'Barazanar da Abba Kabir Zai Fuskanta daga Kwankwaso a 2027 bayan Bijire Masa'

'Barazanar da Abba Kabir Zai Fuskanta daga Kwankwaso a 2027 bayan Bijire Masa'

  • Fasto Elijah Ayodele ya tsoma baki game da ficewar Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zuwa APC mai mulkin Najeriya
  • Limamin ya gargadi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, cewa burinsa na wa’adi na biyu na fuskantar barazana mai tsanani
  • Ayodele ya yi hasashen rikicin siyasa a Kano, tare da gargadin Tinubu kada ya yarda da duk masu sauya sheka zuwa APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Fasto Elijiah Ayodele ya yi hasashen siyasar Kano a 2027.

Fasto Elijiah Ayodele ya gargadi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kan burinsa na neman wa’adi na biyu a 2027.

An gargadi Abba Kabir game da shirin Kwankwaso a 2027
Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf.
Source: Twitter

An gargadi Abba Kabir game da Kwankwaso

Haka na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, ya sanya wa hannu da Tribune ta samu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar da Kwankwaso ya yi fata Abba ya shiga maimakon hadewa da Ganduje a APC

Ayodele ya ce Rabiu Kwankwaso zai yi duk mai yiwuwa domin ganin bayan gwamnan a zaben 2027 da ke tafe.

Fasto Ayodele ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kano ba zai lamunci Yusuf ya koma kan karagar mulki ba a karo na biyu.

Wannan gargadi na zuwa ne bayan sauya shekar Gwamna Yusuf daga NNPP zuwa jam’iyyar APC, lamarin da ya janyo sabani tsakaninsa da Kwankwaso.

Ayodele ya ce sauya shekar Yusuf zuwa APC za ta haddasa rikicin siyasa mai tsanani idan ba a kula da lamarin da hikima ba.

Ya ce:

“Wa’adi na biyu na Gwamna Abba Yusuf na cikin matsala sosai. Sauya shekar sa zuwa APC za ta kawo masa rudani da matsala.”
Gargadin da aka yi wa Abba Kabir bayan barin Kwankwaso
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Ayodele ya kara da cewa Kwankwaso zai yi amfani da duk wata hanya ta kudi, siyasa, shari’a domin ba shi matsala a zaben.

Ya ce tsohon gwamnan zai tsaya tsayin daka domin ganin an dakile burin Abba Kabir na neman wa’adi na biyu a Kano.

A cewarsa:

“Gwamnan ya shirya fuskantar matsala mafi muni, domin za a yi komai don hana shi dawowa mulki.”

Kara karanta wannan

Komawa APC: Ministan Tinubu ya fadi abin da tarihi zai rika tuna Abba da shi kan barin Kwankwaso

Hasashe game da rigimar siyasa a Kano

Fasto Ayodele ya kuma yi hasashen cewa za a shiga wani yanayi na rikici da tashin hankali a siyasar Kano.

Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya ido sosai kan jihar, yana mai gargadin cewa abubuwa na iya rikidewa idan ba a dauki mataki ba.

Bugu da kari, Ayodele ya yi gargadi ga Shugaba Bola Tinubu kan masu sauya sheka zuwa APC.

Ya ce ba duka masu komawa APC ke da niyyar taimaka wa Tinubu ba a zaben 2027 inda ya ce daga wasu cikinsu suna da manufar haddasa rikici da durkusar da jam’iyyar APC daga ciki.

NNPP ta soki Abba Kabir a Kano

Kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta yi magana kan abin da zai faru a zaben 2027 duk da ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC.

Jam’iyyar ta zargi Gwamnan da cin amanar Rabiu Musa Kwankwaso, tana cewa Jagora ne ya gina shi har ya kai matsayin da yake.

NNPP mai adawa a Najeriya ta jaddada cewa duk wanda Kwankwaso ya tsayar a Kano a 2027 zai yi nasara ba tare da wahala ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.