a Ganye, Adamawa, yayin taron neman goyon bayan PDP, lamarin da ya jawo maganganu
  • A cikin bidiyon, an ji matasa suna ihu “ba ma yi” yayin jawabin gwamnan, abin da ya sa Fintiri ya dakata ya mayar da martani cikin fushi
  • Gwamna Fintiri ya kalubalanci masu adawa da shi kan zabe, yana mai cewa su tsayar da dan takara, shi ma ya tsayar, a ga wanda zai ci zabe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ganye, Adamawa - Wasu matasa a jihar Adamawa sun fusata Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yayin taro a Ganye.

Lamarin ya fusata Gwamna Fintiri har ya mayar da martani cikin fushi wanda ya dauki hankulan mutane da ke wurin.

Matasa sun fusata Gwamna Fintiri a taro
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa. Hoto: @GovernorAUF.
Source: Twitter

Matasa sun yi wa Gwamna Fintiri ihu

Kara karanta wannan

'Abin da na fada wa Abba Kabir game da butulce wa Kwankwaso - Sanatan NNPP'

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar ya wallafa a shafin X a yau Talata 27 ga watan Janairun 2026.

An ce lamarin ya faru ne yayin da gwamnan ya kai ziyara a Ganye da ke jihar inda ya bukaci goyon bayan PDP.

A cikin bidiyon, an ji wasu matasa a gefe suna ta ihu da cewa 'ba ma yi' yayin da gwamnan ke jawabi a taron.

Ihun da suke yi ya yi yawa wanda har ya dauki hankalin gwamnan da ya tilasta shi mayar da martani.

Gwamna Fintiri cikin fushi ya soki mai ihun da cewa waye ya ce ya yi daman kuma babu wanda ya ce dole sai ya yi.

A cewarsa:

"Waye ne baka yi, wa ya tambaye ka ka yi? Wa ya ce maka ka yi? Kai ma ba a yinka.
"Babu wanda ya ce yana sonka, iskanci kuma ba gado ba ne, kowa zai saka hular kuma ya nuna maka kai ba komai ba ne.
"Saboda haka ba za mu bari a wulakanta shugabanni ba, ba ka yi, ba ka yi, wa ya ce ka yi, ka zuba mu zuba a ga wanda zai ci zabe kuma sako na ba gare ka ba ne, ga wanda ya haife ka ne."

Kara karanta wannan

Tsagin Kwankwaso a NNPP ya yi martani mai zafi kan ficewar Gwamna Abba daga jam'iyya

Gwamna Fintiri ya caccaki matasa da suka yi masa ihu a taro
Taswirar jihar Adamawa da jam'iyyar PDP ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Gwamna Fintiri ya sha alwashi kan zabe

Gwamna Fintiri ya bugi kirji game da zabe inda ya ce su tsayar da dan takara shi ma ya tsayar a ga wanda zai lashe zabe.

Daga bisani, ya bukaci mai kula da kayan sauti ya saka masu waka domin taka rawa da shashewa.

"Ya tsayar mu tsayar a ga wanda zai ci zabe, kai DJ saka mana waka mu yi rawa."

- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri

Fintiri ya saka doka bayan barkewar rikici

A baya, kun ji cewa an samu barkewar rikicin kabilanci a jihar Adamawa da yammacin ranar Lahadi 7 ga watan Disambar 2025.

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi gaggawar daukar mataki ta hanyar sanya dokar ta baci ta tsawon awa 24.

Hakazalika, Gwamna Fintiri ya umurci jami'an tsaro da su gaggauta zuwa yankin da lamarin ya auku domin dawo da doka da oda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.