Jam'iyyar da Kwankwaso Ya Yi Fata Abba Ya Shiga maimakon Hadewa da Ganduje a APC
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana damuwa kan ficewar Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC, yana kiran lamarin da rashin adalci
- Kwankwaso ya nuna cewa bai dace Abba Kabir ya mika nasarar da suka samu tare a Kano ba wajen mutanen da ya kira makiyasu a siyasa
- Ya kara da cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim, ya nuna bakin ciki kan sauya shekar, yana tuno rawar da ya taka a baya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan sauya shekar Abba Kabir Yusuf, daga NNPP zuwa jam’iyyar APC, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin da ya ba shi mamaki da kuma cike da rashin adalci.
Kwankwaso, wanda shi ne jagoran NNPP na kasa, ya tuno yadda ya tallata Abba Kabir Yusuf a siyasa, musamman a zaben 2023 da suka samu nasarar lashe kujerar gwamnan Kano bayan shan kaye a 2019 a hannun Abdullahi Ganduje.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Rabiu Kwankwaso ya yi ne a wani bidiyo da hadiminsa, Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Bayanin da Rabiu Kwankwaso ya yi
Yayin martaninsa, Rabiu Kwankwaso ya ce yana jin zafi da bakin ciki kan yadda lamarin ya kasance, yana mai cewa ba zai iya tuna irin wannan lamari a rayuwarsa ta siyasa ba.
A cewarsa:
“Rashin adalci, tun da nake a rayuwata ta, zan dade ban iya tuna inda aka taba yin irin haka ba.”
Ya kara da cewa da ya fi dacewa Abba Kabir Yusuf ya koma wata sabuwar jam’iyya kamar ADC, maimakon kai nasarar da suka samu tare zuwa wajen mutanen da ya kira makiya.
Kwankwaso ya bukaci jama’a su duba gwagwarmayar da suka sha a zaben 2019, zaben da bai kammalu ba (inconclusive), da kuma yadda suka sha wahala a kotuna kafin daga bisani su samu nasara a 2023.
Pius Anyim ya koka da halin Abba Kabir
Kwankwaso ya bayyana cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim, ya kira shi domin jin gaskiyar abin da ya faru a Kano, yana tambaya ko labarin sauya shekar Abba Kabir Yusuf gaskiya ne.
A cewar Kwankwaso, ya tabbatar wa Anyim cewa lamarin ya faru, abin da ya sa tsohon shugaban majalisar dattawan ya nuna matukar damuwa.
Kwankwaso ya ce Anyim ya tuna yadda a 2019 ya rika daukar Abba Kabir Yusuf zuwa wuraren manyan ’yan Najeriya a jihohi daban-daban domin neman goyon baya.

Source: Getty Images
Ya ce har sun kai ziyara Ebonyi, inda suka kwana a gidan Anyim, lamarin da ya kara masa mamaki ganin abin da ake cewa Abba Kabir Yusuf ya yi yanzu.
Kwankwaso ya kara da cewa Anyim Pius Anyim ya shaida masa cewa tun da aka fada masa labarin, ya gagara cin abinci saboda bakin ciki, yana mai cewa da ya so da ba su taba zuwa wajensa domin neman goyon bayan Abba Kabir Yusuf ba.
Barau ya yaba wa Abba Kabir Yusuf
A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya taya Abba Kabir murnar shiga jam'iyyar APC.
Barau ya tabbatar da cewa ya sauya sunan kungiyarsa da ke tallata manufofinsa da shugaba Bola Tinubu domin saka Abba a ciki.
Baya ga haka, Barau ya yi kira ga dukkan magoya bayansa da su nuna goyon baya ga Abba Kabir domin ya samu nasara a jihar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


