An Ga Katin Zama 'Dan APC na Bello Turji, Jam'iyya Ta Yi Magana

An Ga Katin Zama 'Dan APC na Bello Turji, Jam'iyya Ta Yi Magana

  • Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta ce an gano katin shiga cikinta na bogi da aka danganta wa babban ’dan bindiga a Najeriya, Bello Turji
  • Jam’iyyar ta ce an kirkiri katin ne domin bata mata suna da kawo rudani yayin rajistar yanar gizo da ke gudana a jihar da ma duk Najeriya
  • APC ta jaddada cewa babu wata rajista da aka yi da sunan Bello Turji, tana mai cewa lambobin katin sun sabawa ka’idar da ta gindaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara – Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta musanta rade-radin da ke yawo cewa jagoran ’yan bindiga, Bello Turji, memba ne na jam’iyyar, tana mai cewa katin dan ta'addan da ake nunawa a kafafen sada zumunta na bogi ne.

Kara karanta wannan

Abba da Kwankwaso: Shugaban malaman Kano ya yi maganar da ta ja hankali

Jam’iyyar ta bayyana cewa hada katin bogin wani yunkuri ne na bata mata suna da karkatar da hankalin jama’a daga yadda ake gudanar da rajistar sababbin mambobi ta hanyar yanar gizo.

Katin Bogi da aka yi wa Bello Turji
Bello Turjia hagu, da katin bogi da aka yi da sunan shi a dama. Hoto: Murtala Muhammad Sabo|Zagazola Makama
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa Mai magana da yawun APC a Zamfara, Yusuf Idris, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, inda ya ce jam’iyyar ba ta da wata alaka da katin da ake dangantawa da Bello Turji.

Katin APC na Bello Turji na bogi ne

Yusuf Idris ya ce jam’iyyar ta ci karo da wani katin APC da aka kirkira, wanda ke dauke da suna da hoton Bello Turji, lamarin da ke nuna kamar shi memba ne na jam’iyyar.

Rahoton TVC ya nuna cewa ya ce aikin wasu mutane ne masu mummunar manufa da ba sa jin dadin yadda rajistar mambobi ke tafiya cikin nasara a Zamfara.

Ya kara da cewa ko gama-gari zai iya gane cewa katin bogi ne, duba da kura-kuran da ke cikinsa. A cewarsa, an rubuta lambar kwanan wata da babban “26” da ake dangantawa da 26 ga Janairu, wanda bai dace ba.

Kara karanta wannan

Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

Idris ya kuma nuna cewa hoton da aka saka a katin Bello Turji hoto ne da aka riga aka sani, wanda jami’an tsaro da ’yan Najeriya da dama ke gane shi. Ya ce hakan kadai ya isa ya nuna cewa katin kirkirarre ne.

Karin bayani daga jam'iyyar APC

Jam’iyyar APC ta Zamfara ta ce babu wanda za a iya yi wa rajista a jam’iyyar ba tare NIN ba. Idris ya ce Bello Turji ba shi da NIN, wanda hakan ke kara nuna cewa duk wani katin da ake dangantawa da shi na bogi ne.

Ya kara da cewa kafin Hukumar NIMC ta yi wa mutum rijista, dole sai an dauki cikakken bayanansa, kuma ba za a taba daukar hoton wanda ke sanye da kayan soja dauke da bindiga ba.

Idris ya kuma bayyana cewa bayanan rajistar da ake yi a gundumar Kware sun nuna cewa babu wata lambar shaida da ta fara da “26”, wadda aka ware wa jihar Neja, ba Zamfara ba. Ya ce rajistar APC a Zamfara na farawa ne da lambar “36”.

Nentawe Yilwatda da wasu 'yan APC
Shugaban APC, Nentawe Yilwatda na yi wa 'yan jam'iyyar bayani. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

A cewar mai magana da yawun jam’iyyar, binciken farko-farko ya alakanta kirkirar katin da Babangida Aliyu Shinkafi, wanda ake kira Waziri, abokin Sani Abdullahi Shinkafi, wanda aka dakatar daga shiga rajistar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Juyin mulki a Najeriya: Ana zargin sojojin da aka kama na cikin mawuyacin hali

Abba ya fitar da 'yan takarar APC

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zabi mutane biyu da za su tsaya wa jam'iyyar APC a zaben cike gurbin 'yan majalisar Kano.

Hakan na zuwa ne bayan Abba Kabir ya koma APC, inda ya samu tarba daga tsohon shugaban jam'iyyar, Abdullahi Umar Ganduje.

A kwanakin baya, jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ayyana mutane biyu da za su maye gurbin 'yan majalisar da suka rasu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng