Ganduje Ya Goyi bayan Abba Ya Yi wa APC Takarar Gwamnan Kano a 2027
- Tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf na kan hanyar samun wa’adi na biyu a 2027
- Tsohon shugaban APC ya yaba da matakin gwamnan na sauya sheƙa zuwa APC yayin da ya tabbatar da mara masa baya a mulkinsa
- Wannan na zuwa ne a lokacin da APC ta karbi Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu daga cikin mukarraban gwamnatin jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana ra’ayinsa kan makomar siyasar Kano.
Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na kan turba mai kyau ta samun wa’adi na biyu a zaɓen shekarar 2027.

Source: UGC
BBC Hausa ta wallafa cewa Ganduje ya bayyana hakan ne kwanaki kadan bayan Gwamnan ya sauya sheka zuwa APC.
Abdullahi Ganduje ya yi maraba da Gwamna Abba
Tsohon Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya nuna farin cikinsa kan matakin da gwamnan Kano ya ɗauka na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
A cewarsa, wannan mataki ba ƙaramin tasiri zai yi ba ga daidaituwar siyasa a jihar da ma yankin Arewa gaba ɗaya.
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa shigowar Abba Kabir Yusuf cikin APC zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi, tare da buɗe sabon babi na haɗin kai tsakanin manyan jagorori.
Ganduje ya ce idan aka ci gaba da wannan tafiya ta fahimtar juna, APC za ta samu gagarumar nasara a zaɓuka masu zuwa.
Yadda Abba ya girgiza siyasar Kano
A ranar Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kammala sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC a hukumance.
Lamarin ya kawo ƙarshen watanni na raɗe-raɗin siyasa da hasashe kan inda makomarsa ta dosa.

Source: Twitter
An gudanar da bikin sauya sheƙar ne a gidan gwamnatin jihar Kano, cikin wani karamin biki da ya samu halartar manyan ’yan siyasa, shugabannin jam’iyyar APC, da magoya baya.
Bayan ya sauya sheka, wasu daga cikin 'yan Kwankwasiyya sun ruka ajiye mukamansu a gwamantin Kano tare da jaddada mubaya'a ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Lamarin ya kara dumama siyasar jihar Kano da ta kwana biyu tana daukar zafi saboda zargin Gwamna Abba Kabir Yusuf da cin amanar NNPP.
Abba ya sa hoton Ganduje a gidan gwamnati
A baya, kun ji cewa sauyin siyasa ya bayyana a fadar gwamnatin jihar Kano, bayan da aka ga hotunan Abdullahi Umar Ganduje, tare da wasu fitattun jiga-jigan APC a dakin taron gidan.
Rahotanni sun nuna cewa wannan sauyi ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin ayyana komawar gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.
A yayin da aka saka hotunan manyan jagororin APC, ba a hango hotunan jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ko sauran manyan kusoshin jam’iyyar ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

