Bayan Shigan Abba APC, NNPP Ta Yi Maganar Butulci, Shirin Kifar da Shi a 2027

Bayan Shigan Abba APC, NNPP Ta Yi Maganar Butulci, Shirin Kifar da Shi a 2027

  • Jam'iyyar NNPP ta yi magana kan abin da zai faru a zaben 2027 duk da ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC
  • Jam’iyyar ta zargi Gwamnan da cin amanar Rabiu Musa Kwankwaso, tana cewa Jagora ne ya gina shi har ya kai matsayin da yake
  • NNPP mai adawa a Najeriya ta jaddada cewa duk wanda Kwankwaso ya tsayar a Kano a 2027 zai yi nasara ba tare da wahala ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Jam’iyyar NNPP a Jihar Plateau ta bayyana damuwa game da cin amanar Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir ya yi.

Jam'iyyar ta bayyana cewa sauya shekar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa APC ba zai lalata martabar NNPP ko kuma damar ta na samun nasara a zaben 2027 ba.

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC

NNPP ta caccaki Abba Kabir kan cin amanar Kwankwaso
Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwasiyya da Gwamna Abba Kabir. Hoto: Rabiu Musa Kwankwasiyya da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Source: Twitter

NNPP ta yi mamakin komawar Abba APC

Shugaban NNPP a Plateau, Kwamared Tokji Nadem, ya shaida wa Nigerian Tribune cewa ficewar gwamnan ta ba su mamaki.

Ya ce abin mamaki ne duba da rawar da ya taka tun kafuwar jam’iyyar da kuma kusancinsa da jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwamared Nadem ya bayyana ficewar a matsayin cin amana, yana cewa hujjojin da aka bayar ba su isa su tabbatar da barin jam’iyyar ba, musamman ganin irin tagomashin da NNPP ta yi wa Gwamna Yusuf har ya kai matsayin da yake kai a yau.

Ya ce:

“Matsayinmu shi ne gwamnan ya ci amanar jam’iyya da kuma jagoranmu, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso. Idan ka haifi yaro ka raine shi daga babu zuwa wani matsayi, daga baya sai ya guje ka gaba daya, me za ka kira hakan? Cin amana ne tsantsa.”
NNPP ta bugi kirji duk da ficewar Abba zuwa APC
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa.
Source: Facebook

'Musabbabin shaharar Abba a siyasa'

Shugaban NNPP a Plateau ya ce kafin zuwan Kwankwaso, sunan Abba Yusuf ba ya da karfi a siyasar Kano, yana mai cewa Kwankwaso ne ya bude masa hanya har ya zama gwamna.

Kara karanta wannan

Zance ya fito, an ji matakin da za a dauka kan mataimakin gwamnan Kano idan ya ki komawa APC

A cewarsa, Kwankwaso ya hana wasu dama domin ya ba Abba Yusuf damar tsayawa takara, amma martanin da ya samu daga baya ya kasance abin takaici.

“Ina so in tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ficewarsa ba ta canza komai ba. Kwankwaso dan siyasar kasa ne, jama’a har yanzu suna tare da shi duk da sauya shekar gwamnan."

- In ji Nadem.

Ya kara da cewa wasu ‘yan siyasa sun manta cewa siyasa tana bukatar biyayya da hakuri, ba cika burin kai kadai ba.

Shugaban ya nuna kwarin gwiwa cewa NNPP za ta sake lashe Jihar Kano a 2027, yana mai cewa duk wanda Kwankwaso ya tsayar takara ba shakka zai yi nasara.

Nadem ya bayyana sauya shekar Gwamna Yusuf a matsayin abin Allah-wadai, musamman ganin cewa sun shafe fiye da shekaru 40 suna tare da Kwankwaso.

Minista ya yi maraba da Abba zuwa APC

Mun ba ku labarin cewa Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya yi tsokaci kan matakin Gwamna Abba Kabir Yusuf na komawa APC.

Festus Keyamo ya yaba wa Gwamna Abba kan dawo wa APC, inda ya ce dawowarsa ta nuna kamar bai taba barin jam'iyyar ba .

Ministan ya kuma bayyana yadda tarihi zai rika kallon Gwamna Abba kan rabuwa da NNPP wadda ubangidansa, Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.