Sai Tinubu: 'Dan Atiku Ya Sha Alwashi, Za a Hadu da Shi a Kada Mahaifinsa a 2027

Sai Tinubu: 'Dan Atiku Ya Sha Alwashi, Za a Hadu da Shi a Kada Mahaifinsa a 2027

  • 'Dan tsohon mataimakin Shugaban kasa, Abba Atiku ya jaddada cewa babu jam’iyyar siyasa da za ta kayar da Bola Tinubu a 2027
  • Yana wadannan kalamai ne duk da mahaifinsa, Alhaji Atiku Abubakar ke kokarin tattara kawunan 'yan adawa a kifar da Tinubu a filin zabe
  • Abba Atiku Abubakar ya yi kira ga ‘yan Najeriya su mara wa shugaban ƙasa baya ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa – Abba Atiku, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa babu wata jam’iyyar siyasa ko haɗakar jam’iyyu da za su iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu komawa fadar Aso Rock.

Abba, wanda ya shiga jam’iyyar APC a kwanan nan, ya yi wannan furuci ne a Yola, babban birnin jihar Adamawa, bayan ya karɓi katin rajistar zama 'dan mazabar Gwadabawa da ke karamar hukumar Yola ta Arewa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya dura Najeriya, zai je taro Gwamna Abba zuwa APC a Kano

Abba Atiku Abubakar ya yanki tikitin zama cikakken dan APC
Abba Atiku Abubakar (tsakiya) tare da abokan siyasarsa a wajen karban katin zama dan APC Hoto: Basiru Yusuf Shuwaki
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa a cewarsa, shawarar sauya shekar da ya yi zuwa APC ta samo asali ne daga burinsa na bayar da gudummawa mai ma’ana ga sauye-sauyen tattalin arziki da na bunƙasa ɗan Adam.

'Dan Atiku ya yabi manufofin Bola Tinubu

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Abba Atiku Abubakar ya ce yana ganin manufofin da Shugaba Tinubu ke jagoranta na da tasiri na hakika wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Abba ya jaddada cewa Shugaba Tinubu na tafiyar da mulki bisa adalci da cancanta, ba tare da nuna bambancin kabila, addini ko yanki ba.

Abba Atiku ya jaddada goyon baya ga Bola Tinubu
Abba Atiku Abubakar, dan tsohon mataimakin Shugan kasa Hoto: Barau I Jibrin
Source: Twitter

A kalamansa:

“Ina so in bayyana cewa babu wani mutum ko wata jam’iyyar siyasa da za ta hana Shugaba Bola Tinubu dawowa Aso Rock a 2027. ‘Yan Najeriya sun ga ayyukansa masu kyau; ba mai nuna wariya ba ne, kuma ba ya yin naɗe-naɗe bisa addini ko yanki, sai dai bisa cancanta."

Kara karanta wannan

Akwai kura: Hannatu Musawa ta yi gargadi kan ajiye Kashim Shettima a 2027

Ya ƙara da cewa irin wannan tsari na shugabanci ne ya sa jama’a da dama ke ƙara nuna amincewa da shugabancin Tinubu, tare da ganin cewa ci gaba mai ɗorewa na buƙatar ci gaba da irin waɗannan manufofi masu ma’ana.

Abba Atiku na son a zabi Tinubu a 2027

Abba Atiku ya ce ci gaban ababen more rayuwa da bunƙasa ɗan Adam da ake gani a sassa daban-daban na ƙasar nan sun ƙarfafa masa guiwa wajen mara wa Shugaba Tinubu baya.

A ganinsa, waɗannan nasarori ba za su dore ba sai an samu cikakken goyon bayan ‘yan ƙasa. Saboda haka, ya yi kira ga magoya baya da ‘yan Najeriya gaba ɗaya da su haɗa kai wajen tallafa wa shugaban ƙasa.

Ya ce:

“Shugaban ƙasa na buƙatar goyon bayanku domin ci gaba da kyawawan ayyuka. Ya dace mu tattara mutane da yawa, mu kuma mara masa baya ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba."

'Dan Atiku Abubakar ya koma APC

A baya, mun wallafa cewa Abubakar Atiku Abubakar, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

An sanar da sauya shekar ne a hukumance ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026, a zauren majalisar tarayya, inda ya bayyana manufofin Tinubu a matsayin dalilansa na sauya sheka.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da shugabannin jam’iyyar APC daga shiyyar Arewa maso Gabas ne suka tarbi Abubakar Atiku Abubakar, wanda aka fi sani da Abba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng