Abba da Kwankwaso: Shugaban Malaman Kano Ya Yi Maganar da Ta Ja Hankali
- Shugaban majalisar malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya furta kalmar “a ci daɗi lafiya” a wani karatu da ya gabatar, abin da ya jawo hankalin jama’a
- Maganar ta zo ne a daidai lokacin da rade-radin siyasar Kano ke kara zafi bayan sauya shekar Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC mai mulkin kasa
- Martanin jama’a ya bambanta, inda wasu suka dauki maganar a matsayin barkwanci, wasu kuma suka danganta ta da halin da siyasar jihar Kano ke ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Shugaban majalisar malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya yi wata magana da ta dauki hankalin jama’a yayin da yake gabatar da wani karatu, inda ya furta kalmar “a ci daɗi lafiya” a gaban masu sauraro.
Kalmar ta yi fice ne musamman ganin yadda ake yawan furta ta a kwanakin nan, tun bayan da aka fara rade-radin sauya shekar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da shugaban malaman ya yi ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook bayan Abba ya sauya sheka zuwa APC.
Sheikh Ibrahim Khalil: 'A ci daɗi lafiya'
Yayin da Sheikh Ibrahim Khalil ke gabatar da karatun, an ji shi yana furta kalmar “a ci daɗi lafiya”, kalma da ta riga ta zama ruwan dare a tsakanin jama’a a wannan lokaci na sauye-sauyen siyasa.
Bayan ya fadi kalmar, shi da masu sauraron karatun sun fashe da dariya, lamarin da ya nuna cewa an dauki maganar cikin yanayin barkwanci da nishadi.
Wasu daga cikin masu sauraro sun yi masa magana kai tsaye, abin da ya sa ya kara da cewa:
“Ah to, ba shikenan ba, ai Ibrahim Khalil din kenan ai dama.”
Wannan bayani daga bakin malamin ya kara jawo hankalin jama’a, inda aka fara fassara maganar ta hanyoyi daban-daban, musamman a yanayin siyasar Kano da ke cike da jita-jita da rade-radi.

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu
Magana kan yanayin siyasar Kano
Tun bayan da aka fara rade-radin sauya shekar Abba Kabir Yusuf zuwa APC daga NNPP, kalmar “a ci daɗi lafiya” ta zama abin furtawa ga duk wanda ake ganin zai bi gwamnan ko ya nuna alamar mara masa baya.

Source: Facebook
Sauya shekar Abba Kabir Yusuf ta dauki hankali ne ganin yadda ya shafe shekaru da dama tare da Rabiu Kwankwaso a siyasa da sauran al’amuran rayuwa, lamarin da ya sa wasu ke kallon matakin a matsayin babban sauyi a siyasar Kano.
Martanin jama’a kan cewa a ci dadi lafiya
Maganar Sheikh Khalil ta haifar da martani iri-iri. Umar Ali Ilu ya ce yana fatan Kwankwaso zai yaba da amincin malamin a 2027, yana mai bayyana kwarin gwiwa cewa malamin ba zai yi butulci ba.
Aminu Ibrahim Magaji ya bayyana cewa ko da ba a fada ba, su dai za su “ci daɗi lafiya”, yayin da Abdussamad Yaaqoub Mahmud ya nuna mamaki, yana cewa malamin ya sanya shi dariya.
Abdullahi Ibrahim Muhd kuma ya ce suna fatan Sheikh Ibrahim Khalil zai fito a matsayin dan takarar Kwankwaso nan gaba, yana mai nuna yadda kalmar da maganar malamin suka kara daukar hankalin al’umma a siyasar Kano.
Abba ya fitar da 'yan takarar APC
A wani labarin, mun kawo muku cewa Abba Kabir Yusuf ya fitar da 'yan takarar APC da za su tsaya a zaben cike gurbi da za a yi a Kano.
Za a yi zaben cike gibi a Kano ne bayan rasuwar wasu 'yan majalisar dokokin jihar Kano a watan Disamban shekarar 2025 da ta wuce.
Tun bayan rasuwar 'yan majalisar, jam'iyyar NNPP karkashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso ta fitar da 'yan takararta domin zaben.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

